Sashe 48
Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
     Dan renin hankali, kawai shige min yayi tun ina ture shi da jin haushin abin da yake min har dai na zuba mishi ido, dan ban san lokacin da nabi jirgin shi ba, sai da aka bankad'e kofar da mugun karfi, tare da wani irin iska, muka mike daga ni har shi, gyara zaman rigana nayi cik'e da kunya, zan bar falon.
  Shi kuma ya zubawa kofar ido babu kowa daga ni sai shi, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juyo gare ni har na shige d'akina.
    Bai shigo ba, kawai ya fice daga gidan.
    Â
       ....
Kwatarkwashi.
  A kauyen garin, kwance Jakadiya Sahurah take, idan ka ganta tsufa ya cimma ta, amma har yanzu tana nan a tsayen ta.
     Abu daya take fama dashi shine makanta, wanda tayi rashin lafiya ta sanadin haka idanunta suke daina gani.
     Mik'ewa tayi tare da kallon kofar d'akin ta kamar tana gani, kafin ta lallubi sandarta, tace.
"Har ila yau, bai zo ba. Koda ba a haife shi bane? Ina tsohon shekaru ashirin da takwas, sai dai ko mace. Ina indai ita ce, tsuguno bata kare ba.
       Idan kuma na miji ne! Karshen zamanin yazo, waye zai isa Daura."
  Gyada kai tayi tare da mik'ewa ta fito bakin kofar ta, tana surutunta, mutanen gidan da take kallon hauka suke mata, yayinda ita take ganin kamar basu san meke damunta ba shi yasa suke kiranta da Mahaukaciya.
   ---
"Saurin me kike? Bayan shi zai zo! Karki damu kanki tabbas zai zo nimanki, kuma har ya saka a tafi mishi dake, da dai kinyi hakuri ne dole zaki fuskanci kalubale daga gare shi." Inji wani algungunmin tsohon wanda yake sanye da fatar ɓauna.
      "Hmm! Kawai ka kife shi! Yadda ba zai iya zama a karagar mulkin, ka haukata mishi Ƙwaƙwalwar shi, yadda." Ta faɗa.
"Dakata!" Ya d'aga mata hannu..
"Ba Jaamal bane! Jalaludeen ne, karfin tsarin da yake nima zai iya kashe min aljanuna da suke min aiki. Daf yake da zama me cikakken iko da nasara, karki yarda ya kasa wannan damar zuwa gida biyu.
      A sannan ne babu wanda zai dakatar dashi ko ya hana shi, sai dai har yanzun muna da damar niman Sahurah, domin itace take da masaniyar akan yadda zai dakatar da kome, kuma naga baku son dakatar da abin da yake faruwa a masarautan.
   Dan haka dukkan ku, ku bazama niman Sahurah yadda zaku iya dakatar da ita, idan shi ya same ta. Tabbas zai nimo ki, nake ba hatta sauran wanda yake boye a bayan idanun jama'a. Amma kafin nan ku fara mishi bayani Yaren da zai fahimta haka zai sanya a fara wani tunani na daban."
   Ajiye mishi jakar hannunta tayi tare da barin d'akin. Da sauri.
 Tana isa gurin motar ta shiga, tare da zama ta dauki alkalami ta fara rubutu, da ajami.
  اسلام الاكة
بي غيثو إرت الدنم مسلث، Ø¯ÙØªÙ† سشقن ييث غزك. كمر يدد كدقك عن كو ÙÙŠ ابين د يدث. كغرغطس يدد ءٱخ سير تاكررم غب. كركگشيس كبر شي يري ثكد شيرم، دغن دمطر دغ إدمكثي
دغ
Ùلن طثي....
Daga haka ta nade takardan sannan, mikawa driven tace mishi.
"Idan mun isa ka kai daura."
Amsa yayi sannan yajata suka nufi cikin garin kwantagora.
***
Kwana biyu da rikicin Jay tare da Munih ya sauka a d'akinta, Allah sarki, yau munga feleke. Shiga da ficce, shan kamshi habaici da rawan kai.
Dake ina sama, ina jinta ban ma leko ba balle tace an zo saka mata ido..
     Har dare, ana girki can da ta gama zagayenta ta gama ihu da zage zage, babu wanda ya kulata.
          Har ya shigo, ina zaune akan kafet, hankali na yayi kan na'ura me ƙwaƙwalwa, ji nayi an tab'a ni, na d'ago kaina daga shi sai yar gajeren wando tare da farar riga, ya gyara fuskar shi da kasumbar shi, mika mishi hannu nayi.
Ina murmushi, buge hannuna yayi da sauri na mai da hankali na kan shi, tare da zuba mishi ido.
"Zo d'an kanina!" Kamar na zage shi, ya buge hannuna.
"Toh meye nayi kuma?"Â A sannu ya mike zai bar d'akin nace mishi.
"Don Allah, kayi hakuri ba san laifina ba."
    Mik'ewa nayi na isa gare shi, ya riko hannuna, cikin na shi, yana me kaiwa fuskar shi. Kashe mishi ido nayi sannan nace mishi.
"Au! Yallabai aski kasha haka, shi yasa naga kana kyalkyale amarci."
   Saka hannun shi dukka biyu yayi ya rungume ni, yana murmushi sannan yace min.
"Yau wuni guda, ina kallon wayana ko dan sakon nan babu, sam baki damu dani ba."
     Hada goshina yayi da nayi, ina yar karamar dariya nace.
