← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 68

Sashe 68

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Zantukansa duka ta bayan kunne suke shigarta tunda ya rike mata hannu. Bakon yanayi na farinciki ne yazo gareta amma ga mamakinta sai da ta tuna BB a wannan lokacin. Kukan da taki yi a gida ne ya kwace mata sosai take yinsa yana dagawa Bilya hankali. Yayi zaton kukan rabuwa da gida ne yayi ta rarrashinta har suka isa gidan.

Hannu ya mika mata don ta fito sai taki kamawa saboda tsoron kada ta sake jin yanayin dazu. Bai kawo komai ba a ransa suna shiga gidan da yaji komai na morewa aka fara kiran isha. Masallaci ya fita ya barta a zaune. Sai da taji gidan shiru ta tashi tayi sallah.

Tana idarwa batare da ta tashi daga kan abin sallar ba ta dauki wayarta ta kira Mawadda.

Kwance take komawarsu gida kenan duk ta gaji ko kayan jikinta bata iya ragewa ba. Sunan Qareeba ta gani gabanta ya fadi.

"Antinmu lafiya dai ko?"

Kuka Qareeba take yi da gaske "Mawadda yaya zanyi? Ya kika yi ke? Wallahi BB ne yake fado min gabana sai faduwa yake kamar in koma gida"

A take fuskar Mawadda ta sauya itama ta soma kukan tana tausaya mata.

"Antinmu kiyi hakuri kuma ki sakawa ranki wannan masoyinki ne wanda ya aureki domin Allah ba don jikinki ba. Ki daure zuciyarki domin a duniya bamu da masoya sama da masu aurenmu duk da wasu sun rigasu ganin tsiraicinmu sun tozarta mu da wulakanta mana rayuwa"

Kukan Qareeba ya tsananta itama Mawadda haka.

"Ina son Bilyamin sosai Mawadda amma zuciyata ta karaya. Bazan taba yafewa BB ba ina fatan ko ina yake Allah Ya kara saka mana"

"Amin Antinmu Allah Ya kare sauran mata"

Kuka suke ta yi suna rarrashin juna sannan suka ajiye wayar.

Dahiru yana tsaye a jikin kofa yana jin yadda take kuka kuma ya fahimci da wa take wayar. Idanunsa ne suka yi ja yana kara jin tsanar BB a zuciyarsa. Shigowa dakin yayi Mawadda ta taso daga kan gadon da sauri ta rungume shi.

"Zan kai karar Anti Qareeba ta taba min mata"

"Ayi mata afuwa amarya ce"

Mayafinta ya soma warewa "Baki cire kayanki ba ko babu nauyi?"

Kwantar da kanta tayi a kirjinsa "jira nake yi ka dawo ka cire min na gaji"

Ya dage gira "in gasa miki jiki kuma tunda kin kwana biyu babu hutu"

Ta gyada kai tana sake shigewa jikinsa ya.

******
Qareeba ma ashe Bilya yaji duka wayar da tayi. Tausayinta da sonta ne ya sake shiga ransa. Yana matsowa gareta tana yin baya idanu kamar su fado don firgici. Binta yayi ta yi har suka isa jikin bango.

"Ya muka yi dake?"

"A ina?" Tace a tsorace.

"Kince bazaki taba bari abinda yaron nan yayi miki yayi tasiri a ranki ba. Me ya faru yau? Tsoron Bilyaminu kike yi?"

Ta girgiza kai hawaye yana digowa.

A nutse yake kallonta tayi masa kyau. Mayafinta ya cire a hankali yana yi mata magana.

"Ni masoyinki ne, ni mijinki ne, ni abokinki ne wanda bazai taba cutar dake ko son ganin hawayenki ba."

A hankali tace "kayi alkawari?"

Hannuwanta ya janyo ya rungumeta tsam a jikinsa sannan yace "nayi alkawari...amma akwai 'yan lokutan da zan dan sakaki kukan kadan"

"Kamar yaushe?" Tace da karamar murya.

Dan bakinta ya zana da yatsansa yana kallon fararen idanuwanta "kamar daren yau" sannan ya hade shi da nasa.

*******

Cikin Nawal yana da wata hudu Mawadda ta soma nata laulayin. Murna a wurin Dahiru baa cewa komai. Wannan karon ita take shagwaba son ranta yana biye mata.

Ranar da Qareeba tazo sun sha hira sosai suna karfafawa juna gwiwa akan kaddararsu. Amincinsu ya dore fiye da zato da tsammani.

Nawal ce ta fara sauka ta haifi da namji kyakkyawa dashi kato. Farat daya ya shige zuciyar Mawadda har ana tsokanarta ko mace zata haifa ne ayi 'yar gida.

Attahir ya bawa Dahiru damar yiwa yaron huduba da suna Ahmad wato mahaifin Nawal. Wata hudu a tsakani Mawadda ma ta haifi nata kyakkyawan bafillacen da ya dauko mahaifinsa sak. Shima Attahir ne yayi masa huduba da sunan da Dahiru ya zaba wato Abdulhadi (Abdul).

Anyi taron suna inda 'yan uwa na kusa da nesa suka halarta.

