← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 68

Sashe 14

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai ta gyada kawai zuciyarta tana kuna. Tasha tambayoyi sosai sannan tace ta sauko. Yaya ta kalla tace ta kirawo Baban yarinyar.

Da sauri ya suri silifas dinsa ya bi bayanta suka sami wuri suka zauna ita kuma Mawadda tana tsaye.

"Bawan Allah garin yaya kuka yi sake 'yarku ta sami kanta a wannan yanayin?"

Gajeren bayani yayi mata tace "a gaskiya lalurar yarinyar nan ba kasafai take faruwa ba idan anyi fyade. Amma kuma ana samu a daidaikun lokuta. Yawanci tsabar tashin hankali ke zaburar da mace idan haka ta sameta motsi kadan sai ya firgita ta har ta kasa rike fitsarin. Yanzu zan rubuta mata gwaje-gwaje da nake so ku samu kuyi zuwa gobe in sha Allah. Sai na ga sakamako zan san wane irin mataki ya kamata na dauka"

Baba ya rinka mata godiya tamkar ance Mawadda ta warke ta gama. Ta dakatar dashi.

"Zan bata gado saboda ciwon nan yana bukatar kulawa kada ya zame mata wani abu a gaba. Dadin dadawa ina bukatar sanya mata ido domin na gano wasu abubuwa da zasu taimaka wurin magance wannan matsalar ta fitsari."

Su Baba to kawai suke cewa ta kirawo wata ma'aikaciyarsu ta wakilta taje a bawa Mawadda gado a bangaren mata. Sannan a tabbatar anyi gwajin da ta rubuta a yau.

Cikin dan lokaci kadan an basu gadon a dakin can gefen taga. Kafin likitan ta iso haka taje ta yayyafawa jikinta ruwa tayi sallah saboda wucewar lokaci ga rashin kayan canjawa. Ganin haka Yaya ta karbi kudi a wurin Baba ta koma gidan Barira. Ta dauko musu kaya da zannuwa da kuma abin rufa da tabarma. Barira ta hada musu abinci suka koma tare.
******

Shirye shiryen fara karatu ya kankama a wurin Dahiru. Ya kira su Baffa ya fada musu aikin da ya samu duk sunyi murna. A nan kuma yake jin tahowar su Mawadda Kano. Duk da su ma su Baffan basu san me kuma yasa suka chanja asibiti ba amma ansan ba lafiya ne.

"Kana nan akan bakanka na aurenta har yanzu?" Baffa ya tambayeshi.

"In sha Allahu. Yanzu haka ma ina jiran Yayanmu Bilya ya dawo zamu fara duba gidajen haya"

"Dahiru ina jiye maka ga karatu, ga aiki sannan ka hada da aure. Auren ma irin wannan ba na dadin rai ba. Kada garin neman suna komai ya baci fa"

Murmushi yayi kamar Baffan na kallonsa "Baffa addua kawai zaku tayani da ita saboda ni dai don Allah nake son aurenta ba komai ba."

Bai kara cewa komai ba ya kashe wayar. Yasan yanzu kowa zaiyi kokarin cusa masa ra'ayin rabuwa da Mawadda. Sai dai ya shirya toshe kunnuwansa indai iyayensa suka saka masa albarka. Bai taba son wani yadda yake sonta ba. A halin yanzu yana ji a ransa tausayinta har yafi son da yake mata yawa. Bazai taba iya barinta ba saboda yanzu ne ma take bukatar kulawa da dukkan wani gata da shi ko wasu masu sonta zasu nuna mata.

Da yamma suka fita neman gida don yafi son ya samu da wuri.
******

Ranar lahadi washegarin da aka kwantar da Mawadda su Ade suka taho. Kafin isowarsu an kaita wurin gwaji inda aka debi fitsarinta da jini. Tun daga nan Baba ya fara sarewa da lamarin asibiti saboda kudin da yaji zai biya na wannan kawai. A haka ma wai don asibitin na gwamnati ne.

