← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 68

Sashe 8

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su Inna gida suka wuce da Dahiru yayin da Baba da Baffa suka tsaya yana yi masa bayanin yadda abin ya faru. Ade har tayi hanyar gidansu wanda iyayen Mal Fatihu da Iyarta suke ciki tare sai ta fasa. Gidan Mal Isiyaku ta wuce kai tsaye.

Ummiyo ce ta amsa mata sallama Inna ta zaga bayi. Tana fitowa tayi arba da Ade a tsakar gida tace ta shigo cikin rumfa. Dahiru yana bayansu duhu yasa basu ganshi ba. Zai shiga kawai ya ga Ade ta durkusa a kasa gaban Inna tana kuka sosai.

"Don darajar Al'Qur'ani da iyaye Innar Dahiru ki rufawa yarinyar nan asiri. Na sani maganar aure da Dahiru ko ba'a fada ba ta tashi kamar yadda nasan da wuya wani ya taba aurenta. Amma ki taimakeni ko don kada zaman garin nan ya gagaremu don Allah ki rufa mana asiri"

"Haba Sa'ade sai kace wata bare? Wannan magana nayi miki rantsuwar duk ranar da kika ji ta a waje to daga bakin wani ta fito ba ni ba. Bazan taba fadawa kowa an yiwa Mawadda fyade ba. Kinga ai bamu ma san takamaimai me ya faru ba"

Dahiru ja da baya yayi har wani jiri yake ji. Tausayi sosai Ade ta bashi. Motsin da yaji a bayansa yasa shi juyawa ko ma waye ya gudu kafin ya waigo.

Har Ade ta fito tana ta yi mata godiya. Ita dai Inna bata da niyar tozartasu amma taji dadin da kafin magana tayi nisa Ade ta gane cewa batun auren nan a barshi kawai.
****

Kusan tare Ade da Baba suka shiga gidan iyayen nasu. Iya tana daga dakin farko idan an shiga wani soro sai 'yan tumakinta. Daga soro na biyu kuma tsakar gidan iyayen Mal Fatihu ne wato wa ga Iya. Rashin jituwa da dangin miji bayan rasuwarsa yasa ta dawo gidan.

Suna sallama Innar Fatihu da Malam babansa da Iya suka taso suna tararsu da tambayoyi.

Malam yace "kun daga mana hankali yara tun dazu sun zo sun ce Mawadda ba lafiya. Tana ina yanzu? Yaushe ta dawo garin ma duka bamu da labari?"

Iya kuwa harara ta dokawa Ade "wani sabon salon kinibibin ne kika shigo garin nan sai a bakin jama'a naji wai kin fara biyawa gidan tsohon mijinki."

Baba na gaisheta kamar yadda ta saba tun rabuwarsa da Ade ta juya masa keya harda tura dankwali gaba.

Innar Fatihu ta tabe baki "ke kam zan ga lokacin da zaki girma, yaro na gaisheki kina juya keya abu duk a gwaguye"

Sanin cewa yanzu zasu fara rigima Malam ya tsawatar "bana son shirme, ance yarinya ba lafiya baku tambayi halin da take ciki ba sai rigimarku da bata karewa. Sa'ade ina kuka barota?"

Daga ita har Baba duka jikinsu a sabule ga idanunta a kumbure saboda kukan da bata san adadinsa ba a yau.

Baba ne yace duka su zauna magana mai mahimmanci zasu yi. Jin haka Iya ta kwala ihu harda zaman 'yan bori ta soma kuka haikan tana fyatar majina.

"Ni Tarasulu me zan gani, wayyo Allah mun shiga uku mun lalace."

Ade ta bata rai ganin wannan abu da mahaifiyarta take yi "Iya meye haka kuma don Allah?"

