← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 68

Sashe 50

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

BB ya shigo daga bakin kofa ya tsaya "kinsan bani da kyau Mawadda. Ki ajiye wannan haukan mu zauna lafiya kafin na tuna miki da waye BB."

Wukar ta saita a wuyanta har yanzu tana kuka amma kokari take ta dake zuciyarta domin idan tsoro yayi galaba ta suma shikenan zai sami yadda yake so "da ka tabani BB gara na kashe kaina"

A karo na farko da yaji tsoro kenan. Duk wahalar da yasha meye ribarsa idan ta mutu.

Ja yayi da baya "ajiye wukar kizo muyi magana. Ga wayarki nan" ya fito da wayar daga aljihunsa sannan yace "kizo ki kira ko ma wa zaki kira don baki isa na kaiki gida ba"

Jiki na rawa ta yar da wukar sannan ta taho bakin kofar ta mika hannu "bani"

Cafkota yayi yana kokarin hadata da jikinsa ta suka soma kokawa yana shirin fara yi mata muguntarsa ta duka ta dage ta kai masa wani naushin hauka a kasan mararsa sai gashi ya saketa ba shiri yana kurma ihu kamar mahaukaci. Wayarta ta dauke ta koma dakin ta rufe tana numfarfashi.
*****

Su Baffa sun iso daga Tariwa gidan Mal.Fatihu ya cika da 'yan jaje kamar ba dare ba. Dahiru da Attahir suna kofar gidan a mota bayan sun gama magana da 'yan sandan da suka zo.

Hannunsa da ya soma kumbura Attahir ya kalla "don Allah ka amince muje a gyara hannun nan kaga har ya fara kumburi"

"Ka barshi baya min ciwo"

"To idan ba'a gyara ba me zaka dauki 'Yar uwarmu idan ta dawo? Kada kace min da kafarta zata hau saman nan kana biye da ita"

Murmushi Dahiru yayi "nagode Attahir"

"Da me?"

"Komai ma, amma ka tafi wurin Nawal don Allah"

Daure fuska Attahir yayi "iyakar amintar tamu kenan Dahiru? Kana cikin wannan yanayin in shiga dakin amarya inyi me?"

Marwanu ne ya kwankwansa gilas din motar yace su shigo ciki akwai baki.

Da su ka shiga Dr Tani ce tare da mijinta da Qareeba da bata iya tafiya sosai sai an riketa. Ko zama Dahiru baiyi ba ya fita abinsa. Tana kuka ta shiga basu hakuri har take nuna musu Qareeba da labarin abin da BB yayi mata.

"Kinsan ance komai nisan jifa kasa zai fado. A da baki damu da halin da wannan iyali zasu shiga ba da abinda kika yi musu. Sai dai gashi tun a duniya kina ganin sakayya" cewar Baffa

Dr Auwal ya tayata basu hakuri da basu taimako wurin neman 'yarsu domin su ma neman BB din suke.
******

Loba boy ya sami wani gefe ya tsaya ya kira Garwashi.

"Oga hasashenka fa ya zama true"

Garwashi ya ture yarinyar da ke kusa dashi a wani club a Kaduna ya matsa gefe.

"Ina sauraronka me Danmani yake yi?"

Kwanaki biyu da suka wuce kafin Garwashi ya koma Kaduna ya ga Danmani da sabuwar waya. Yana tambayarsa sai cewa yayi cikin kudin da suka raba ya siyo. Garwashi ya karba yana gani shi kuma Danmani shaf ya manta da hotunan Mawadda da ya daukowa BB. Batare da nuna fushi ba yayi saurin rufe folder din hotunan ya cigaba da dube dube amma zuciyarsa ta bashi babban yaron nasa ya ha'incesu ne shiyasa da duka suka yi shirin komawa Kaduna yace yana da uzuri sai Garwashi ya rabu dashi amma ya bar Loba boy yana binsa a boye.

