← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 68

Sashe 65

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga shi har ita sai murmushi yayin da Furera ta shiga bude kwanuka neman fate. Tashi yayi ya fita ta bi bayanshi tana nunawa Mawadda ta karbe food flask din kada Furera ta cinye.

Attahir ma yace gara su tafi an hana su Dahiru cin abinci. Sallama suka yi musu zasu dawo anjima suka fita ya rage dakin saura Ummiyo, Furera da Mawadda.

Sai da Mawadda ta jira Furera ta dibi mai isarta tace da Dahiru zai ci ya bata fuska. Ko don tabawar da tayi ta bata wurin jage jage saboda keta yace baya so. Na Nawal ta sake zuba masa ta wanko hannu ta dawo ta haye gadon daga gefen kafarsa da take a nade a mike ta takwanshe kafafunta yana jingine da filo a zaune ta soma bashi.

Furera tana kallonsu har ta gama zaman wanda dama da uku ma tayi ba da biyu ba don ta tanka ta samu ta fada mata magana.

"Iskanci da rana tsaka Mawadda meye haka? Mutum yana fama da lalura don bakin naci da jaraba a nan din ma sai..."

"Anti Furera abinci zan bashi ba wani abu zamuyi ba fa"

Ummiyo ta soma dariya gashi dai taji kunyar zaman da suka yi. Bude baki yayi da hannu take bashi idanunsa a kanta suna yiwa juna murmushi.

Furera sai ta kasa hadiyar abinda yake bakinta don takaici. Da yanzu fa Hansa'u ce take kula da Dahiru yake nuna mata soyayya irin haka. Itama shegiyar yarinyar wai ta kalli tsabar idonta tace mata ta hakura da Dahirun. Tsaki ta ja bazata iya kallon wannan rainin wayon na Mawadda ba. Ta kalli Ummiyo.

"Ke! Tashi mu fita wannan abin da suke yi gaba zai kara don idan bakiyi wasa ba cinyarsa zata hau a gabanki"

Mawadda ta rufe ido "kai Antinmu ai ba lafiya gare shi ba yanzu" ta mayar da kallonta gareshi tana wani fari da ido yana biye mata da tambayar ko itama ya bata a baki.

Saura kiris Furera ta fashe ta tashi ta fice Ummiyo ta bi bayanta tana dariya. Haba mata duk basa sonta saboda yadda take wahalar musu da dan uwa.

Can bayan fitar Bilya da Qareeba wurin motarta suka je.

"Bilyamin me yasa baka ci faten ba? Ni nayi da kaina"

Wani benci ne a jikin bango suka zauna da tazara a tsakaninsu kafin ya amsa mata "ashe kin iya girki"

"Kala-kala kuwa"

"To amma kina ganin za'a bawa wannan makaniken mace kamar ki Qareeba ya rinka cin daddadan girkinki?"

"Kana tunanin guje min ne?" Ta fada tana kallon idanunsa. Duk abinta kasa jurewa tayi ta kawar da kanta.

Gyaran murya yayi ya nemi ta saurare shi da kyau "Qareeba ban mallaki komai da zai bani damar aurenki ba. Kinga jiya muka hadu zan so mu bi komai a sannu saboda kada nan gaba abin yazo bai yiwu ba"

Zuciyar Qareeba ta karye. Tasan me yake hange amma tayi rantsuwa idan har ya amince mata to bata miji sai shi.

"In hakura kenan?" Tace idanu na ciccikowa da kwala.

"Zaki iya zama dani da matar nan da ta cinye abincin da kika dafawa Ahirin?" Ya bata amsa da dariya.

Rike baki tayi kafin ta kwashe da dariya.
"Matarka ce don Allah"

Yayi murmushi "uwargidanki ba"

Qareeba abin ya bata mamaki yadda Furera ta shigo ta iya cin abinci bata zo da komai ba harda yiwa mijinta tayi. A take taji ta rainata. Ta rinka dariya yau ta ga wadda ta fita.

