Sashe 52
Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Inji wani d'an iskan? Bayi na ne, daga masarautan mu aka kawo min su. Ni jinin Sarauta ke bin jikina, ba daurin dausono kunun bayan ludayi ba, duk wata yar iska ina dai-dai da ita kuma kar na dawo daga rakiyar bakina ba same ku kuna aikin nan in ba haka ba zan sa akawo min Barde ya hukunta min kowacce ku."
Daga haka nayi wuccewa ta na raka su Qarama, tun da na juya da sauri suka bar aikin kowacce tabi Zabba'u zuwa Shashina. Nan suka shiga zagina wai na kwashe bayina dama basu da bayi ne, karshe dai maganar aka yi ta ririta alamarin har washi gari suna. Mamah Nanah ta shigo da safe tayi min cin mutuncin na fitan hankalin, har da min gorin haka zan zauna ban haihu ba.
"Ai Nagodewa Allah, dan ban samu ba amma ai bayi barci ba, kuma ban makara ba. Yana sane dani, kuma ina ganin girmanki dan haka ki fita kafin na kasa sarrafa fushina." Na gaya mata sannan na wuce d'akina, can sai ga su tare da Jay da Husnah, Mamah Nanah tana kuka take gaya mishi naci mutuncinta.
Ina cikin daki ina cire kayan da zan saka kawai naji ya fincikoni zai mare ni, na rike hannun shi.
"Tsakani na da kai shekaru shida zuwa bakwai! Ashe kuwa baka isa ka d'aga hannu ka dake nie ba, wallahi baka isa ba. Na kuma gaya maka baka isa ba, kana tab'a ni zan rama." Na sake hannu shi na cigaba da abin da nake. Nan ya shiga gaya min magana. Har da ce min dan ya rufa min asiri yana zaune dani duk da ina matsawa rayuwar shi da wari bai tab'a jin ya rabu dani ba. Kai abubuwa marasa dad'i haka ya gaya min. Tun ina iya jurewa har na kasa na shiga mayar mishi, abin da ya haifar mana da zazzafar sa'in'sa, kamar zai dake ni kuma kuma na kafe bai isa ba. Kawai muna cikin haka Mamah Raihanah da Mamah Sarah suka iso, ban san waye ya gaya musu ba.
"Wawuya sakarya wacce ta rasa mijin aure ta makale min." Juyawa nayi ina kallon shi, murmushi nayi domin su Mamah sun shigo, kawai sai ji nayi an kifa mishi marin da ya sashi tsorata, ba kowa bane sai Abban shi.
Domin yana tare dasu Mamah aka gaya musu muna fada, ban ce kome ba, kawai na shiga hada kayana, kallon Abban shi yayi idanun shi jajjur, sannan yace.
"Ni dama na jima da saketa, domin wari take min!"
Sake kwalbar turaren hannuna nayi ya fadi a kasa sai da ya tarwatse, wani irin hawaye ne ya zubo min, na shiga ta cikin kwalbar na wuce na ka rasa kwashe kayana na cikin ma'ajiyar kayana, ina kwashewa ina zubawa a cikin kwatinae.
Waya tace ta kawo wuta, na dauka tare da sakawa a kunne na.
"Na'am Baabina!"
Shiru nayi hawaye na zuba min cikin karfin hali nace mishi.
"Laa babu komai, wallahi kawai muna magana ne akan sha'anin sunan da za ayi ya fara fada, amma wallahi babu kome dan har ya fita ma!"
Sake jadadda min yayi idan akwai matsala na gaya mishi.
"Wallahi na rantse maka babu kome, yanzun ya fita da na bashi wayar." Addu'a yayi min tare da saka min albarka, suna tsaye na kwashe kayana, na zuba a cikin jakkuna na, sannan na dauki babban hijab dina na saka, na shiga ban daki na wanke fuskana na fito, kallona suka yi na sunkuyar da kaina kasa.
"Fatimah! Zaki wuce sokoto yau Insha Allah. Sannan kiyi hakuri Nagode da rufa min asirin da kika yi dan bashi kika rufawa ba wani ne."
Tunda Abban shi ya mare shi yafita, har zan fice Mamah Sarah tace.
"Dawo nan! Mamah ki tafi da ita, Amma wallahi ku duba Alamarin Jay ba haka kawai bane yayi wannan aikin, bamu san me aka gaya mishi ba, kuma kunji yace tana wari akwai matsala fa!"
Juyawa Mamah Raihanah tayi ta sauko, tare da kiran matan shi ta zauna tare da daura daya akan daya tace musu.
"Zan tafi kuma Fatimah zata bar muku gidan ku! Na baku sati Uku! Wallahi tallahi billahil azim, na koma dawowa gidan nan, Jay bai zo Abuja niman Fatimah ba,
Na rantse da Sarkin sarauta. Wallahi sai kun bar gidan nan, kuma sai na baku mamaki," daga haka tayi kiran mu,
Har zata fita tace.
"Ku ajiye magana ta, kar na riga shi zuwa gidan nan, domin kuwa zuwana babu Alkhairi a cikin ta " daga haka ta haura zama muka sauko, tana rike da hannuna, a ranar muka bar garin, su a tunanin su Sokoto na wuce nan kuwa wucewa tayi dani Abuja.
Bayina kuwa cikin gidan suka koma.
Nayi kuka tun kafin na isa, har ina jan zuwa, ai kuwa muna shiga gidan ta fara min balbalin Bala'i.
"Sha-sha-sha, kin zauna hanjin cikin ki, suna saki kuka kekan baki yi kama da jinin sarauta ba, share hawayenki zai zo nan kuma ina nan ina jiran mara kunya."