Shi Loba boy ya jima yana harin mukamin Danmani yana son zama na hannun dama sai yanzu dama tazo.

Garwashi ya gama jin bayaninsa na satar amarya ya kutuntuma ashar "kai baka wurin nace zamu yi mata solidarity saboda 'yar uwa ce 'yar Kano ce?"

Loba boy an sami yadda ake so zai ture gwamnatin Danmani yace "Oga alakar tafi haka ma. Sai da abin ya faru na gane ashe dangin matar kawuna ce"

"Bana son shafta Loba boy. Ita da suke Bebeji kai kuma Dawakin kudu?"

"Oga ashe baka sani ba Bebejin daga jikin Dawakin kudu aka yanketa lokacin mulkin sojoji"

Garwashi rai ya baci kuwa jin haka yace "kace dai wannan rigimarmu ce ta famili lallai Danmani don wulakanci abin kuma harda tabo gida"

Loba boy ya cigaba da ingiza shi yace kada yayi komai gobe da sassafe zasu taho Kano.
******

Sun cika alkawari kuwa domin karfe goma da rabi ma a garin Kano tayi musu. Zama suka yi kamar wasu 'yan sanda suka gama tsara yadda zasu sulala Danmani kamar tafasasshen nama.

******

Yadda Mawadda bata runtsa ba haka su Dahiru suka kwana tare da iyayenta. Gari na wayewa suka koma ofishin 'yan sanda aka sanar dasu ana bincike sosai su cigaba da addu'a.

Hannun Dahiru ya kumbura Baba da kansa ya nemi mai gyara aka matsa matsa ya shigo ciki lokacin ya matsawa Attahir shima ya tafi gidan Baba Prof ganin Nawal.

An gama gyaran Attahir ya dawo yaci karo dasu Garwashi a kofar gidan. Wai saboda kada ace musu 'yan daba shine duka su biyar suka sako manyan kaya burum burum kamar wasu barayi.

Hannu Garwashi ya mikawa Attahir suka gaisa yace sun kawo taimako ne suna bukatar izinin ganin iyayen amaryar da aka sace ko babanta.

Attahir ya hade rai "kun zo damfara dai to ayi gaba mun yafe"

Garwashi ya rage murya yace sun zo da bayani ne akan BB. Janyo shi Attahir yayi suka yi ciki sauran na biye dasu.

Baffa yace "wadannan fa?"

Garwashi yace yana so a rage jama'a ko su sami wuri da zasuyi magana babu takurawa domin aikinsu na bukatar sirri. Ba don sun yarda ba sai don ganin Dahiru ya tada hankalinsa yace a sauraresu suka tashi suka koma dan falon nan. Wuri ya cunkushe Attahir yace ko zasu koma gidansu ne tunda Garwashi yace baya son hayaniya a bakin aikinsa. Mamaki suke yi amma ga dukkan alamu dai bai yi kama da irin malaman bogin nan ba. Rankayawa suka yi gidan Baba Prof aka zubawa su Garwashi idanu.

Dariya yayi ya soma musu bayanin kansu da haduwarsu da BB da kuma sa hannun Danmani da suke zargi.

"Zamu taimaka saboda munyi alkawarin solidarity ga 'yar uwa. Kuma ashe ma dangin matar kawun wannan ce ta wajen kakarta mace ko? " ya nuna Loba boy.

Inna da Iya suka kalli juna. Iya tace "ko kece naga kamar yana da billenku?"

Innar Fatihu ta rufe billenta da sauri "meye haka ne TaRasulu?"

Baba Prof yace sun basu dama amma idan suka ga ranin wayo su shirya zasu damka su wurin 'yan sanda ne.

Garwashi ya dubi wani yaronsa ya ce masa fara.

