← Book details Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 72

Sashe 35

Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

             Dan danne danne yayi sannan ya kira. Sai da yayi shiru na wasu lokuta kafin ya iya buɗe bakin shi yace.
"Ke wacce irin mutum ce da bata da cikakken hankali, aure zaki yi? Ko sanin ya kamata baki yi ba, yaushe kika tsarewa aurenki da har zaki so wani auren?"

       Kashe wayar aka yi, ya kuma kira yaji taki shiga nan haushi ya kama shi, ba tare da ya kuma wani abu ba, ya rufe wayar.

......
Abuja.
Ina aiki a kicin kawai naji kiran waya ina dauka, ya fara gaya min magana. Da na fahimci cewa zai b'ata min rai shine na kashe wayar baki daya, na cigaba da aikina.

Indai halin jay ne babu bukatar na damu kaina, ba yau muka saba ba. Kuna wayar na kuma yi dan nasan ya hakura ba zai kira ba.
Dan haka na ajiye na cigaba da aikina.

Sake kira aka yi na share, karshe ina na kuma dauka, ina sakawa a kunne na, ya shiga masifa.

"Kaga Ni bana son shirme da yaranta, dan na fahimci baka san ciwon kan ka ba, don Allah karka kuma kira na, mayye mara zuciya, kaje kayi rayuwar ka mana, Asood kafita harkokina."

Daga haka na katse kiran Asood, na cigaba da abinda nake. Dan da farko na zata Jay ne ashe ba shi bane. Asood ne.

----
Wasa wasa, aka saka bikin Jay, yana cika yana batsewa aka fara kai kayayyakin auren daya gidan Galadima, daya kuma aka wuce dashi Damagaram, cikin wata uku da aka saka bikin anata hidimar gidana sabon Asibiti dan baban shi na Canada ya kawo mishi takardun shaida karatun shi.

Dan haka aka shirya mishi tafiya Maiduguri, sun zo su amma shi bai samu damar zuwa ba, sabida ana tunanin kar a kuma dauke shi.

... Tunda ya shigo garin, aka karb'e shi cikin gata da farin ciki, ga uban dangin Maman shi da kuma gidan sarautan da aka shiga mishi hidima da biki.

Anan Ministan harkokin lafiya Dr Bulama yake tambayar shi matsayin Karatun shi.

"Yallabai! Na karanci ɓangaren mata da yara ne," gyada kai yayi sannan yace.
"Zaka yi aiki da mune ko zaka gina naka na kanka?"

Gyara zama yayi sannan ya sunkuyar da kanshi..
Yana faÉ—in.
"Nafi son nayi aikina da kaina, amma naji ance sai naje Nsukka nayi jarabawar gwaji."

"A'a mun dawo da ita gwagwalada, zaka iya zama a cikin gidana na can kayi jarabawar a can, idan ka gama sai ka dawo gida. Sannan kuma asibitin zan so kayi mana anan, amma nasan mahaifinka yana kewarka kuma zai bukaci kayi a daura, dan haka ga zamu bada gudummawar mu."

Nan ya dauko takardan cheq ya rubuta mishi kudi masu yawa, yayi godiya sosai.. lokacin da ya shiga sauran gidajen, dangin Maman shi haka suka yita bashi gudunmawar su na Asibitin da za a gina mishi karshe ya nuna musu kudin yayi mishi yawa.

Nan suka shiga ba shi labarin, rayuwar Mahaifiyarshi, tun daga kakar shi da tafita da Jannart, har zuwa irin sadaukarwa da mahaifiyar shi tayi, sannan suka zuba mishi ido.

Yana kallon su bai ce kome ba, a hankali ya sunkuyar da kan shi, kasa, sannan yace.
"Kenan masarautan zagaye take da ruffenfen sirrin da suka kasa cimma matsaya akan shi?"

"Masarautan cike take da tsinuwar mutane da aljanun." Inji Umma Kaltum, kanwar Mahaifiyar Jannart,

Sun jima suna tattaunawa kafin yayi mata sallama, ya nufi gidan kakan shi, ya same shi. Shida wasu malamai, juyawa yayi zai fita wani Dattijon a cikin malaman, ya kira shi.

Shiga yayi ya zauna tare da sunkuyar da kan shi Sarki Kazeem yace musu.
"Shine Jikana na fari, dan gurin Jannart Hassanah, bai jima da dawowa kasar ba."

Gyada kai malaman suka yi sannan suka zuba mishi ido kafin suka ce ya tafi, yana fita babban cikin malaman yace musu.
"Wannan yaron yazo rusa tarihi ne! Bayan shi kan shi tarihin ne, karfin hali da juriya duk yana da ita, kafiya da naci ya dauke kome. Sai dai kuma ban san wani irin yanayi zai kasance ba, daga ranar da taurarin su ya hadu guri guda.

Domin duk matan shi babu wacce zata iya daukar nauyin kasadar da take cikin rayuwar shi. Idan kuma aka samu toh tabbas tarihi zai iya mai maita kan shi, domin masu fushi da fushin wani suna fusace akan shi, sannan wata duniyar tana niman shi domin dai-dai mata alkaryanta, kada ku sake yin wasa da rayuwar shi, koda kuwa yanayin tafiya ce ta kama shi, yayi ta Addu'o'i. Domin akwai matsala ba akan shi zata faru ba kan duk wacce tsautsayin...
#Mai_Dambu
10/23/20, 9:56 AM - Ummi Tandama: *Ba domin tsawo a kanga wata ba*

"Duk wacce tsautsayin ƙaddara ya shiga tsakanin su da shi, dole itace zata maye gurbin da aka rasa amma muna namu Allah yana nashi.'"