Tayi min fadar yadda na bari ya rena ni, sannan kuma ta kuma kara min da nasiha, tun daga ranar take yawan jana hira.
--- a can daura kuwa, daga Husnah har Munih kowacce zargin yar uwarta take dan gani suke kowacce tana da wata mummunan manufa, dan haka suka shiga nuna junar su...
Bayan anyi suna, aka watse saura Munih ba, Jay kan Abban shi fushi ya dauka dashi, abin da ya shafi rayuwar shi na yau da kullum, har kowa ya fara fahimtar haka, kuma ya kira Rahil ya gaya mata, itace ta kira babanta ta gaya mishi nan suka dukufa da addu'a da sadaka, ba dare ba rana, kullum yi ake..cikin niman Yardan Ubangiji. Nan ma Daura ba abar su ba, haka ma Sokoto Ummin itama ta maida hankalinta sosai gurin sauka da sadaka.
... Abin da ya matukar d'aga musu hankali, shine yadda wasu abubuwan suke bayyana daga cikin masarautan....
10/23/20, 10:03 AM - Ummi Tandama: *_Ana zaton wuta a makera... Sai a kasame shi a masaka_*
Abin da ya faru ba kome bai ne shine fitowar Hashim baban Fahad yana kalubalantar Jay da rashin adalci, takanas yaje ya sami Jaamal da Aswad da zance bayan sun gaisa. Nan suka shiga hirar duniya. Daga nan ya kawo batun Jay.
"Jaamal da zaka bashi shawara akan ya daina zurfaffa bincike akan iyayen mu, da kome yazo da.."
Ruwan dake gaban Aswad ya sauka ya watsawa Hashim a fuska, tare da mik'ewa ya d'ago kwalar rigar Hashim zai mishi magana Jaamal yace.
"Kyale shi! Manta dashi, kaje ka gaya musu nace bazan iya dakatar dashi ba, duk wanda ya isa namiji ne ya dakatar da shi."
Kallon su Hashim yayi sannan ya juya zai fita. Jaamal yace mishi.
"Albasa bata yi halin ruwa ba, amma mun maka Uzuri." Haka ya fita ran shi a b'ace, yana komaws gidan shi ya sami Fahad yana waya da Qarama, bayan ya gama ya sami Hashim a falo yana gayawa mahaifiyar Fahad abin da Jaamal da Aswad suka mishi,
Shiru tayi kafin tace.
"Amma sun fika gaskiya, taya zaka ce a dakatar da yaron daga aikin da yaƙe? Bayan kai da kanka kake cewa, Yaron yana abin da ya dace, don Allah karka bari haka ya shafi zumunta dake tsakanin mu, domin ko babu kome, mun zama daya ga kuma Fahad da Jannart, don Allah domin yaran mu kar mu girmama abin ya zama babba."
Jikin Fahad yayi mugun sanyi, dan haka ya fita daga gidan baki daya ya koma kofar gidan su ya zauna yana nazarin abin da ya faru da Mahaifinshi. Kuma yayi imani haka kawai mahaifin shi bazai tab'a juya halin shi ba. Dan haka Ya turawa Jay sako.. dake kan shi a sunkuye yake yana d'agowa yaga wasu kartin maza akan shi, kafin yayi wani yunkuri har sun rufe mishi bakin shi. Tare da wurga shi cikin mota, haka suka tafi dashi. Babu wanda ya sani. Cikin abin da bai fi minti arba'in ba sun bar unguwar baki daya.
---
Jay yana zaune yaga sakon Fahad, koda yayi kokarin kiran Fahad din wayar taki shiga sabida rashin yanayi me kyau, dole ya hakura, sai bayan awa biyu ya samu wani sako daga Fahad din da ya turo mishi.
*_Wasu mutane da ban san su ba sun dauke ni. Amma ina da yakinin zaka iya kub'utar dani, idan kuma haka bai samu ba! Jay ina maka fatan Alkhairi sannan ka gayawa Firdausih Qarama ina son ta_*
Turawa Najim sakon yayi, sannan aka shiga bibiyar sakon, abin mamaki a cikin masarautan yaƙe domin har yanzun lokacin Wayar bata daina aiki ba. Dan haka Najim ya turowa Jay sakon.
Allah ya taimaka bai fita fada ba,dan haka ya badda sawu tafi cikin masarautan yana bibiyar bayyanin da ake mishi..
......
Bayan awa daya Allah ya taimaka ya sami Fahad a can a yashe, sannan aka kira shi da wayar Fahad din yana dauka aka ce mishi.
"Ta yaro kyau take bata karko, gashi mun shirya maka gadar zare! Kuma ka fada ka wanke kanka idan ka isa."
"Tsoho me ran karfe na same ka! Ka jira zuwa na katsina."
Daga haka ya kashe wayar, yana mik'ewa Najim suna isowa. Aka É—auki Fahad zuwa asibitin masarautan.
. A nan aka kwantar dashi, dake an kunsan gama wasu shashi na asibitin, dan ma ana wasan kwaikwayo da Jay dan yace babu abinda zai hana shi aikin shi na likitanci, shi yasa yake gayyatar, su Hikmi Abeel su zo suyi aiki a cikin asibitin shi.
Lokacin da ya dawo, zai haura sama yaga wuccewa mutum, bai kawo kome ba, ya nufi dakin Munih me fama da dan karamin ciki, tana zaune sai waya take tana gayawa Mamanta irin kayan da za a saya mata, zama yayi yana kallonta, kashe kiran yayi ya zuba mata ido cikin takaici, domin wallahi bai tab'a jin sha'awar Munih a matsayin matar shi ba.