Sashe 31
Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amma ba a shiga Zariya kai tsaye ba, sai Bakwa Turunku ya gaya wa ‘yarsa Zariya, cewa ta je wajen kufannin iyayensu, wato Kufena kenan, ta je ta fara zama a wurin, kuma akwai rafi a wajen. Sai dai da Sarauniya Amina, wadda ita ce 'ya a wajen Zariya, ta dawo daga yake-yakenta, sai ta ce wurin ya yi fadi da yawa. Idan aka gina hedikwatar mulki a wurin a wancan zamani na yake-yake, to mahara za su iya kai masu hari. Saboda haka, ta ce a koma kusa da rafin da ake kira Fadamar Bono a cikin gari, wanda daga baya da Fulani suka karbi mulki suka mayar da sunan zuwa Fadamar Sarki.
Da aka gama sake shata gari, sai Sarauniya Amina ta sa wa wannan zagayen da’irar da aka yi sunan kanwarta, wato Zariya. Don ta girmama suna ‘yar uwarta, kuma dalilin sunan garin Zariya kenan. Kuma ta gina gida a cikin gari, inda ya zama fadar Zazzau, inda mahaifinta ya zauna, kuma har yanzu nan ne fadar masarautar Zazzau. Ana kiran gidan da sunan ‘Gidan Bakwa�.
*Asalin Ganuwar Zazzau*
A zamanin da, mai karfi shi ke da iko a kasashen Hausa da sauran wurare, saboda haka kowacce kungiyar al’umma da suke so su yi karfi, sai sun kewaye kansu, yadda mahara ba za su shigo masu ba. Wannan shi ne dalilin ganuwa a kasar Hausa, kuma inda duk aka yi ta, an yi ne don wurin ya zama hedikwatar mulki na al’ummar wajen.
To, a Zazzau wadanda suka fara yin ganuwa a cikin gari, aka mayar da cikin gari hedikwata, wato babban birnin mulki na Zazzau, su Bako Turunku ne, mahaifin Sarauniya Amina ta Zariya. Â
Ganuwar Zariya, ita ce ta dauka tun daga dutsen Kufena, ta kewaya zuwa Hanwa, ta shigo wajen barikin soja, inda ake kira Jushin Waje. Ta biyo ta Kofar Galadima, ta Kofar Kona, ta hada da rafin Saye, sannan ta koma ta Gwargwaje, ta hadu da Wusasa, kana ta koma Kufena. Saboda sanin dabarun yaki, sai Sarauniya ta sa bawanta, wato Bono, ya je ya sara da’ira da rafin Sarki a tsakiya ya kewaya aka yi kofofin garin guda takwas, wadanda suka hada da Kofar Kibo, da Kofar Kona da Kofar Galadima, da Kofar Bai, da Kofar Doka wadda a da ake kira Kofar Kano, da Kofar Jatau, da Kofar Kuyambana da kuma Kofar Gayan.
*Sarauniya Amina*
Sarauniya Amina Habe ce ta Zazzau, sai dai wasu masana tarihi na kallon ta a matsayin Sarauniya, amma ba Sarki ba ce, don haka babu sunanta a jerin sarakunan Habe. Ma’ana, akwai sarautu da ake ba ’ya’ya mata a da a karkashin sarautar Habe. Alal misali, akwai Sarauniya, akwai Gimbiya, akwai Iya, akwai Madanni, da dai sauran su. Duk wadannan sarautu ne na ’ya’yan sarakunan Habe.
Saboda haka, Sarauniya Amina ba wai ta zama ita ce Sarki ba, a lokacin mahaifinta (Bakwa Turunku) yana sarki, ita kuma tana matsayin sarauniya, wato babbar ’yar sarki. Bisa al’ada, babban dan sarki shi ne shugaban rundunar sojoji na wannan masarauta.
To, ita Amina ita ke rike da wannan kambi, kuma ita ta yi ta yake-yake. Ta buga daga Zazzau ta yi arewa har Kano, har Katsina, ta kare iyakokin masarautar Zazzau.
Ta yi kudu da yamma, don kara fadi kasa da karfin mulki, kuma da haka ne ta dangana da kasar Naija ta yanzu, ta dangana da kasar Idah, wato kasar Attah Gara a jihar Kogi.