Da suka dawo ta samu dan bacci har su Ade suka iso bata sani ba. Sunyi sa'a karshen sati dama da wuri ake barin 'yan dubiya su shiga.

Tana cikin bacci ruwan hannunta ya kare Nos namiji ne a kusa aka kira shi yazo zai cire mata. Bude idon da zata yi ta ga namiji a kanta ta kwala ihu iyakar karfinta ta tashi a firgice.

"BB ka rufa min asiri kada ka cutar dani. Wayyo Allah Babana ka taimakeni"

A rude take gabadaya tana ta sambatu. Baba yana waje da kaninsa sai su Ade da Iya don Yaya ma ta tafi gidan Barira karo zannuwan da Mawadda zata rinka chanjawa.

Da kyar suka iya kamata idanunta akan Nos din tana kuka.
"Ade kada ku bari ya tabani wallahi akwai ciwo"

"Babu me tabaki kinji ki kwantar da hankalinki" ta amsa mata

"To kice ya fita"

Iya ta kalle shi da alamun roko. Shi tausayi ma yarinyar ta bashi ya fita sai Nos mace ce tazo ta cire mata allurar don ta goce.

Wani baccin ne ya soma fizgarta ta kwanta a jikin Iya.

"Allah dai ya kwashewa wannan tsinannan yaro albarka. Dubi yadda yasa ta tarawa kanta 'yan kallo saboda yadda ta firgita. Allah Ya kaimu a sallameta ko zan sayar da gonata ta gado sai mun shiga kotu da yaron nan"

"Kayya dai Iya da kin bar maganar nan. Dame zamu tunkari shari'a da wadanda suka fimu. Sannan daga lokacin kowa zai san sirrinta duk inda ta zaga a nuna ta"

Wani tsaki Iya tayi mai kara sosai "amma kin bani mamaki. Wane sirri ne ya rage mata bayan a garin namu babu wanda bashi da labari yanzu. Kuma da kike batun za'a nunata an dade ba'a nuna ta ba. Iyaka ace ga wadda aka taba yiwa fyade ba wadda taje yawon ta zubar ba ko. Kai! Ni kam kuna bani mamaki abu mai girma kamar wannan ya faru ayi ta kubi-kubi dashi wai kada ya fito duniya ta sani"

"Yanzu Iya ba kya jin yadda rayuwar mata irinta take tagayyara?"

"Me zai hana ta tagayyara kuwa iyaye sai su rufe magana abar yarinya ita kadai tana fama da bakinciki. Yanzu da tayi shiru bamu sani ba haka zata rinka zabura muna banka mata hayaki ace mutanen boye ne. Kinga idan baza kiyi komai a kai ba ni ki barni. A ganina shirun da akeyi da rashin daukar mataki shine yake bada damar gobe ma a sake. Sannan yana daga abinda yake sa matan su ga kamar sune masu laifi ba matsiyatan da suka cutar dasu ba"

Shiru Ade tayi don ko kadan bata maraba da a kai maganar kotu a yiwa Mawadda tonon silili.

Sake kallon Iya tayi tana ta fada ta jinjina kai. Wannan karfin hali nata ga talauci ga rashin wayewa amma baya dakusar da ita akan niyyarta.

Suna nan zaune sai ga Baba ya shigo da Dahiru da Bilya. Ade na hango su ta dubi Iya.

"Don Allah kada ki ce musu komai"

Iya tayi guntun tsaki "ku kuka sani, mutane sunyi sanadiyar tona sirrin da kuke ta boyewa ya fito har akwai wani abu na mutuntawa tsakaninku kuma"

Da suka karaso sun gaisa dasu tare da tambayar mai jiki.

