← Book details Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 72

Sashe 39

Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Jay bana son damuwa! Daga abun arziki sai ya koma na tsiya, Insha Allah zan yi aurena lafiya,, kai kuma ka cigaba da tsiyar halinka wawan Yaro kawai, baka da hankali gata tayi maka illa."

  "Khatoon!!! Ni kike kira da wawan Yaron?!"
"An gaya maka ban kaddarar so me zanyi da Kanin bayana, kana dan mitsitsi da kai, me zaka iya yi da mace irina, kaje kayi da kananun kwalayen matanka da aka dankara maka su. Sha-sha-sha kawai."

    Huci yake kamar zuciyarshi zata diro, mafi girman cin fuska da aka mishi a duniya, shine nayi mishi. Dama kuma na saba, dan haka Ni ban wani damu can ba.

      ***
Wani irin haushi yake ji, kamar ya rufe mutane da duka, shafa ciwon shi yayi. Tare da kallon kan shi a madubin dakin shi, yana son hango ta ina Yaron yake.
             Karewa kan shi kallo yayi yaga babu ta inda yayi alaka da yaro Aanih ta kira shi da yaron da rashin sanin hakkokin dan adam, shine Yaro.

        Marin kan shi yayi, tare da kwafa.
        ***
Bikin Jay  ya zama bikin da ake mishi wani irin tanadi na musamman, kasancewa Jikar Tsohon sarki kuma mahaifin shi yake rikon kwarya, uwa uba. Kakan shi na gurin Uwa sarki ne dangin Mahaifiyar shi kusan manyan attajirai ne a garin Borno.

    Haka yayi mugun tasiri a kan bikin, domin kuwa kowa murna yake da bikin kafaffen sadarwa ake shelar auren, ta ko ina na'am ake da al'amarin.
...
An kai kayan auren Munih Damagaram, sannan aka kai Na Husnah, kuma dukkan su biyun babu wacce ya tab'a kira da sunan soyayya, haka ya kuma sanya kowacce tana zargin ko yafi son yar uwanta da ita.

      Abinda ya shiga kawo musu kishin juna da kuma tsana na musamman. Kowacce tana jin itace.

.......
Saura kwana biyu bikin muka tawo daga Sokoto tare da Ummi, da yamma likis muka shiga gidan, a gajiye nake d'aga kafana sabida tafiyar motar da muka yi.

             Ummi ce a gaba, sai Hanisah da kuma Janny a kusa dani. D'aga kaina nayi muka yi ido biyu da shi.

      Ya kara wata irin girma, a raina nace.
"Jibgege!"

    Kallon banza yayi min, sannan ya kauda kan shi, a ran shi yana aiyana yadda zai samu damar mun rashin mutunci. Ko sau daya ne.

            Zama muka yi aka shiga gaisawa, tunda muka gaisa da Mama ban kuma bin takan shi ba, sako ya turo min.

*Gayyar soÉ—i! Kin zo cin shinfaka da miya ne?!*

_Haba Yaro kaine baƙon aure,.Ni wani irin aure ne ban gani ba, wani irin abu ne ban gani ba_

      D'agowa yayi muna kalli juna, cizon bakin shi yayi tare da mik'ewa zai bar falon.
      *Hmm!*
     _Inji me Ciwon hakori_

     Fuuu ya bar falon, kamar wanda na mishi zagin ƙare dangin.

Kara wayata tayi na dauka.
"Fito ki same ni"
"Bazan fito ba"

Kafin ya kuma magana na kashe wayar, haushi ne ya kuma kama shi.

        Tunda aka fara shagalin bikin ban kuma ganin shi ba, amma kullum muna nan muna fada a waya, har ranar daurin auren.

         Bayan an daura auren shi a Nijar aka kuma daura anan naji ba dad'i, amma na share batun shi, na shiga mutane akayi  hidima dani.

             ---
Da dare bayan kawo amare aka tafi liyyafa, dama munyi da Saif zai zo. Dan haka na ci uban kwalliya muka fito gurin, tunda na shigo gurin na hango shi dunkule yana hura hanci, Ni kuma na zauna kusa da Saif..muka shiga hiran kamar ba gobe wallahi na manta da batun Jay.

             Dan na fahimci nice nake haukata, kawai mun yi nisa a hira sai ganin shi nayi akan mu.
"Malam bata gaya maka cewa tana da aure ba?"

Da sauri na d'ago kai ina kallon shi, murmushi yayi sannan ya zaro takardu daga aljuhun wandon shi ya direwa Sa'id duba ka gani.
"Har da shaidar cikina a jikinta, kai duba."

     Kallona Saif yayi sannan ya sake murmushi, yace.
"Toh Naji amma ban ji daga bakin mahaifinta ba!"

Ƙatuwar ajiyar zuciya na sauke tare da murmushi nace.
"Kasan lissafin yaro ba daya yake da na manyan ba! Shi yasa ya kwaso jiki ya kula min makirci. Yaro man kaza. Da an saka a rana ka narke. Tashi muje."

Muka mike tare da barin shi kamar ya fasa ihu, sabida bakin ciki.
Har muka bar gurin, a fusace  Saif ya juya kamar zai buge ni.
"Meye alaƙar ki da shi?! Ba na rabaki da shi ba, ko bance bana son alaƙar ku da shi ba? Fatimah ina zuba miki ido ne bawai dan bana son damuwa bane kawai ina kallon ki ne na kuma ganin ki da yaron can zan baki mamaki. Na rabaki da yaron nan."