Ta je har kasar Nasarawa ta yau, saboda karfin yaki da iya gudanar da yaki da jaruntaka. Tana da rundunoni da take jagoranta, kuma duk inda suka tunkara suna yin nasara, kamar yadda tarihi ya nuna.
*Sarakunan Habe*
Tarihi ya nuna cewa, an yi sarakuna sittin na Habe, wadanda suka mulki masarautar Zazzau tun daga kan Gunguma, wanda shi ne ya fara yin sarauta a matsayin ‘Madau-Zazzau� na farko a wancan lokaci, kuma shi jika ne na Bayajidda.
Habe sun kwashe shekaru fiye da dari suna mulki, har ya zuwa lokacin mulkin Sarkin Zazzau Makau, wanda shi ne na karshe a jerin sarakunan na Habe, wanda shi ne ya fara zuwa Suleja (wadda aka fi sani da Abu-Ja tun asali).
Ga kuma jerin sunayen sarakunan na Habe:
Gunguma
Matazu
Tumsah
Tumusa
Suleman
Maswaza
Dinzaki
Nagogo
Katchina
Nawanci
Macikai
Kawo
Bashi Kar
Majidadi
Dihirahi
Jinjiku
Sakannu
Monan Abu daga shekarar 1550 zuwa 1530
*Gidan Dan Masukanan daga shekarar 1530 zuwa 1532*
Nohir daga shekarar 1532 zuwa 1535
Kawanissa daga shekarar 1535 zuwa 1536
Bakwa Turunku daga shekarar 1536 zuwa 1539
Ibrahim daga shekarar 1539 zuwa 1566
Karama daga shekarar 1566 zuwa 1576
Kafo daga shekarar 1576 zuwa 1578
Bako daga shekarar 1578 zuwa 1581
Aleyu I daga shekarar 1581 zuwa 1587
Isma’ilu daga shekarar 1587 zuwa 1598
Musa shekarar 1598
Gadi daga 1958 zuwa 1601
Hamza shekarar 1601
Abdullah daga shekarar 1601 zuwa 1610
Burema daga shekarar 1610 zuwa 1613
Aleyu II daga shekarar 1613 zuwa 1640
Muhammad Rabo daga shekarar 1640 zuwa 1641
Ibrahim Basuki daga shekarar 1641 zuwa 1654
Bako II daga shekarar 1654 zuwa 1657
Sukana daga shekarar 1657 zuwa 1658
Aeyu III daga 1658 zuwa 1665
Ibrahim daga shekarar 1665 zuwa 1668
Muhammad Abu daga shekarar 1668 zuwa 1686
Sayo Ali daga shekarar 1686 zuwa 1696
Bako Dan Musa daga 1696 zuwa 1701
Is’haq daga shekarar 1701 zuwa 1703
Burema Ashakuka 1703 zuwa 1704
Bako Dan Sunkuru daga shekarar 1704 zuwa 1715
Muhammad Dan Gunguma daga shekarar 1715 zuwa 1726
Uban Bawa daga 1726Â zuwa 1733
Muhammad Gani daga shekarar 1733 zuwa 1734
Abu Muhammad Gani shekarar 1734
Dan Ashakuku daga shekarar 1734 zuwa 1737
Muhammad Abu daga shekarar 1737 zuwa 1757
Bawo daga shekarar 1757 zuwa 1759
Yunusa daga shekarar 1759 zuwa 1764
Yakubu daga shekarar 1764 zuwa 1767
Aleyu IV daga shekarar 1767 zuwa 1773
Cikoku daga shekarar 1773 zuwa 1779
Muhammad Maigamo daga shekarar 1779 zuwa 1782
Is’haq Jatau daga shekarar 1782 zuwa 1802
Muhammad Makau daga shekarar 1802 zuwa 1804
Yadda wasu wurare suka fita daga masarautar Zazzau
Lokacin da Shehu Usman Danfodiyo ya kawo jihadi a wuraren Hausa Bakwai da Banza Bakwai, Malam Musa yana jagorancin yaki. A tarihince, an ji cewa an kama Zazzau ba tare da an kashe ko da mutum daya ba.
