← Book details Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 72

Sashe 44

Magajin Izzah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       "Yan mata! Meye na kwanciya haka? Ko baki son Saif ne?" Lumshe idanuna nayi tare da mai da kaina cikin matashin, murmushi yayi sannan ya kuma tab'a wuyana, zuwa kirjina da yake bugawa.

            Kallon shi na kuma yi, kafin na janye hannun shi daga jikina, a hankali ya zare rigar jikin shi, bayan ya cire aninin rigar shi, sannan ya janyo ni jikin shi tare da had'a jikinmu. A hankali yake zame min rigar jikina.
            Cikin sauri na d'ago kaina, tare da kallon shi, sunkuyar da kaina nayi. Sumbatar goshina yayi cikin jin tausayina, yana shafa bayana.

                       Rabani da rigar jikina yayi sannan ya ja bargon ya rufe ni, sannan ya shiga ban daki ya haɗa ruwan zafi tare da dauko karamin tawol ya fito dashi.

...... Yazo ya shiga goge min jikina, tare da kallon jikina. Yana goge min wayar shi tayi kara, dauka yayi tare da sakawa a kunne, sannan ya cigaba da magana yana goge min jikin. Cak ya tsaya.
"Muniba! Idan kika Kuskura kika min rashin hankali, wallahi idan na dawo sai kin koma Canada, ina gaya miki."

       Shiru yayi tare da wurga wayar saman gadon, sai da ya gama goge min jikin sannan ya dauko abincin ya fara bani, ina yunkurin amai, dole ya mike tare da fita.

             Can ya kuma dawowa, ya sanya min ruwa sannan ya ajiye min sauran maganin da zan sha, kafin ya kalle ni, barci na shirin dauka na, yace.
"Bakin ce min wawan Yaro ba? Ki shirya daren gobe zamu raba reni!" Daga haka barci yayi gaba dani.

   Ban farka ba sai karfe uku, lokacin har an gama tattara min kome nawa, sannan aka fita dashi.

        Ina tashi na wuce ban daki nayi wanka da alola, dakyar nayi sallah, ina idarwa na shiga ɗura abincin kamar wacce ta shekara bata Ci ba.

          ----
Tunda ya gama kula dani, ya isa gurin abokan shi, ya uzura musu lallai su wuce Daura, bai tab'a jin son kusantar matan shi ba, sai yau da ya goge min jikina, anan yaji lallai ya dace da zama angon gaske.

      Tunda suka biyo jirgi suka nufi Daura, yake ɗokance da Husnah dan baya ta Munih.

     Koda ya isa, ya sami gidan a cike mutanen borno sun zo, masalaci ya nufa yayi sallah, sannan ya nufi gidan shi, kiran Husnah yayi suka shiga shashin sa.

      Hmmm! Sai da ya zama angon gaske sosai sannan ya fito, suka haɗu da Munih zata shiga dakin shi ya dakatar da ita.

             "Zan shiga naga Uwar me..." Buge mata baki yayin sannan ya nuna mata hanyar fita.
"Allah zai saka min!"

    Bai kulata ba yayi ficcewar shi, tana ganin ya fita, ta shige dakin shi, taga meke faruwa. Aikuwa hango Husnah tayi tana barci tare da sauke ajiyer zuciya. Tsaki tayi tare da barin d'akin. Kamar ta fashe da kuka.

              ........
Yau jikin shi yake a nitse, sabida yaji abin da kowa yake ji, wani gani gani yakewa abokan shi.

    .---
Hudu aka shiga dani shashin Umman Baabi, tayi min nasiha akan zaman aure shiru tayi bayani akan rayuwar aure da ma'aura, musaman yanda aure ya koma a wannan zamanin,
Da tazo magana akan Matar So, kuwa har wani take tayu musu...
MATAR SO SUNANE DA KOWACE KE SON AKIRATA DA SHI
. Babban gishirin Zaman aure Wanda zai kaiki da mallakar zuciyansa tamakar kin wanke kin bashi ne.
1.Hakuri,
2 .juriya,.
3. ladabi da biyayya. Sai kin jure Zaki Iya hakuri Sai Kuma kinada hankuri zakiya may Ladabi da biyayya.
Babban makamin mace agidan miji Kuma sune
ADDUA ADDUA ADDUA DA MIKA LAMARINKI GA ALLAH.
*BABBAN HANYAR MALLAKA KUMA*
1. Iya girki (ba indomie ko spaghetti ba nope
2. Iya sarrafa Shi a shimfida (Iya jima'i) karki/ka zama lusari
3. Iya Magana. Kisan irin kalaman da Zaki dinga furtawa. Iya mu'ala da mutane. Yin adalci kyautata zato da Kuma yin uzuri.
Ta cigaba da cewa.
"A wannan zamanin iyaye muna sakaci da yawa yarinya ta girma har tayi aure baki nusar da ita rayuwar aure da rayuwar da zatayi anan gaba ba, maxan ysnzun basu damu da ki musu, wani abin azo a gani matuƙar zaki riƙe girki iya sarrafa harshe, ya sarafashi a gado, mutunta danginshi maida damuwarshi naki, ki kambama alamarinshi fiye dana kowa,

