← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 68

Sashe 66

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haushi ya kamata saboda so take suyi fada kuma yaki biye mata. Sai ta chanja taku "wa ya sani ma ko sai da suka gama watsewarsu aka yi maka tayin kwantai"

Hannu ya daga zai mareta sai ya kasa. Yadda taga idanunsa sunyi ja ba karamin tsoro ya bata ba. Amma ganin ya sauke hannun ta shiga tafi harda guda.

"Ahayyeeee nanaye...wato saboda zaka yi aure kake shirin dukana. Ga fili ga maidoki wallahi ka tabani ka tabo masifa ka tabo bala'i. " ta nuna shi da yatsa tana cigaba da cewa "banda kai ma dai lusari ne mara zuciya me zai kaika yin auren jari auren kwadayi"

Bata gama rufe baki ba ya falla mata marin da yake ta kokarin danne fushinsa kada yayi.

"Furera bana son zama cikin mazan da suke tauye iyalansu don suna neman aure amma ki sani idan ki ka kaini bango ranki ne kadai zai baci. Qareeba zata shigo gidan nan ba da dadewa ba in sha Allahu. Bazan ce ki kwantar da hankali ku zauna lafiya ba. Idan tazo ki cigaba da nuna mata haukanki itama zata nuna miki nata. Kuma ina mai tabbatar miki ke karamar alhaki ce a wurin Qareebata"

"Qareebarka? To ni kuma ta waye?" Tace a fusace.

"Ohooo"

Fita yayi abinsa bayan yasha turare yayi kyau sai gidan Dr Tani. Yau Dr Auwal ne ya bukaci ganinsa inda ya tabbatar masa ya bashi ita bayan yayi masa 'yan tambayoyi.

Gida yace zai bashi kyauta inda zai sakata yace ayi hakuri zai kama haya kafin ya gama ginin da yake yi a Zawaciki. Bai nemi Qareeba don ta zama jarinsa ba. Ya tabbatar samunsa na yanzu da yardar Allah zai ishe shi ya rike mata biyu.

Wani sabon girma da kima ya kara a idon su Dr Tani suka ce idan an gama da case din BB ya turo domin basa son a dauki lokaci mai tsaho.

Bayan sun shiga ciki ta fito da murnarta.

"Bilyana Mummy ta fada min an baka ni"

"Shiru ya kamata kiyi ni zan fada miki da kaina"

Bakinta ta rufe tana dariya. Can kuma tace "gaskiya ka bani wuya sosai"

"Da nayi me?"

Da muryar shagwabarta tace "Tun yaushe ka sanni ashe kaine mijin amma sai yanzu ka fito"

Dariya ta bashi "ko in koma ne?"

"Wasa nake yi don Allah"

Kayan abinci ta jere masa kamar tasan da yunwa yazo. Yana ci tana masa hira mai cike da ban dariya.

******

Washegari karfe bakwai a gida ta yiwa Mawadda. Ta gyara gidanta da ya soma hada kura saboda shigowar sanyi ko ina sai kamshi. Lafiyayyen girki tayi sannan ta shiga bandaki ta soma gyara da turara jiki tamkar amarya.

Shiryawa tayi cikin kananun kaya bisa shawarar Nawal. Wando ne mai laushi a hannu amma a ido kamar jeans blue ya kama jikinta. Rigarta fara mai dogon hannu da duwatsu a tsakiya itama ta kama ta. Kunyar kayan taji don bata taba shiga irin wannan ba sai yau. Navy blue din mayafi siriri ta samu tayi yafa a kanta da yasha gyara.

Tana gaban mudubi wurin biyu da rabi taji shigowar mota ta hau murmushi ita kadai. Dama duka kayan kwanan nasu ta taho dasu tun safe abin sallah guda daya ta bar masa da zata taho. Bakin kofa tazo ta tsaya amma bata bude ba tana jiyo takunsa har ya iso suna magana da Attahir yana kara yi masa godiya. Kofar taji ya kama tayi saurin bude masa haka kawai gabanta yake bugawa kamar ta dade bata ganshi ba. Ga kunyar kayan jikinta.