Fitowar Furera da Ummiyo ya katse mata hanzari. A fusace ta matso inda suke.

"Ka bani kudin mota na tafi. Wai don rashin mutumci a gabana yarinyar nan Mawadda take bawa Dahiru abinci a baki...a baki fa kamar wani karamin yaro. Shi kuma sai wani lumshe idanu yake kamar wanda ya sha wani abu"

Iska Bilya ya furzar ransa yana kuna ya mike zai bata amsa Qareeba ta riga shi don haushi matar take bata sosai.

"Mawadda da Ahirin ba miji da mata bane"

Ummiyo tace "kuma masoyan asali ba"

Furera ta daure fuska.
"To waye mara mijin?"

Qareeba ta kalli Bilya "Bilyamin...."

Zaro idanu Furera tayi "Bil me kika ce? Kai wai ma wace ce ke ne? Me kuke yi a nan?"

"Wadda tayi faten da kika shanye " Bilya ya ce.

"Anti Qareeba sunanta" Ummiyo ta bata amsa a takaice.

"Auuuu ita ce wadda Dahiru yayi aiki a gidansu ko? Shine kima zo duba shi harda girki? Sannu da kokari. Su Mawadda an manta da asalin miji sai wani fiffika take ita ta auri mai kudi"

Qareeba ta kalli Bilya don ta tattaro bakar magana zata bata amsa amma tana tsoron kada yaji haushi. Sai gashi ya bata mamaki.

"Qareeba ga uwargidana Furera. Furera ga Qareeba amaryarki in sha Allahu"

Su biyun kallonsa suke yi ya dake abinsa yana binsu da ido shima. Qareeba ta tabbatar yau Allah Ya kawo mata nata mijin. Furera sai da ta nutsu maganar ta sauka a kwanyar kanta kawai sai ta tura hannunta a makogaro tana kakarin amai. Kanta suka yi Bilya yana cewa meye haka. Ta dago idanu jazir da bala'i.

"Ni zaku kashe don kana son yin aure? Shine aka barbade faten aka bani nasha. To Allah Ya isana. Kuma kayi auren idan ka isa."

Ummiyo ta matsa gefe "Anti Furera babu wanda yayi kiki tayi kika dauka fa"

"Aikin asirin kenan Ummiyo. Abu a ajiye babu mai ci sai ni ina zuwa naji kamar yana cewa daukeni Furera...daukeni"

Da gaske tana ta kakaro amai abu ya gagara. Bilya ya kira Danlami yace yayi sauri ya dawo da motar idan ya kai matarsa gida shima zai tafi ne.

Ciki suka koma suka barta don ita tace kafin ta fara kishi dole ta fito da faten tsakin nan wanda ya sami wuri a cikinta ko gezau yaki fitowa.
*******

Wayar gaggawa aka yiwa Alh Sule tun dare daga ofishin Hisba sai gashi asubar fari yana idar da sallah ya kamo hanyar Kano hankali a tashe. Da kwatance ya isa ofishin nasu da aka kwatanta masa.

Haj Mara ta fita hayyacinta saboda tsabar tashin hankali. Yana isowa bayan an fito dasu ya daga hannu ya sharara mata mari sai da ta ga wani haske nan ya gilma.

Duk zafin bai dameta ba kamar wata muguwar tsanarta da take gani a idanunsa. Zubewa tayi a kasa jiki na rawa ta rike masa babbar riga.

"Alhaji kada kace kaima ka yarda da zargin da ake yi min."

Zuciyarsa har kuna take "Marakisiyya kin cuceni kuma a yau na kara nadamar aurenki. Sai dai nasan kaddara ce ta rayuwata. Na fada na kuma fada yaron nan kina cutar shi ne amma kin ki ji. Karshe ma kin koya masa tsanata da kin jin maganata a matsayin makiyinsa. Yau gashi dan cikina ake zargi da neman mahaifiyarsa"

BB da jikinsa ya gama tsami ya dago kai da kyar "Alhaji na zata Mawaddata ce fa. Mutanen nan sharri suka kula mana."