Yaransu sun taso cikin kulawa daga iyaye biyu a bangare guda kuma Dahiru ya bawa Mawadda shawarar bude kungiya da suka sanyawa suna _GUMIN HALAK_. Wannan kungiya da kudin da Alh Sule ya bata suka kafata wadda zasu rinka kai taimako da agaji ga duk wani mai karamin karfi da iyayen gidansa suka tauye masa hakki bisa zalunci musamman mata 'yan aiki wadanda ake duka ko yiwa fyade.

Cikin dan kankanin lokaci kungiyar ta bunkasa inda aka sami likitoci, lauyoyi da manya sukayi hadin gwiwa dasu domin kwatowa mutane 'yancin da talauci ke sawa a danne musu. Mutanen da suke neman halali da guminsu aka tozartasu.

Ahmad na da shekara daya da wata hudu Abdul kuma shekara daya Qareeba ta haihu. Bakin Dr Tani kamar zai hade da keya Qareebanta ta haifi 'yan biyu mata kyawawa dasu. Dakin cike yake da mutane Bilya yana gefen matarsa don ido ya bude yanzu daga shi har ita soyayya suke gwadawa juna da gaske. Furera an zama yan kallo don ta buga ta hakura saboda Qareeba da gaske tayi mata fintinkau. Ko kadan Bilya baya wulakanta ta amma ta zubar da damarta tun da dadewa.

Wata mata ce mai wankin bandaki ta shigo wata nurse ta daka mata tsawa cewa tun yaushe ake kiranta ta wanke bandakin bata zo ba.

Jiki na rawa tace " kiyi hakuri mara lafiya gareni a gida"

"Idan bazaki iya aikin bane sai na fadawa yallabai a nemi wata"

Hakuri matar take ta bayarwa har su Yaya suka sa baki. Ade ce ta kura mata ido can dai tace "kamar Hajiya Sakina maman abbati"

Da sauri ta dago "nice ina kika sanni?"

Ade ta rike baki...lallai duniya rawar 'yan mata ta gaba ta koma baya. Sakina matar Alhaji ita ce a haka.

"Ade ce tsohuwar mai muku wanke-wanke"

Sakina sai kuka harda rungumeta "Ade kece haka? Ikon Allah"

Waje suka fita inda ta fada mata a satin da ta koreta mijinta yayi mata saki uku wai ta sace masa kudi. Ashe daya daga cikin masu aikin da take yiwa rashin mutumci ce ta dauke. Tun daga lokacin duniya ta juya mata yau gata tana wankin bandaki a asibiti. Naira dubu biyu Ade ta bata tana jinjina lamarin Ubangiji.

Iyaye sun tafi dakin ya rage su Dahiru da matansu. Qareeba ta kalli Attahir tace "kanina Attashir ungo"

Hassanar mai dan karen kuka ta mika masa sannan ta mikawa Dahiru Hussainar tana kallon Bilya "Bilyana kasan burina akan yaran nan"

"Sai kin fada Qareebata"

Dariya aka soma yi tace "suna gama ko da JS 3 ne kowacce ga baban mijinta nan. Na yiwa 'ya'yana Ahmad da Abdul kamu"

Bilya ya riko hannunta "in sha Allahu zasu yi mana biyayya mu hada zumunci"

Dahiru yace "mungode Anti Qareeba"

"Ni ke da godiya Ahirin. Ina haifar namiji sunansa Dahiru"

Attahir ya saba Hassana a kafada tana kuka duk da babu yunwa da gani zata yi rigima. Sai jijjiga ta yake yana 'yar rawa.

Dahiru dariya har da dukawa yana tuna lokacin da Attahir yake cewa bazai hada jini da dangin dolaye ba. Ana bashi yarinya ya cafe sai juyi yake kamar ya manta ba su kadai bane a wurin. Kukan ne yaki karewa ya ce da Mawadda ta sauke Ahmad yazo ya rarrashi matarsa.

Akan abin sallah ya zauna ya dorata a cinya daya Ahmad na daya cinyar yasa hannu a kanta sai gata tayi shiru. Nawal ta daukesu hoto a waya tana dariya.

Mawadda tace dauko Abdul ta hadawa Dahiru suka zauna suka yi selfie su hudu.

Suna can suna hotuna Bilya ya kamo hannun Qareeba ya sumbata.

"Nagode matata"

Suma kowa kallon nasa iyalin yake yana godiya ga Allah.

~~~~~~~~

ALHAMDULILLAH

Ina mika godiyata ga Allah da Ya bani ikon rubuta wannan labari. Abinda na rubuta daidai Allah Yasa mu amfana dashi. Inda nayi kuskure kuma ina rokon Allah Ya yafe min.

~~~~~~
Godiya ta musamman ga 'yan uwana ahalin Fikra da kuma ku da bazan manta daku ba wato members na groups din *TASKAR FIKRA* hakika kunyi min *SOLIDARITY* shiyasa nake muku *SonSo*.

Kamar yadda kuka sani labarin *GUMIN HALAK* na sayarwa ne amma ina godiya ga duk wadanda suke bibiyar rubutuna ko a ina suke.

A karshe ina fatan Allah Ya sake hadamu da alkhairi a littafina na gaba _*KU DUBE MU*_.

Ina fatan zakuyi min solidarity ku saya domin shima na sayarwa ne in sha Allahu.

*Batul dinku ce mai Son So*
Chapter 68 · 0% Book details