Ade zata amsa Iya tayi saurin katseta "jiki da saukin musulunci gata tana bacci. Raunukan zahiri dai suna ta warkewa amma kwarewa a tsegumi yasa an dasa mata wani tabon a kahon zuci. Uhmm ko da wane idon jama'ar gari zasu rinka kallon jikata kuma Allahu Ya'alamu"

Duka su biyun kai suka sunkuyar a kunyace don sun san dasu Iya take. Bilya ne ma ya iya bada hakuri sannan ya kara da cewa "muna nan muna neman gidan da zasu zauna ba a kauyen zai ajiyeta ba"

Tsananin farinciki a take ya kama Iya ta kalli Bilya ta koma tana kallon Dahiru.

"Kai yaro rantse, kace Allah Dahiru zai aureta"

Ledar lemo da ayaban da suka zo da ita Dahiru ya ajiye ya fice ganin su Baba duka shi suke kallo. Bayan fitarsa Bilya ya fada musu halin da ake ciki na dangane da samun gurbin karatu da aiki da zaiyi.

"Nifa shiyasa tun ranar da aka gabatar min dashi nace in anyi duniya dan Manzo Mawadda bata da miji bayan Dahiru. Zuri'ar gidanku ba daga nan ba ni shaida ce ra'ayil aini. Aure a wannan yanayin wallahi sai dan kwarai da ya haifu cikin uwa da uba."

Ade dai kasa cewa komai tayi Iya ta saka ta jin matsananciyar kunya. Amma anya iyayensu Dahiru sun sani kuwa? Shi kuwa Baba fita yayi yabi bayan Dahirun. A can gefe ya hango shi zaune. Ganin Baban yasa ya taso da sauri.

Kaunarsa ta sake shigar Baba ya yi masa murmushi "Dahiru nasan kai yaron kirki ne kuma ko gobe ka nuna kana son wata cikin kannen Mawadda zan baka. Amma ka hakura da ita, tata kaddarar kenan hakuri da aure"

Yana jin kunyar Baba gaskiya amma baya jindadin yadda kowa yake ganin rabuwa da ita shine alkhairi garesu.

"Baba don Allah ku sa mana albarka kawai. Na fadawa su Baffa kuma sun amince"

"Bazan so kaina ba Dahiru. Ko a yanzu ma mungode sosai da kulawa. Amma ka dauketa a matsayin kanwarka kawai. Idan ma saboda magana ta fito ne duka babu komai ko me za'ace za'a gaji a bari"

Magiya sosai Dahiru ya soma yi har ya bawa Baba tausayi. Amma don ya kara nuna masa illar auren duk kuwa da cewa ransa yana so ya sanar dashi dalilin zuwansu asibiti.

Dan nazari Dahiru ya soma har Baba yaji jikinsa ya kuma yi sanyi kada ya fasa da gasken sai kuma yaji yace "Baba haka zamuyi ta hakuri har ta sami lafiya amma aure in sha Allah ba za'a daga ba."

Kwalla ce ta taru a idon Baba. Ya sani wannan ba karamin abu bane. Ko dansa ne haka ta faru da wadda zai aura da wuya fa ya amince. Baya jin zai taba mantawa dashi ko auren bai yiwu ba yasan ya so 'yarsa kuma yaso rufa masa asiri.

"Nagode amma ka jira zamuyi magana da shi Mal Isiyaku kaji."

Bilya ne ya leko yace Mawadda ta tashi suka nufi hanyar dakin Dahiru yana rokon Baba akan su taimaka kada a fadawa iyayensa lalurar da ta kamu da ita yanzu. Baba ya ji shi ne kawai amma fada ya zama dole musamman yadda ya kara yarda da wuya ake boye abu a duniya. Bazai so a zargesu ba a gaba.

Tun shigowar Nos dinnan namiji har yanzu da Mawadda ta farka hankalinta bai gama kwanciya ba. Shiyasa su Dahiru basu wani dade ba suka tafi. Iya kuwa ta rinka mata fada akan ya kamata ta soma sakin jikinta da mutane.

Da yamma Dr. Tani ta shigo ta sake dubata. Sakamakon gwajin ta fadawa su Baba
Chapter 14 · 0% Book details