Labule ta daga masa tana tsaye daga gefe ya kura mata ido kamar yau ya fara ganinta. Idanunsa na kanta har ya isa kan kujera ya zauna ya ajiye sandunansa a gefe.

"Taho taho kada ki sani suman zaune" yace yana miko mata hannu.

A kunyace ta karasa kusa dashi ta zauna ya janyota barin jikinsa ya rungume. Yana ji ta saka hannuwanta ta zagaye shi itama tana kara makalewa jikinsa.

Shakar kamshinta yake mai ratsa zuciyarsa "I miss you Matar Dahiru"

"Awa ta nawa da baroka a asibiti?"

"Kenan bakiyi kewata ba ko"

"Maida wukar Mijin Mawadda"

Ya dago habarta "to kinyi?"

"Fiye da zatonka" tayi masa murmushi.

Tashi yayi ya sakala hannu a kafadarta ta kaishi daki. Duk wani motsinta akan idonsa yana binta da kallo. Jikinta kadai ya isa ya ruda mutum.

"Zaki yi min wankan"

"Nifa bana son shagwaba ka warke. Tun ciwon na sabo banyi maka ba sai yau saboda rigima"

Langabe kansa yayi "ni ko?"

"Rigimarka tayi yawa Yayanmu. A asibiti...."

"Can ma don kada kisa a kama mu ne na hakura"

Ita kam gaskiya tana jin kunyar wannan abu amma ya ta iya. Sai wani nanikarta yake ya kwanta akan cinyarta yana mita.

"Kwalliyata zata baci kafin ka gama gani" tace a sanyaye saboda rashin mafita.

"Zanyi miki kuka irin wanda sai Attahir ya hawo a guje"

Tashi tayi ba shiri ta hada masa ruwan sannan tazo ta ja hannunsa tana kumburi don ba haka taso ba. Wani fitinannen murmushin ya rinka yi mata tana shiga ya tura kofar da hannu. Da kayan jikinsu ya sakar musu shawa a ka suka jike. Kamar ta saka masa kuka

"Yayanmu!"

Zagayeta yayi da hannu yana dora kansa a kafadarta "kinga tsoron zamewa nake shiyasa na rikeki. Ai banyi laifi ba ko"

"Baka yi ba" tace don ta riga ta sallama tasan bata da wata mafita kuma. Da kanta ta matsa jikinsa tana hade bakinsu.
********

Kotu ta cika makil duk yawan fankoki zafi ake yi saboda jama'a. Dangin Mawadda, na Dahiru, Baba Prof, Dr Tani da kuma uwar gayya Haj Mara su ne daga gaba gaba.

Alkalin wannan karon mace ce wadda tayi fice a cikin Nigeria saboda rashin ramgwamenta akan duk wata shari'a da ta shafi fyade. Justice Raliya Habu kenan matar da kudi ko son zuciya har yanzu bai sa an taba kamata da laifin tauyewa wani hakki ba sai dai idan lauyoyin ne suka gaza. Gilashinta ta turi kan hanci ta bukaci lauyoyi su gabatar da kawunansu.

"Sunana Barrister Jibril Jibril nine lauyan masu kara"

"Barrister Wisdom Odili lauyan wadanda ake kara"

Justice Raliya ta basu damar fara gabatar da hujjoji da shaidu. Wannan karon shari'ar bata yi kama da zata bada wahala ba saboda yawan shaidu da suke a hannu. An shigo da BB ya rame ya kwanjale babu kyaun gani. Haj Mara tamkar wadda cutar tsotsewar jini ta kamata duk shekarunta sun fito karara babu kyaun gani.

Bisa aiki na kwarewa da JJ ya nuna yayi nasarar nemo likitan da ya duba Mawadda a asibitin Bebeji. Haka nan kuma ya samo Inspector Nalado wanda suka samo hotunan raunukanta tun na farko.

Dr Tani tazo ta fadi duk abinda tayi a wancan zaman shekarun baya sannan Qareeba da Dahiru suka bada shaida akan abinda ya sameta itama.