Karki ce ya cika fushi ko yana da miskilanci a'a ke zaki koya mishi sakewa dake dakuma sauran mutane, Matar fari itace ke fara lalata alamarin namiji duk yanda kika É—aurashi haka zai mike, sannan akwai kura kuran damuke aikatawa, rashin yin kwalliya a gidajenmu sai zamu fita unguwa, zan muku misali dani kaina, na zauna a cikin gidan nan dadda tun kuruciyar mu har girman mu ko jagira banyi nafita dashi toh waye zanwa a waje ? bayan ina da wanda ya ajiyeni namishi,! wannan É—abi'ar tasamu mazauni a cikin zukatar Yarana baki É—aya, idan mace takai mace kuma ta amsa mace babu malamar da zata zauna da ita tace mata ga yanda zatabi da namiji, sabida rayuwarshi kamar na É—an shekara uku ne, da zaran ya tada rigimar shi, sai ki duba dabi'ar karamin yaro ki gani, da zaran ya fara kuka zan faÉ—i a kasa yayita shureshure, a lokacin zai baki haushi kaman ki jibgeshi amma idan kika tuna da, cewa kukanshi kara miki zafin kai zaiyi, niman alewa ko wani abu zaki fara dan ku rabu lafiya,

Toh namiji ma haka yake shi bazai faÉ—i ba, amma zai koma gefe yayita huci idan kina da wayo, a lokacin sai ki saukar da kai ki bashi hakuri, idan kika ga yaki sa shi a gaba kita rarrashinsa, wanda idan kinga zaki iya saka mishi fitinanne kuka shi akawa laifin tuni zai manta da wani rigima ya sauko, toh a lokacin sai kiyi amfani da damar haka ki bashi hakuri dan zai damu shi akawa laifi ke kuma kike kuka, Mata muna da matsala a rayuwarmu sosai bazamu iya rarrashin miji ba amna zamu iya rarrashin mai saida É—an kunne dan yayi mana sauki,, haba mata ina hikimar tamu take ina kwarewar tamu take, tunda Asiyah ta iya bawa fir'auna shawara ya É—auka waye ne mijin naki da bazai É—auka ba,

Ummu Salma an karɓo daga gare a hadisin da buhari da musulin suka rawaito.

Tace manzon Allah yana zama yayi shawari dasu, akan alamuran addini ko, kuma wani yaki, indai manzon Allah zaiyi shawara da matarshi ke wacece da bazaki bawa mijinki lokacinki ba, ina kira gareku mata yan boko karki ce aiki ya hanaki kula da miji, zakiyi kuka nan gaba idan ya auro undergrad, kina ji kina gani zai, mai dake gefe ya saka wancar a gabanshi idan bai yi haka ba toh yar aikin gidanki da kika bar mata gidan ita zai aura, idan mai tunani da tsoron Allah kenan idan kuma aka rasa haka, kina ji kina gani zai na bin yar aikinki suna masha'arsu, ko kuma yaje waje nima, wallahi muji tsoron Allah, wai tsabar rashin daraja a gurin mace mijinta zai raba gurin kwanciya da ita, sabida tana wari da hamami, wai nikam mi kuke shirin zamane matan arewa, tun a gida zaki koya mata gyaran jiki girki tareraya, iya magana, sabida sha'anin rayuwa baki san inda xata zauna ba, amna ina sai dai ki koya mata shan maganin mata, karki manta kishiyoyinki can yayi kyau amma rayuwarta ba kyau, wannan zuri'anmu guda biyu É—aya take cewa.
"Ana surutun Aanih ta lalace, abinda da wasu yaran suke a cikin Zuri'ar waye ya isa ya faÉ—a?

Ko su da suke auren wani kwanciyar hankali suke samu da ake mata gorin taki aure!.
Abin tausayi, sai nayi murmushi sannan nace musu suyi hakuri,

Fatimah karki manta wacece ke? Shin idan kika zauna lafiya a dakin ki, hankalin waye zai kwanta? Idan kika kaso auren ki suwaye zasu miki dariya
Da haka nake miki nasiha ki gyara rayuwar aurenki kija mijinki da danginshi a jiki wani sabon salo wai kuna kiran iyayen miji da ulcer ko hawan jini, a'a kuskure ne, ke zaki rushe dangantsrku ke zaki gini, ina da suruka, naki na saka ido akanta da mijinta, ina da yara mata baxan so nimaa cutar min dasu ba, akan Yan ukuna zan kwaɓe hijab da rigar malamta na gurzawa surukina rashin kirki, dan ni nasan abinda na bashi, idan yace min bata da kunya shi xan fara tuhumq kafin na tuhumeta, sabida karfe ɗaya baya amo sai da wani a kusa da shi, karki manta shi tashi Uwar bata raye sai mahaifin shi,.da matan Ubanshi.

Sannan zaki zauna da yara ƙanana masu karancin shekaru irin naki, shi zaki zauna ki biye musu ne kuyi ta abin kunya, kin san waye mijinki, dan akan laifin mari kawai ya iya wargaza miki lissafi toh idan kuwa haka ce Tabbas idan ya birkice miki zaki iya dakatar dashi.

Toh dole kiyi amfani da shekarunki, na farko kija girman ki, na biyu ki zauna lafiya a dakin mijinki koda kuwa matan shi suna tsaye akanki, zaman shi suke zaman shi kike, ke baki isa koran su ba, haka kema baki isa koran shi ba. Akan me zai saka ki d'aga hankalinki.

Fatimah Aryaan yana bukatar ki nutsu a dakinki, yana bukatar hakurin ki, hakurin nan yake bukata, shi yake son kiyi! Ana ce muku...
#Mai_Dambu
10/23/20, 9:58 AM - Ummi Tandama: *Ba a yi ciki dan tuwo kawai ba*

Dole kiyi hakuri da shi sabida kin fishi shekaru, matan shi kuma kusan kanen ki ne, shima din haka, duk wanda ya ce miki zaki yi aure dan jin dadi yaudarar ki yayi, domin ita rayuwar auren domin hakuri aka gina ta.

Dole harshen ki ya zama yana tafiya da kamaninki, ki zama wacce fuskarki bai tab'a nuna damuwarki ba.
Chapter 44 · 0% Book details