Shima Alh Sule ya sani Haj Mara bazata taba yin abinda ake zargi ba. To amma tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa ke duka. Cike ciken takardu yayi tare da 'yan sandan da aka kira suka zo suka daukesu bayan ta aminta da bakinta biyan kudi tayi aka fito mata dashi.

Wunin ranar sur ayi nan office din dasu su gama bayani a koma yi wani wurin dasu. Sai da aka gama komai aka kwashesu sai police station. Wannan karon harda Bobo anyi nasarar kamawa inda suka tarar da kofur Pascal a cell din shima yaci uban duka. Haj Mara kuma tana bangaren mata.

Sai da komai ya kammala da yamma aka kira Dahiru aka sanar dashi an kama su BB kuma an matso da shigarsu kotu nan da sati daya. Godiya yayi musu yace Allah Ya nuna mana lokacin.
******

Kwanan Dahiru uku aka sallame shi. A cikin kwanakin nan ya san shi cikakken dan gata ne don sosai Mawadda take bashi duk wata kulawar da ta dace. Shagwabarsa yake mata son rai tana biye masa.

Qareeba kullum sai taje asibitin inda ita da Bilya suka sake shakuwa kowa ya san da soyayyarsu mai ban mamaki.

Son juna suke yi da gaske ba wai don Dahiru yayi masa tayinta ba itama ba don ta dade da rashin aure ba. Cikin dan kankanin lokaci Bilya ya gama fahimtar wacece Qareeba. Mutane sun santa da dolanci da shagwaba ne kawai. Shi kuwa a yanzu ya santa a matsayin mutum wadda bata boye boye. Abinda tasan gaskiya ne to ko a gaban waye bata shakkar yinsa. Haka zalika shagwabar da dolancin shi burge shi suke yi sosai. A tata fahimtar kuma ta gane Bilya irin mutanen nan ne masu sadaukar da farincikinsu domin kyautatawa wasu. Yana da matukar kirki da saukin kai. Sai kuma to her advantage ta gane baya jindadin rayuwar aurensa. Bai fada ba amma a shekarunta da iya abinda ta gani game da Furera ta san cewa Bilya aure dai yana dashi amma soyayya irin ta ma'aurata ku nesanta da juna kuna begen juna bai sansu ba. Hirar soyayyar ma bai iyawa sosai sai kawai tayi amfani da wannan damar take nuna masa kulawa irin wadda bai saba gani ba. Hakan yasa nan da nan ta shige zuciyarsa. Balle yadda take yiwa 'yan uwansa.

Daren ranar da za'a sallami Dahiru ta kira Bilya. Yana zaune ya saka abinci a gabansa sai juyawa yake ya kasa kai ko loma daya saboda masifar Furera. Abincin ma Hansa'u ce tayi don ta dena girki babban dansa ya kawo masa.

"Ka dai ji kunya Yasin. Ka rasa wadda zaka nema sai matar da kaninka da kuka fito ciki daya ya gama wankewa rigar mama."

Bai iya fada ba wannan sai Dahiru. Shiyasa yaki kulata. Amma furucinta na karshe ya kona masa rai "idan dai ya taba wankewa to lallai Dahiru ya cika yaron kirki mai girmama na gaba. Tun a lokacin ashe yaji a jikinsa matar yayansa zata zama shiyasa yake wanke komai nata"

"Rigar mama fa nace ko baka ji da kyau bane"

A hankali saboda baya son daga murya yaransu suji yace "naji mana. Idan ta zo sai ni kuma na cigaba da wanke mata tunda 'yar hutu ce bata saba ba"
Chapter 65 · 0% Book details