Zugar su Garwashi kaf sun nuna solidarity domin kuwa sun bada tasu shaidar har zuwa yadda suka taimaka aka gano Mawadda bayan sun saceta.

Barrister Wisdom dena yi musu tambayoyi yayi saboda babu amfanin yin hakan. Haka aka gabatar da Bobo shima ya tabbatar da kade Dahiru da suka yi wanda yazo da sanduna.

Jama'a cikin kotun sunyi tir da halin akuyanci irin na BB da uwarsa mai taya bera bari. Alkalin ta dage shari'ar zuwa kwana shida ranar da zasu dawo a yanke hukunci.

******

Yau kotun har tafi zaman farko cika saboda 'yan jarida har daga gwamnatin tarayya. Case ne babba da yake ciwa mutane tuwo a kwarya.

Bayan gama sauraron bayanai Justice Raliya Habu ta soma magana kamar haka.

"Duba da hujjoji da shaidun da lauyoyi suka gabatar wannan kotu mai alfarma ta yanke hukunci kamar haka."

Shiru kotun tayi baka jin ko da tari an baza kunnuwa.

"Kotu ta karbe lasisin aikin Dr Tani daga yau bazata sake aiki a matsayin likita a kasar nan ba saboda tayi amfani da damarta wurin bada shaidar karya da cutar da mai gaskiya."

Dr Tani sunkuyar da kanta tayi dama ta dade da zaton hakan.

"Hussaini Joji wanda aka fi sani da Bobo kotu ta yanke masa hukuncim shekara biyu saboda taimakawa wurin sace matar aure, fitar da mai laifi daga hannun yan sanda da kuma bada gudunmawa ta yunkurin kisa"

Gigicewa Bobo yayi don bai taba shiga hannun hukuma ba duk tsiyarsa.

"Haj Marakisiyya kotu ta ci ki tarar naira miliyan biyu da zaki bawa Mawadda Fatihu saboda danne mata hakki, bacin suna da taimakawa wurin cutar da ita. Har ila yau zakiyi zaman gidan yari na wata shida saboda fitar da mai laifi daga hannun hukuma"

Kukan ma tuni ta dena saboda dacin zuciya da bacin rai. Ta rasa komai ta rasa kowa saboda Babawo.

"Babawo Sule Chanji. Duba da irin laifukanka wannan kotu ta yanke maka daurin shekara ashirin da biyar tare da horo mai tsanani"

Murna da farinciki a wurin su Mawadda baa cewa komai. Dahiru ji yayi kamar ya taso yaje ya rungumeta don kukan farinciki take yi.

Garwashi da yaransa Alkali tayi musu gargadi akan daba ta kuma basu shawarar su nemi sana'ar da zata rikesu bata fatan sake ganinsu a kotunta indai ba alkhairi bane ya kawosu.

BB yana ta hargagin sai ya kashe Dahiru ya auri Mawadda aka fitar dashi sannan aka sallami kotun bayan Alkali ta tashi.
[31/01 9:36 am] Batuul Mamman: *GUMIN HALAK...*💰27

*Batul Mamman*💖

Daga kotun gidan Mal Fatihu suka wuce gabadayansu. Dr Tani kafin su tafi da nata iyalin ta rike hannun Mawadda ta sake rokonta gafara. Babu bata lokaci tace ta yafe.

Garwashi yazo tare da yaransa. Loba boy dai yaji dadi an kulle Danmani shima ya sami rabon wata shida. Dahiru da Attahir suka jasu gefe suka basu sati daya kowa yayi shawarar me zaiyi amma kafin nan duk su koma gaban iyayensu su nemi gafararsu. Da farinciki suka tafi bayan Mawadda da kowa ya sake yi musu godiya.

Suna isa gidan abincin sadaka da aka dafa tun safe aka shigar fitarwa lodi lodi ana kaiwa asibitoci domin godiya ga Allah. Gidan ya cika da hayaniya tamkar ana biki. Dahiru ya turawa Mawadda text don yaji shiru ko nemansa bata yi.

_(yau fa akwai celebration kiyi ki gama mu tafi da wuri)_
Chapter 66 · 0% Book details