← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 68

Sashe 28

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su Mawadda ana ta shirin kai amarya suyi nan suyi can. Ba ita ba ba Rafi'a ba kowacce tayi kyau sosai. Jikinsu ya saba da gyara kowa na sha'awarsu.

Dahiru na zuwa ya tarar da motocin daukar amarya sai kawai ya shiga cikinsu yayi parking a karshe. Motarsa tafi ta kowa kyau da haduwa a wurin mata suka fara kokarin shiga. Lock ya saka kawai yana ta murmushi shi kadai ko a yaya zasu hadu da Mawadda.

Wata mai tsaurin ido cikin 'yan matan amarya ce taje ta fadawa Mawadda wani abokin ango yaki bude motarsa. Mayafi ta dora kan riga da skirt din jikinta ta ce bari ta duba idan angon yace wadda za'a saka amaryar a ciki baka ce kila mutumin amarya yake jira.

Yarinyar ta fada mata ruwan goro ce mai masifar kyau.

"Bari naje na gani idan bai daukeku ba da motarsa mai masifar kyau ko iyaye ya taimaka ya diba" ta fada tana murmushi tayi waje.
[08/01 8:32 pm] : *GUMIN HALAK...*💰12

*Batul Mamman*💖

Tana fitowa wata yarinya ta kwala mata kira "Anti Mawadda mai waccan motar yace a fada muku a tasa za'a dauki amarya"

Kallon motar tayi ta ga baka ce kamar yadda angon ya fada mata. Kamar ta juya sai ta hango motar da aka kai karar mai ita ga mata da yawa da basu sami tafiya ba kuma dangin ango suna ciki kowane lokaci zasu iya fitowa a tafi. Yanke shawarar rokarsa tayi don duk tunaninta cikin tawagar angon yake.

Sannu a hankali take takawa da takalminta mai tsini tayi kyau sosai.

Tun da ta doso motar Dahiru ya nemi nutsuwarsa ya rasa. Zuciyarsa kamar ta fito saboda halin da ya shiga na ganin macen da har yau bai taba son wata kwatankwacin yadda yake sonta ba. Matar da tunaninta bai taba barinsa ba tsahon shekara takwas da basa tare. Idonsa yaji yana masa zafi alamun taruwar kwalla ya shiga mika godiya ga Allah da rayuwar Mawadda bata tagayyara ba kamar yadda yayi ta jin tsoro. Kashe motar yayi ya kifa kansa akan sitiyari yana kokarin daidaita tunani da nutsuwarsa don a yadda yake ji a lokacin cikar kwanciyar hankalinsa shine ya rungumeta.

Ita kuma tana karasowa taji motar a kashe kuma da yake glass din tint ne bata iya ganinsa. Tagar mazaunin dreba ta matso sosai ta dan duka kafin ta girgiza kai tana murmushi a ranta tace ashe ma babu kowa shiyasa ba'a bude ba. Dahiru yana zaune yana kare mata kallo shi kadai yana murmushi ganin ta sake dukawa tana kallonsa wanda a zahiri fuskarta take kallo ta gilas din.

Sassanyan murmushi tayi kamar tasan ya shagala da kallonta ta gama turo bakinta da ya sha pink din janbaki kamar wadda zata dauki hoto sannan ta mike ta barshi da dariya a hankali. Juyawarta kenan zata koma yayi saurin budewa ya fito kada ta tafi baiyi mata magana ba.

Tsayawa tayi cak tana tunanin me motar nan ya gama da ita. Yanzu da ta dauko soson powder ta sake gogawa a fuskarta kamar yadda tayi niyya ai ya cuceta. Irin haka tunda ya iya yin shiru da farko ai da ya hakura gabadaya sai ta tafi ya fito.