Sake fyace hanci tayi sannan ta dago "cha nake ta cika ne, na ga ke da Fatihun kamar kwai ya fashe muku a ciki gashi yace magana ce mai mahimmanci"

Malam ya girgiza kai cike da takaici.
"Fatihu ina jin ka kaji"

Kai a kasa Baba ya soma labarta musu abinda ya sami Mawadda. Kafin ya kai karshe Iya ta mike tana kumfar baka zani na neman faduwa tana kamo shi

"Qur'anin Allah Fatihu baku isa ba...tabdi yo ni na taba jin danyen aiki irin wannan ma. 'Ya'yan Haule sunje sunyi aikatau dinnan kowacce ta kai mutumci gidan miji sai tawa jikar saboda ka tsani uwarta. Idan ma wata manakisa kuka shirya ku kwance don billahillazi bazan yarda ba." Duk da fada take yi sai kuka kuma yaci karfinta. Ba karamin so take yiwa 'yan jikokinta ba musamman Mawadda abokiyar fadanta. Yarinya ba sawa ba fitarwa har haushi take bata. Ade ta riko hannunta suka zauna tana ta kuka da mita.

Malam da Innar Fatihu suma abin ya taba su. Shawara aka tsayar da safe zasu koma asibitin da kuma tsawatarwa cewa su iya bakinsu kafin magana ta fita don bazata yiwa kowa dadi ba cikinsu.

Iya ta mike tana gallawa Baba harara "da yake ba jikar da kuke son uwarta bace shine zaku ce sai da safe zaku je. To ni yanzu zan tafi. Ke kuma.." ta dungure kan Ade "kin kwaso jiki kin dawo gida har zaki iya bacci kin bar yarinya a wannan halin"

Innar Fatihu ta kada baki tace "Abin ko kara babu dadin abin nima jikata ce"

"Da nayi karar ba ga irinta nan ba. Ca nake 'ya'yan Haule har biyu a Habuja suka yi aikin. Daya a Jos dayar kuma a Fatakwal ina nan rahoto na zuwa gareni. Sai ni don an raina mu nan nan Kaduna fa aka kai min Mawadda. Ina Kano ina Kaduna banda wulakanci. Kuma ku kwana da shiri harda shi shegen gorar ya taba min ita magana bata mutu ba. Idan ana yiwa 'ya'yan mutane fyade a binne magana a bar yarinya da bugun zuciya to Yasin ni sai mun shiga kotu. Yaro ko daga gidan Karuna ya fito zamu kara ai talauci ba hauka bane."

Har ta bar tsakar gidan ana jiyo sababinta. Ade ta tashi zata bita Malam ya hana. Da kansa yaje ya sameta tana laluben jaka wai zata tafi asibiti da shirin kwana. Harda bashi sallahun ya fadawa Fatihu matarsa komai dare zata dawo.

"Tarasulu bana jindadin irin wannan halaye naki ko kadan. Kiyi hakuri zuwa goben da wuri zamu tafi. Sa'ade da Fatihu duk 'ya'yana ne ko don kaddara ta rabasu sai mu kasa hakuri komai sai mun fassara shi da cewa da gangan akeyi. Ki rinka tauna magana kin girma fa."

Shiru yaji tayi ga mamakinsa ashe kuka take yi "yaya fyade ne fa? Yarinya kamar Mawadda mai zurfin ciki ta hadu da wannan bala'i ina zata saka kanta? Wallahi ko dan uban waye yaron nan bazan barshi ba. Allah Ya isa, Allah Ya kwashewa duk wani mara imani mai wulakanta da tozarta mutumcin mata yara da manya domin biyan bukatarsa"

Kukanta ya taba masa zuciya sosai. Su kadai suka rage a gidansu basu da kamar juna. Da kyar ya lallabata ta hakura zuwa wayewar gari. Sai dai babu wanda ya runtsa cikinsu kamar yadda a asibiti ma Yaya bata yi baccin ko da awa daya ba saboda yawan tashin da Mawadda take yi tana ihu.
*****

Tara na safe a asibitin tayi musu gabadaya. Yaya tana gaishe da Iya taki amsawa sai harare harare takeyi ita ba'ayi mata adalci ba.