       Cikin tashin hankali, Sarki Kazeem ya zuba musu ido, had'iye yawu yayi sannan yace.
"Babu yadda za a dakatar da al'amarin?"

       Mik'ewa babban yayi cikin nutsuwa ya taka a hankali zuwa bakin kofar fita yace.
"Idan guguwa ta taso ka tab'a ganin an dakatar da ita? Idan ruwa zata yi ambaliya ka tab'a ganin an sanya mata shinge, toh kamar yadda mutuwa take zuwa babu sanarwa haka kaddarar su ta haÉ—a lokaci guda.

        Dan haka Allah shi yafi mu sanin abin da dace."

     "Sheikh Muhammad, a yanzun haka shirin auren shi ake, mun zab'a mishi mata, ya amshe su amma daya daga cikin su yaki amsar tayinta ." Inji Kazeem.

   Girgiza kai Sheikh Muhammad yayi sannan yace.
"Karku manta, tunda ya amshi tayin sauran haka yana nufin kaddarar su da ita wacce yaki amsar d'aya ce. Haka yana nufin tarihin masarautar su zata kuma mai-maita kanta kenan"

Daga haka suka ficce, daga gidan. Shigowa Jay yayi jikin shi a mace dan ya hadu da su Sheikh Muhammad suka mishi wani irin kallo. Sannan zasu wucce Sheikh Muhammad yace mishi.
            "Tauraron ka yafi nata karfi! Ka nisanceta domin kusantarta dai dai yake da tab'a karfin haskenta, daga ranar da kayi gangancin tarayya da ita. Toh daga sannan kome zai iya faruwa da ita. Ka rabu da ita tayi rayuwarta domin ta hanyar zata kuɓuta daga kaddararku"

        "Kai waye da zaka dakatar da ni abin da ban damu dashi ba? Wacece kake tunanin ta isa nayi rayuwa da ita?  Idan ina son Mata dubu zan iya mallakawa kai na, amma mace bata gabana zaka iya tafiyar ka"

          Yayi gaba yana jin babu dadi, murmushi Sheikh yayi sannan yace.
"Tabbas rayuwar wannan Yaro cike take da Izzah, shi yasa yake jin kome akan shi."

    Daga haka suka bar masarautan baki daya.

    ----
Cikin sauri na fito daga cikin gurin wanke kai, da nazo yi. Ina kallon wayar dake hannuna naga kiran Saif ne, murmushi nayi zan dauka naji an rike hannuna.

                 D'ago kaina nayi naga wata tsohuwa, tana rike da sanda. Ajiyar zuciya na sauke tare da zuba mata ido tsigar jikina yana mik'ewa.

           Murmushi nayi mata a sanyayye na zare hannuna daga nata, na bude jakata zan dauki kudi ina kawai naji wani abu zummm, naji jikina yayi min wani mugun sanyi. Kallon matar nayi kamar zanyi kuka nace mata.
"Me kike bukata?"

Dariya tayi idanuna yana fidda wani irin yanayi shi ba kore ba, shi ba shuÉ—i ba, shi ba rawaya ba. Kafin ya koma fari.

        "Lallai zaki mutu! Domin kuwa kina dab da zama fanko. Ki biyo ni domin kuwa ni ce bazan tab'a."
           "Fatimah!" Naji muryan Saif wani irin ajiyar zuciya na sauke tare da juyawa gare shi, ya ganin idanuna cike da kwalla ya kara leka inda na juya babu kowa, nima juyawa nayi babu matar babu dalilinta.

"Zo mu tafi!" Ya ce min.

     A hankali na isa gaban motar ya bude min na shiga tare da zama sannan ya rufe, ya dawo inda yake ya zauna sannan yaja mu. Kallona yayi sannan yace min.
"Ina ji a jikina kamar bazan same ki ba"

             "Hmmm!" Nace mishi,
"Zahrah!" Ya kira suna na a sanyayye.
"Ina sonki" juya kaina nayi sannan nace mishi.

" bai zama lallai na maida maka abin da ka bani. Amma ina mutunta duk wani alamarin ka."

     "Aanih ko dole nayi Miki ne?"

      Juya kaina nayi tare da kallon farce na, ina tuna lokacin da Jay ya sace ni, har ya mai dani dakin shi, na tab'a farkawa naga yana kallon zanen fulawar hannuna, tare shafawa. Koda na farka b'ata rai yayi sannan tare da barin d'akin.

    Yau ma sai da na saka aka min zanen lallen dake ja ne, kai hannun Sa'id yayi tare da shafa hannun, cikin jin haushi na harare shi. Sannan nayi fiki-fiki zan mishi masifa ya zuba min ido, karshe tamke fuska nayi cikin b'acin rai, har muka isa gida.

            Hannuna na kai domin bude kofar motar yace min.
"Ai ko babu kome zaki min sallama ko Zahrah?"

       "Sai anjima!"nace mishi a dakile, ya fahimci naji haushin abinda yayi min ne yasani jin ba dad'i.
"Toh kiyi hakuri bazan kuma." Ya faÉ—a min a sanyayye, zuba mishi ido nayi naga ya wani narke min.

   Sai ya bani tausayi, na sake murmushi nace mishi.
"Wannan satin zan shiga sokoto"
"Na sani ai shi yasa nake ta tambayarki."
         "Toh ba damuwa zan zo can."
      Daga hakan na juya cikin gida, shi kuma yayi tafiyar shi.
Chapter 35 · 0% Book details