Malam Musa ya shiga Zazzau ta Kofar Bai, a lokacin sarkin Zazzau na karshe na Habe, Sarki Makau ya fita da dakarunsa, ya bi hanyar Hunkuyi, hanyar Kudan, hanyar Kano, tun da an ba shi labari cewa, Malam Musa zai biyo ta hanyar Kano, to sai ya bi wannan hanya.
Shi kuma Shehu Usman Danfodiyo, sai ya ba Malam Musa shawara to ya kauce wa wannan hanya. Ana ganin hakan ba ya rasa nasaba da irin ilhamar manyan malamai na da, bayin Allah, suna addu’a, suna rokon Allah Ya ba su haske da ilhamar yadda abubuwa za su kasance.
Sai aka fada wa Malam Musa, cewa kar ya bi waccan hanya ta Kano, ya zagaya ya bi ta garin Likoro. Kuma haka ya bi, ya zagaya ya bi Farin Kasa da ke kasar Soba ta yanzu, sannan ya bullo wa Zariya ta Kofar Bai, ya kuma shiga garin.
Bayan shi kuwa Sarki Makau yana ta baryar arewa maso gabas, yayin da Malam Musa ya bullo ta arewa maso yamma, saboda haka ba a hadu an gwabza yaki ba.
Da haka Malam Musa suka shiga cikin birnin Zariya, suka rufe kofofin birnin, Sarki Makau na waje, yana jira, sai labari ya isa gare shi, cewa ai Fulani sun shiga Zariya sun kulle kofofi, wato an kori su Sarki Makau kenan.
Daga can Sarki Makau ya gudu, ya nufi kudanci, ya je nan, ya je can, don a lokacin akwai sarakuna irin su Sarkin Fatika da Sarkin Kajuru da Sarkin Kauru da sauran su, wadanda duka da suna bin Sarkin Zazzau na Habe.
Amma da Fulani suka zo, sai suka yi wa Sarki Zazzau Makau tawaye, suka bi Fulani. Suka ci gaba da biyayya, suka kuma zauna a karkashin Sarkin Zazzau musulmi, Bafulatani. Da haka fadin kasar Zazzau ya fara raguwa.
Bayan da Sarki Makau ya bar Zazzau, ya nufi kudanci yana neman goyon bayan kananan sarakunasa da ke can gefe, wadanda tun zamanin Sarauniya Amina aka ci su da yaki, suna biyayya ga masarautar Zazau.
To, Shehu Usman Danfodiyo ya ce, idan mayakan Malam Musa sun sadu da wani wuri da wani babban dutse a kudu maso yamma da Zazzau, su tsaya a wurin. Iyakar daular da yake so ya tabbatar kenan. Inda Makau ya tafi, ya wuce wannan wuri, to, kar su bi shi. Hakan ne kuma aka yi.
Wannan shi ya sa aka kafa Zazzau Suleja a wurin, shi Sarkin Zazzau Makau shi ya tsaya a nan, kuma dakarun Malam Musa ba su ci gaba da bin su ba, suka koma Zariya. Saboda haka, ba a yi yaki da ya wuce wannan wuri ba.
Wato dai masarautar Suleja daga Zazzau ta fito, don haka har gobe masu sarautar Suleja suke kiran kansu da mukamin Sarkin Zazzau, amma Suleja. Shi ya sa za ka ji ana cewa, Sarkin Zazzau Suleja. Kuma duk sunayen unguwannin da ke cikin birnin Zariya, su ne za ka samu a Suleja, kamar su Kwarbai, Anguwan Fatika, su Kusfa, Anguwan Iya da dai sauransu. Saboda sun maimaita wadannan abubuwa da suka baro a Zariya.
Sai dai kuma a wani kaulin, an ce Malam Musa ya ziyarci Zariya ne tun kafin jihadin Shehu Usumanu Danfodiyo, kuma ya zauna a birnin yana koyar da karatun Al-Kur’ani da sauran littattafan addinin musulunci.
To, da jihadin ya shigo, ya kasance yana cikin mukarraban Mujaddadi Shehu Usumanu Danfodiyo, kuma ya sami matsayin ja-goran yaki. Da haka Malam Misa da mayakansa suka kai hari ga Muhammadu Makau, Sarki na sittin a jerin sarakunan Habe, a ranar Asabar goma ga watan Zulhaji a shekarar 1804, lokacin yana filin sallar Idi da ke wajen garin Zariya.