Sashe 68
Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
...... Kwana uku da suka biyo baya na sauko na fara gaishe shi, wai nan na kuma ganin rashin mutunci sosai. Domin kuwa tsakanin shi da Allah ya dauki fushi.
    Dakyar da sudin goshi na samu kan shi ya sauko, tare da gaya min maganar da yafi na da muni, ba dan yace baya sona bane yaki tab'a ni sai na k'iyayye kome nashi, a cikin kwanaki da muka yi a Amurka nayi kokarin koyawa kaina hakuri dashi, domin na kasance ina gani naki gani, ina ji naki ji. Haka yayi mugun sanya samun nutsuwa. Satin mu biyu aka sallame shi muka koma hotel din da yake kusada asibitin, anan muka cigaba da kulawa da lafiyar shi, kullum zamu shirya mu fita, tare da shi, muyi ta daukar hoto. Mutum kamar me aljanun. Yana ganin wasu mazan suna bina da ido zai rufe ni da fada, sai fushi yau ma haka ce ya faru. Tunda wani baƙin fata ya kafe ni da ido, mutumin nan ya shiga masifa karshe dai, muka dawo gida sai ya fara fushi, da dare na matsa kusa da shi, na kwanta.
... .... Tare da rungume shi, ta baya, amma ya cire hannuna, a hankali nake wasa da gashin kanshi. Ya juya a fusace, kawai na tura mishi, bakina dole yayi shiru. Daga nan kuma ya shiga shagalin shi.
 Kome ya tuna sai gashi nan ya ture ni, tare da juya min baya, dariya ya bani sabida ya iya bori, a cikin Jay babu iya ka, kai jama'a.
     A cikin kwana biyu muka shiga tattarowa zuwa gida, dan dukkan mu, mun yi kewar gida, a hankali yake gaya min yadda yayi kewar Najim da Fahad, kuma Nima na fahimci haka daga yadda yake jidar musu tsaraba, nima ya sani dole na kwashi kaya da kudin da yake hannun mu, turarruka da kayan kwalliya kawai na diba.
   Sai kaya masu kyau na zamani wasu Rumah da Hanisah da Jannart da Raihah. Na sayawa Iyayen mu maza suma turarruka tare da matan.
Sai Husnah da Munin suma na diba musu, har muka bar kasuwar zamanin.
    .... Washi gari muka bar garin, kaina na kafad'ar shi, muna hira har muka gama kome, sannan muka shiga jirgin mu.
       ---
Ranar juma'a muka iso garin Abuja, da karfe tara na dare, a gajiye muka fito, daga gidan Minista Dr Bulama, aka zo daukar mu. Tare da wasu yan mata fannah da Ammah, Sun hadu ba laifi tun da muka shiga gidan.
  Matar gidan jikinta yake rawa,tana hidima da mu, ta kawo wannan ajiye min wannan.
  Sabida ganin Jay a cikin gidan kawai, Yaran matasa da yan mata na gidan sun saka shi a tsakiyar su ana hira dashi. Ni kuwa matar nan bani kulawa tayi ta hanyar sani nayi wanka ta bani wannan naci na shafa wannan sannan take ce min.
"Zahrah! Duk cikar mace matukar ta gaza daukar nauyin cikin mijinta sunanta sakarya!
  Kiji a ranki ki macece, kiji a ranki ke zaki iya sarrafa abinda mijinki zai iya ci, bawai wanda ba zai iya ci ba.
Karki yarda wata mace ta hango kasawar ki, ki nuna mata ko a gidan giya akwai babba, bana son naji ace akwai wacce zata iya karban matsayin ki, Mu Ahalin Jannart, Uwar mijinki muna matukar kaunarki da kuma girmama duk wani abinda ya shafe ki, karki ji kome duk abinda kike bukata ki gaya min, za mu miki."
Kwalla ne ya cika min ido, zuciyata ta kuma cika da kaunar Jay, Kaf dangin Mahaifiyar shi suka matukar kaunata. Na rasa wani irin so suke min, suna matukar girmama alamarina, kamar su goye ni suke ji, bani da Uwa amma Allah ya bani su ta sanadin Jay.
   Daga nan ta bani wata lafayya, na saka bayan na shirya cikin riga da skirt, na atamfa sannan na nad'e kaina da laffayar ta ja hannuna zuwa. Babban Falon Dr Bulama..da sallama muka shiga cikin.
"Ango ba cefene, yau kaine a garin mu, na zata ba zaka tsaya anan bane!"
Shafa kan shi yayi sannan ya sake wata lallausar murmushi, sannan yace.
"Uwargidan Amaryan, duk ke daya. Babu me kwace miki fadar ki."
"Aikuwa na iya kishi Dan wannan jaja amaren ka, waka zan mata da ruwan sanyi."
Murmushi nayi tare da sunkuyar da kaina, sannan muka gaisa da baba Dr, muna cikin gaisawa yace min.
"Maamah! Baki ba shi labarin yadda yayi jinyar shi bane!"
Kallon juna muka yi da Jay ya sake min murmushi, nima na maida mishi, tare da gyad'awa Baba Dr kai nace mishi.
"Idan na fada ba yarda zai yi ba, shi yasa na bar maganar, dan zai ce ba gaskiya bane"
 Gyada kai yayi sannan ya shiga bamu labarin, rikicin da muka yi ta yi, akan ya kirani Maamah, murmushi kawai yake, yana kallona, ganin har lokacin yana me kafe ni da ido, kawai naji a raina da zan iya jin abinda yake ran shi nasan yabo ne da jinjina...