Shiru ya wuce na wasu 'yan dakiku ita taki juyawa saboda yadda jikinta ya bata kallon ta ake yi shi kuma tsabar farinciki ya rasa me zaiyi. Daga kafa tayi zata yi tafiyarta kamar daga sama taji an ambaci sunan da mutum daya ke kiranta da wata murya daga can kasan makoshi har sai da tsigar jikinta ta tashi.

"Mawaddatan wa Rahma"

Mutuwar tsaye tayi jikinta ya soma rawa. Dahiru ya tako a hankali ya zagayo gabanta ya tsaya.

Anya zuciyarta za ta gaskata abinda idanunta suke gani kuwa. A hankali kamar mai tsoron kada ace karya ne abinda ke gabanta tace

"Yayanmu?....Yayanmu ne?? Yayanmu Dahiru???"

Kamar shi amma wannan yafi wancan komai sai dai bata jin akwai canjin da zaisa ta kasa gane fuskarsa duk kuwa da ya boyeta cikin kyakkyawan sagensa.

"Ashe dai zaki gane ni" ta sake jin muryarsa a karo na biyu.

Mamaki da farinciki ne suka lullubeta a lokaci guda. Ta bude baki tayi masa magana amma ko harafi daya ta kasa hadawa. Dahiru kuwa ganinta ya sauke masa duk wata sauran damuwar dake ransa.

Tabata taji anyi ta baya ta juya a firgice sai ta ga 'yar yayarta Bilki.
"Anti Iya tace kizo ki fitar da Anti Rafi'a ko tayi mata duka wai suna ta kuka ita da Ade da Yaya sun hanata fitowa ga mutane na jira"

Sauran yayyen nasu duk suna gidan amarya ana karasa gyare gyaren da ba a rasa ba. Ita kadai ta rage sai su Iya da Innar Fatihu.

Yarinyar ta kama hannunta tana ja Dahiru yayi mata alama da hannu akan ta tafi.

Tamkar wadda iska zata dauka haka take jin jikinta ta soma tafiya kawai taji yace

"Kinyi aure?"

Ko da ta juyo ita yake kallo suka hada ido karo na farko bayan shekarun da suka yi basu hadu ba. Kai kawai ta iya girgizawa saboda ta kasa magana sai idanunta da ta kautar daga nasa.

"Alhamdulillah, amma kina da saurayi?"

Samari kai, ita manema aurenta yawa garesu amma tafi kowa sanin dalilin da ya hanata bawa kowa cikinsu dama. Dr Imran ne ya fado mata a rai sai ta gyada kai.

Yanayin fuskar Dahiru bai sauya ba duk da haka ya sake cewa "Iyaye sun shiga maganar?"

Wannan karon sai da ta murmusa kafin ta kuma girgiza kai.

"Wai, Allah Ya soni ina da sauran dama"

Wayarsa mai kyau da tsada ya miko mata ko bai fada ba tasan me yake nufi. Numbarta ta saka ta mika masa.

Tsayuwar wurin tayi mata wuya kuma tasan ana jiranta sai kawai ta kuma juyawa a karo na uku ya sake dakatar da ita ta hanyar cewa

"Mawaddatan wa Rahma...naji dadin sake ganinki. Sai na kira mu gaisa"

Sai lokacin ta tuna ko gaisawa basuyi ba. Tana juyawa ya shige mota ya dago mata hannu. Bata bar wurin ba sai da ya fita daga layin ta sauke ajiyar zuciya.

Har suka shiga mota a hanyarsu ta zuwa gidan amarya bata dawo daidai ba. Lokaci lokaci take sakin murmushi ko tayi ajiyar zuciya.

*****

Gidan Bilya ya wuce kana ganinsa zaka yi tunanin anyi masa albishir da kujerar Makka ne. Furaira matar Bilya ya gaisar ta dauke kai.