"Ina zan iya da shariyar ka, idan miskilancin ka ya motsa baka ji baka gani, shi yasa naki kula wayar ma, ai fita kayi kana fushi dan nace zan shiga cikin gidan gaida su Mamah."
   Daura bakin shi yayi saman nawa, a lokaci guda muka kalli cikin idanun juna. Nice na fara kasa da kaina, kafin na janye bakina baya nace.
"Jay! Kana sha'awan jikina ne fa! Sam baka tunani na, jikina shine muradinka, tunda da bakin ka kace baka sona."
"Eh shi yasa lokacin da kika turo min Hanisah ta gaya min kina son kayan fitar liyafa, baki yi tunanin bana sonki ba!"
Da sauri na kalle shi, murmushi yayi sannan ya d'aga min gira daya.
"Ni ban tura ta ba! Taji dai muna magana da Saif.."
Cizon bakina yayi, tare da b'ata fuska.
"Karki kuma kira min sunan wani kato a cikin gidan nan!"
"Toh Naji, amma."
"Baki tambayi taya aka yi na kasa wancan tuzurin saurayin baki ba?" Ya faÉ—a min.
"Toh ni nuna ruwa na"
"Zaki ga baki da ruwa."
    Ƙoƙarin kwace kaina nake yi, yaki sake ni, "tun daga ranar da kika shiga rayuwata nake jin duk yadda aka yi, ina da nasaba dake.
      Na rasa fahimtar haka, sai ma rigimar da kika ta takalowa, haka bai ishe ki ba, sai da kika kwafta min mari, sannan kika yi sanadin haɗuwa na da iyayena.
         Ana saura sati daya bikinki, Baba Sarki yake gaya min shekaru Ashirin da daya, da suka wuce, sun daura mana aure. Bayan b'atar da nayi da shekara daya aka raba auren, iyayen mu basu sani ba, daga kakanin mu, babu wanda ya sani.
      Sai gashi kin nimo mijinki, ko kunya baki ji, Baba Sarki da yake gaya min, nayi mamaki dan haka nazo har sokoto, na sami Dattijo, muka yi magana. Na kuma ce ko bana sonki a bani matana ko kuma a tashi Sokoto a tsaye da kafarta.
  Ranar da na sauke ki, ai sabida kar wancan banzan ya kare miki kallo ne, dan haka ki ji a ranki ni har yau ina kan bakana, bazan tab'a sonki ba. Dan bana jin kome akan ki, sai yan uwanta ka."
Wani irin abu naji a raina, ban san lokacin da na ture shi ba, nayi juyawa na kwashi kayana, yana min magana tuni na isa d'akina na rufe kofar, na zauna a jikin kofar, tare da cusa kaina cikin cinyoyina. Wani irin abu nake ji a raina, me mugun ciwo, tare da jin tsanar Jay a zuciyata.
 Bai bi takaina ba yayi ficcewar shi, kasa. Haka na kwana da b'acin rai da asuba nayi mafarkin wai an kawo min shi cikin jini baya numfashi. A firgice na farka na shiga nayi alola nazo na gabatar da sallar nafilla, da sauri na shafa addu'o'in na fito kasa, na tsaya a bakin matakalar benen, ina jin ya fito daga dakin Munih na sauke ajiyar zuciya. Sannan na juya abuna, ya hango Ni, amma ya share ni kamar bai ganin ba.
       Bai dawo gidan ba sai da gari yayi haske, ina kwance a saman...
07035133148/ +22784506476 Zahrah ko Nana Aicha....
10/23/20, 9:59 AM - Ummi Tandama: *Zuma, ga zaƙi ga harbi*
Ina kwance ya shigo, dake Allah ya daura mishi niman rigima, idanuna na lumshe ya shiga ja min babban yatsar kafana, bude ido nayi tare da lumshe su, dan bana son damuwa. Da sauri na kuma buÉ—ewa tare da b'ata fuska kamar zan yi kuka.
     "Dan nace bana sonki shine kike fushi?" Ya faɗa min,
"Toh ina ruwana da kai, karka so ni mana, idan baka soni ba, dubunka sun so ni, dan haka ka kyale ni naji da abinda yake damuna." Fadar haka da nayi ya bashi haushi amma jin na fadi ya barni naji da damuwa ta, ya sashi zama kusada dani. Yana kallon fuskana.
  "Batul!" Tsigar jikina ne suka mike sosai, a hankali na tashi zaune.
" Matso kusa dani naji meke damunki!" Ya fada min tare da mika min hannu, kamar zan yi kuka nace mishi.
"Babu kawai bana son magana ne!"
"Zo ki gaya min meke damunki!"
Ya mika min hannun, babu yadda zan yi haka na isa jikin shi. Kawai naji zuciya ta tayi mugun rauni, kuka ne ya kwace min.
"Ya ilahi! Dan nace bana sonki?"
"A'ah, ba haka bane kawai ina jin wani irin yanayi ne, da ban saba jin shi ba, sai da rasa wani abu daga jikina nake ji shi."
.zuba min ido yayi sannan yace min.
"Kamar Ya? Kawai naji kamar zan rasa wani na jikina ne"
   Murmushi yayi sannan yace.
"Har yanzun akwai masu yarda da canfe kenan? Toh babu abin da zai faru sai Ikon Allah, dan haka karki kuma zubda wannan hawayen masu mugun tsada, kin san nawa darajar su take, da kike zubda min su?"