07035133148/ +22784506476 Zahrah ko Nana Aicha....
10/23/20, 10:21 AM - Ummi Tandama: *Allah, ya maida ƙoƙo masaki.*
_Ke Alkhairi ce duk namijin da ya same ki a rayuwar shi, yayi sa'a_ yace a ranshi, yana murmushi.
  *Akwai sa'ar da mutum zai yi bayan ya sami nagartaccen mutum irinka? Ai kai ne sa'ata baki daya* na fadi haka a raina, ina me sunkuyar da kaina, hira sosai aka bude tare da tattaunawa akan asibitin shi da za a bude mishi, amma kuma naji Baba Dr yana cewa.
" Bai zama dole a bude maka ba, dan naji suna wani batu akan ka Allah ya tabbatar da Alkhairi."
"Amin Ya Allah,"
Muka amsa baki dayan mu,
 Dakin abinci muka nufa, anan muka ci kad'an sannan muka fito, ina kallon yadda yake bina da ido, kin kula shi nayi. Har muka nemi kwancin mu, daki daya aka bamu, dan haka muna shiga.
  ..Na shige ban daki, na watsa ruwa, ina fitowa na same shi, ya rage kayan shi zai shiga wanka, janyo ni yayi tare da kallon fuskana.
"Ki shiryarwa daren yau! Dan ina ganin zan rage za...."
"Yallabai! Kwantar da hankalinka, Ni hutun sallah ma nake, yanzun na gani." B'ata rai yayi wucewar shi abin shi. Bai kuma kulani ba.
  Har ya fito ya samu na fara barci, shiryawa yayi sannan yazo ya kwanta a bayana, tare da janyo ni jikin shi, a hankali barci yayi gaba dashi, sabida mun rigada mun gama gajiya, shi yasa bai dame ni ba.
     ---
A can daura kuwa, sun san mun sauka a Abuja, dan haka Abba da kan shi, ya saka aka kira su Husnah. Bayan sun shigo suka gaishe shi, kallon su yayi sannan yace musu.
"Allah yayi muku albarka." Ya fada a sanyayye, sannan ya kuma cigaba da cewa.
"Gobe Insha Allah, Mijinku zai dawo suna Abuja ne, da yayarku!"
   "Allah ya dawo dasu lafiya, muna jiran su." Inji Husnah,
Kallon su yayi sannan yace musu.
"Ko kuna da bukatar wani abu ne?"
"A'.."
"Eh! Muna da bukatar kudi." Inji Munih, bayan Husnah tana son cewa a'a, murmushi yayi tare da dauko wata takarda me kunshe da kudi ya mika musu.
Suka amsa suna godiya, sannan suka mishi sallama, tare da barin falon, murmushi yayi yana jinjina qarfin halin Munih, yana kuma girmama hakurin Husnah.
 ... .. Yadda take murmushin mugunta bayan sun fito.
"Insha Allah saura kiris naci qaniyar wata, idan na gama da ita na dawo kan farar angulu." Daga haka tayi wucewarta, Husnah bata kulata ba, dan tasan da ita take.
......
    Washi gari
Farkawa yayi ya kalli yadda gashina ya rufe mishi fuska, yana fitar da wani daddar kamshi, shafa kaina yayi sannan yace min.
"Nanah Fatimah!" Tura mishi baki nayi tare da gyara kwanciya ta a jikin shi, sake shafa fuskana yayi zuwa wuya na yace.
"Zuhruyyah! Tashi zan tafi sallah ne!"
A hankali na d'ago kaina sannan na janye daga jikin shi, cire matashin kan shi yayi ya cusa min a jikina, sannan ya daga gadon, kallon yadda na k'amk'ame matashin yayi.
  Murmushi yayi sannan yazo ya sumbaci bakina, zuwa goshina, kafin ya shiga ban daki. Sai da ya watsa ruwa, sannan ya dauro alola tare da saka jallabiya ya nufi masallacin da yake cikin gidan.
          --- Kafin ya dawo nayi wanka, ina fitowa yana shigo min d'aki, zama nayi a gaban mudubi na shiga gyara jikina, ina gamawa na dauki kayana, ina sakawa ya matso kusa dani. Rungume ni yayi tare da cewa.
"Kina da jiki me kyau! Shi yasa baya nuna tsufarki"
  ..... Gyada mishi, kai domin Jay bai iya magana ba, kuma duk abin da zai fito bakin shi, Alhamdulillah Nagodewa Allah, kawai yankota yake.
   Ina gamawa na shirya cikin doguwar rigar yadi me tsantsi, duk da na saka wando da rigar mama, amma haka Jay ya hanani sukuni da surutu.
"Wallahi baki isa ki fita gidan nan da dan jinjirin mayafin nan ba, sabida rashin sanin ciwon kai, toh wallahi naga kafarki a waje zan zane ki kinji na rantse da Allah."
 Zuba mishi ido nayi, gaban madubi na duba kaina naga dole yaji Babu dad'i, domin kuwa duk inda na juya jikina sai ya girgiza, dake ina da ƙaruwar jiki ne, cire kayan nayi sannan na nimo wata atamfar riga da zani, na saka amma dake yau yana jin rikici ne, nan yace bai iya ji ba.
  Na nimo doguwar rigar na saka, na atamfa, na saka ina sakawa ya kare min kallo, kauda kai yayi sannan yace min.