    "Idan kuma baki rabuwa da ita ga?"
     Inji Jay,
" Tsoro ne ya kamani! Don Allah Saif muje ka rabu da shi yarinta ke dawainiyya da shi bazan kuma kula shi ba.".
    
" Ni kike kira da yaro? Ni kike cewa fuska? Lallai kin tsokanowa kanki abin da yafi karfin ki."

    Kai hannu shi yayi zai riko ni,Saif ya janye ni da sauri, ai kuwa Jay ya kai mishi duka. Shima ya rama, kai naga tashin hankali. Domin dambe ne ya sarke a tsakanin su. Na rasa yadda zan raba su,suka ture ni.

        Ana cikin haka sai ga Baba Aswad yazo wucewa yaga suna dambe tsawa ya buga musu, suka rabu.  Jay na faɗin.
"Wallahi na rantse maka baka da rabo a jikinta idan kuma kana ganin  karya ne, nan da sati biyu zamu tabbatar da waye d'an halak."
"Yaushe d'an kwarkwarah yasan hallaci?
#Mai_Dambu...
10/23/20, 9:57 AM - Ummi Tandama: *Wawa ana sonka, amma ba a son haihuwar ka.*

Ban san wani irin yanayi muka shiga daga ni har Jay da Baba Aswad ba, sai dai lokaci guda kome ya tsayawa Jay cak.

Kurawa Saif ido yayi, cikin kaduwa da tashin hankali, ya taka har gaban Saif.
"Kace me? Maimaita min naji?"

"An gaya maka d'an."
Toshe mishi bakin shi nayi, cikin tashin hankali, sannan na koma bayan Jay na tsaya.
"Jay ina tare da kai. Ka rabu dashi kawai."

Janyo ni yayi tare da ture ni, gaban Saif.
"Gata nan amma baka da rabo a jikinta kai. Na yarda ni jinin Kwarkwarah ce! Amma sai na nuna maka Ni ban tab'a niman abu a gurin Ubangiji ya ki bani ba! Dan na yarda da shi.

.....zan nuna maka yadda ake Kwarkwarah yake amsar abu a hannun d'an halak."

Daga haka ya juya abin shi bai kuma magana ba. Bayan shi zan bi Baba Aswad ya yace min.
"Dawo!" Kallon shi nayi zan sake kuka.
"Saifullah! Kayi Kuskuren, ba Jalal kad'an bane Kwarkwarah daga mahaifiyar shi har mahaifin shi, nasarar su daya ne. Tun da ya dawo muke niman hanyar da zamu gaya mishi maganar amma yau kad'ai ka ruguzama mana, tanadin mu akan shi.

Ka fita a masarautar nan kafin Mahaifin shi ya hukuntaka,"

Yana gama fadar haka ya sani a gaba muka bar Saif ya tsaye, cike da Mamaki.

Muna shiga falon Abban Jay muka same kowa a tsaye sunyi jim, suna kallon Jay da ya sunkuyar da kan shi kasa.

Jikina ne yayi wani irin mutuwa, a sannu na taka har gaban shi, na dauki ruwan da aka zuba mishi yasa yaki na mika mishi. D'ago fuskar shi yayi ya zuba min ido.
"Tashi ki bar nan!"

Muryana yana rawa, nace mishi.
"Jay ban san kome ba."

"Ki fita yace! Mayya mata zuciya, an ce ba a sonki dole ke sai ya soki ko kunya baki ji ba, kanin bayanki, kike likewa mara zuciya kawai ki tashi min a gaban mijina kafin na nuna miki abinda zai baki tsoro." Inji Munih.

"Ke dalla kiwa mutane shiru, banza matar cushe, Hamma Jay baya son wata mace Sama da Addah Aanih, idan kuma kina musu na gaya, Ka bar boyewa duniya SOYAYYAR da kake mata.

Sau nawa kana gayawa mutane matar kace ita! Kana yaudaran kanka baka sonta. Wata biyu da suka wuce sabida ceton rayuwarta kai ma aka yanka ka a ciki duk wannan kiyayya ce?

A yayinda Allah baya bamu dama a rayuwar kama ta yayi mu gode mishi ba butulce mishi ba.

Kowa ya kalli Addah Aanih yasan tana haukar sonka bata da zab'i ne tsayar da wani dan ta nisance ka.

Har yau Abba yakan saka hoton Umma Jannart a gaba yana kallonta ba dan kome ba, sai dan abinda kake aikatawa shi ya aikata.

Idan ka gadama ka fadawa kowa kana son Aanih Fatimah, idan kaso kayi shiru. Wanda haka shi zai sanya ka zubda kwalla na tsawon karshen rayuwarka. Amma tabbas Zuciyarka nata ce." Inji Jannart karama.

Har zata fita yace mata.
"Noorie! Dama Ni din Mahaifiyata Kwarkwarah ce?"

Juyawa tayi sannan ta sake mishi murmushi wanda ya sanya ta zubda kwalla, ta tako a hankali gaban shi.
Ta durkusa, a gaban shi. Tana kallon shi sannan tace mishi.
"Mamah Raihanah da Abba dukkan su y'ay'an Kwarkwarah ce, Ummin sokoto da Umma Jannart duk Y'ay'an Kwarkwarah ne.

Su wad'ancan matan sabida masalaha aka samar dasu, ita kuma ta samar da daidaiton zaman lafiya ne da fahimtar juna, ta kuma warware matsalolin rayuwar wasu!"

"Indai haka ne, toh ki ce mata ta je bana sonta."

Mik'ewa tayi sannan tace.
"Hamma yayi maka haƙan."
. Kauda kan shi yayi, dan baya son ma ya kalle ni.
Chapter 39 · 0% Book details