Yaron ya bukaci shiru banda ko da tari ne sannan ya kunna wayarsa ya bude recorder ya karkace kai sai gashi ya fara muryar Nasiru Salisu Zango

_"a yau ne kuma majiyar inda ranka take dauke da labari mai cike da al'ajabi inda iftila'i ya afkawa wata amarya. Amaryar dai wadda danginta suka bukaci a sakaya sunanta wasu bata gari ne suka yi sama da fadi da ita kamar allura an nemeta an rasa a cikin zugar kai amarya. Yanzu haka iyayenta da sabon ango suna cikin gagari suna rokon duk wanda yake da wani bayani da zai taimaka wurin ganota ya nemesu ta wannan lambar waya da zan bayar. Angon harda alkawarin kyauta mai tsoka ga wanda ya sada shi da amaryarsa. Ga dai yadda mukayi da angon"_

Matashin da baifi shekaru ashirin da shida ba ya sake karkata ya kyabe fuska kamar mai kuka sai ha murya ta fito a raunane

_Don Allah ko waye ya dauketa kada ku cutar min da mata. idan kudi kuke so zan bada miliyan daya da rabi ga duk wanda ya taimaka ko yaya ne_

Daga nan ya sake komawa muryar Zango _"to Allah shi kyauta amma ga dukkan alamu lokaci yayi da za'a fara daukar rijistar masu zuwa daukar amarya."_

Kusan kowa sakin baki yayi bayan yaron ya gama Garwashi ya kira Danmani yasa wayar a speaker. Dahiru da Baba suka matso kusa yayi musu alama da suyi shiru.

"Oga ya kana lafiya?"

"Kai Danmani kana Kano abu irin wannan ya faru baka fada mana ba sai wani ne cikin abokai na yace yasan ina da network ya turo min rakodin din"

Danmani ya dan tsorata "ban gane ba Oga"

Garwashi ya rage murya "kaga yanzu nake ji an sace wata amarya jiya angon yayi alkawarin miliyan daya da rabi. To nafi son muyi aikin nan mu biyu a kyale su Loba boy yadda kake ta bani shawara"

Tashi Danmani yayi jiki na bari bayan Garwashi ya kunna recording din da ya manna da wayarsa ya gama ji. Yace masa "ance Kano ta rude mutumina kowa na son nemota, ni kaina sammako nayo na shigo gari kazo mu hau aiki"

Danmani mayen kudi wanda shine babban lagonsa yace "Oga ina jin fa mutumin nan BB ne ya sace matar da ya tura mu aiki a kanta. Haka kawai hankalina bai kwanta dashi ba bayan ya bamu kudin nan har gidan da yake nabi bayansa rannan. To amma daga baya na share. Kana ina ne mu hadu sai mu nemi angon. Sai dai banji lambar wayar ba"

Garwashi yayi murmushin saurin kama Danmani "bari naje gidansu mu tabbatar sai na sameka a cikin gari mu wuce"

Babu wani dogon tunani Danmani ya amince. Shi akan kudi dama kansa toshewa yake. Dahiru ne ya bawa kowa mamaki da yazo ya rungume Garwashi yana masa godiya tun ba'a ganta ba. Jiran minti shabiyar suka yi bayan anyi notifying 'yan sanda amma basu sanar dasu su waye Garwashi ba domin sunyi musu halacci.

Danmani doki ya hana shi sakat ya kira Garwashi yace su hadu a hanya. 'Yan sanda suka yi basaja akayi akayi Dahiru ya zauna ba'a sani ba ko suna da makamai ya dage sai yaje.
*****

BB yayi kwanan izaya don ya daku fiye da tunaninsa. Gumi yake ta yarfewa a nan falon ya kwana a yashe. Mawadda tana daki tana kuka bayan tayi sallah. Wayarta ta kalla ta sake fashewa da wani kukan. Ashe fanko ce ya cire batir din.

Da kyar ya tashi ya rarrafa ya dauko wayarsa ya kira Bobo yace yazo ya kaishi asibiti. Sannan ya koma kofar dakin yana bugawa yace idan bata bude ba har ya bude da kansa zai bata mamaki.
Chapter 50 · 0% Book details