Ganin Mawadda duk ta kare shi yafi daga mata hankali. Tana kuka tana surfawa BB tsinuwa da Allah Ya isa.

Duka zaman jiran likita suke yi sai ga sergent Bala da Nalado sun dawo. Ba jimawa Dahiru ya shigo ya gaishe da kowa na dakin.

Rabonsa da Mawadda tun ranar da zata tafi aiki sai jiya. Yau yana dago kai suka hada ido tayi saurin rufe nata hawaye na biyo baya. Me ya kawo shi inda take bayan yanzu bata da sauran daraja da kima? Ita din yanzu abar gudu ce da kyama ta tabbatar maganar aure tsakaninsu tuni tabi iska.

'Yan sanda sun nemi ta sanar dasu yadda abin ya faru sai dai idanun jama'a yasa ta kasa sai zubar hawaye. Idanunta har wani kwarmi suka yi saboda yini kuka. Ganin haka aka sallami kowa sai Babanta da Iya wadda ta dage babu inda zata je. Ita ta rike hannun Mawadda ta fada musu abinda baki zai iya fada. Iya tayi kuka har muryarta ta dashe. Kofar dakin ta dawo ta zayyane musu halin da Mawadda ta shiga a hannun BB. Duk wanda yake wurin yaji tausayinta sosai. Dahiru zuciyarsa kamar ta buga. Ji yake inama shi din wani ne da ko ya bar BB da rai sai yayi masa abinda idan ya ga mace ko da tunkiya ce sai ya canja hanya. Abu daya ya kudurcewa zuciyarsa shine aurensa da Mawadda babu fashi. Idan da yana sonta ne yanzu kaunarta da tausayinta sun taru sunyi masa yawa a zuci. A shirye yake ya fuskanci iyayensa da duk wanda zai nemi hana shi aurenta saboda yasan hakan shine daidai. Kasancewa da masoyi a lokacin da kaddara mara dadi ta same shi shine cikar soyayya.
[03/12 23:02] Meela Adeel: *GUMIN HALAK...*馃挵5

*Batul Mamman*馃挅

Bayan dan lokaci 'yan sandan suka fito. Sun bawa Baba shawara akan cewa idan yana bukatar maka BB a kotu sai yayi shiri sosai saboda shari'a yanzu sai da kudi. Sannan zasu zo da abokin aikinsu wanda zai dauki hotunan raunukan jikinta washegari saboda kafa shaida. Mutanen sun basu tausayi musamman Mawadda. Har hakuri suka bawa Baba wulakancin da suka yi masa a ofishinsu. Godiya yayi musu shima ya raka su sannan ya dawo dakin.

Iya tana rungume da Mawadda kamar za'a kwace mata ita. Da yake sun taho da abinci Innar Fatihu ta zuba mata kunun gyada fari kal yana ta kamshi amma taki karba.

Yaya tace "Inna haka muke ta fama taki cin komai. Jiya nayi fadan nayi nasihar amma duk a banza"

Nan fa suka shiga lallabata amma da aka matsa mata ma sai tasa musu kuka
"Ku barni yunwa ta kasheni na huta don Allah"

"Ahir na kuma jin wannan zance Mawadda. Kin taba ganin bawan da yafi karfin jarabta daga Allah?" Cewar Innar Fatihu

Iya ta tsuke baki
"Ya haka ne, abin kiyi mata sannu-sannu sai fada saboda dai...."

Malam ne ya katseta "za'a sai da hali ne Ta Rasulu? To dai asibiti ne ba gida ba. Sai mu koma inda muka fito iyayenta suyi jinyarta"

Shiru tayi babu wanda ya sake cewa uffan kada Malam ya korasu gida.
Chapter 8 · 0% Book details