Yayi dariya don yasan dalilin fushin "matar Yaya kinsan babban wa uba ne matarsa kinga ta zama uwa. Fushin me kike yi dani kuma yau"

Ta kula wani nishadi ma yake yi tayi kwafa "nagode da wulakanci Dahiru. Wai kai kayi kudi kana nuna min iyakata"

"Assha me kuma ya kawo wannan maganar don Allah" ya fada murmushi na bayyana a fuskarsa mai nuni da rashin damuwa da fushin nata.

Hakan ya kara kular da ita "ba laifinka bane, laifina Hansa'u ne da ta dage sai kai. Tukwicin da ka ga ya dace ka bani kenan duk wahalar da muka yi da kai lokacin karatunka ka guji kanwata ko"

Hakuri ya bata don wannan rigimar kullum ya shigo sai anyi. Saboda shi kanwarta gidan ma ta dawo amma idan ka cire gaisuwa baya yarda wata hira ta hadasu. Ya tabbatar baya sonta bai ga dalilin sanya mata burin karya ba.

Tare da yayansa suka yi sallar magariba sannan yaci abinci ya tafi gida.

A daren yayi ta kiran Mawadda wayarta chaji ya kare kuma da ta dawo gida ta nemi chaja ta rasa. Haka nan taji babu dadi don tana tunanin da wuya idan Dahiru bazai nemeta ba. Yadda ta damu da rashin chajin har Ade sai da tayi magana tace ko akwai kiran wanda take jira ne. Wannan maganar ce tasa ta jin kunya ta hakura ganin an soma yi mata dan biki.
*****

Washegari ta kama lahadi Dahiru bazai je office ba. Baba Prof ne ya gayyace shi rakiyar daurin aure suna dawowa yace masa lallai ya wuce gidan Dr Auwal yau su gaisa da mutan gidan.

Bazai taba iya ketare maganar Prof ba shiyasa bayan ya kaishi gida ya tsaya. Horn yayi maigadi ya bude suka gaisa ya fada masa yazo wurin masu gidan ne. Maigadi ya ga babban mutum irin wannan ba wata-wata ya bude masa.

Shigarsa ke da wuya wata motar ta shigo. Matsawa yayi wurin mutumin da ya fito daga ciki ya mika masa hannu suka gaisa.

"Kamar nasan fuskar nan"

Dahiru yace "Safwan ko? Dahiru ne mai wanki da shara"

Idanu Safwan ya ware ya shiga zagaye Dahiru sannan ya saki ihu "Ahirin kaine? Tabdi, muje ciki"

Sun shiga korido da zai sada su da kofar falon Safwan ya rike masa hannu yana ta zuba surutu Dahiru ya tsaya daga bakin kofar.

"Ya haka muje mana"

"Ka shiga ka fara sanar dasu. Bai dace na shigo kai tsaye ba"

Safwan yace hakane ya shige da sauri yana ta mamakin ganinsa.

Dr. Tani tana yanke farce da nailcutter ya shigo ya zauna a gefenta.
"Mummyna..."

Dadin ganin autanta tayi yayi fes dashi ga uwar kiba yana ta hadawa.

"Ka ci abinci kuwa?" Ta tambaya don tasan matarsa da kyuyar girki ita kuma bata yarda danta ya wahala ba.

Kamar wani wawa irin maganar shagwababbu yace "Kai Mummy kema kinsan naci. Tun ranar da ki ka fada mata idan bata soya min chips da kwai yadda nake so zaki sa nayi mata kishiya ta canza. Yau ma shi tayi min da safe"

Dahiru yana jinsu ya girgigiza kai "ana jika har yanzu"

Kamar Safwan ya jiyo shi ya buga tsalle ya mike "Mummy albishirinki"

Murmushi tayi a zatonta ko jika zata samu "goro fari kal"

"Tare muke da Dahiru. Dahiru mai shara da wanki!"

Wani uban tsaki ta ja har zuciyar Dahiru.

"Me kuma ya kawo shi? Shi kadai ne ko an rakito iyali daga kauye a fake da zuwa gaishemu nan kuwa yawon maula ne"

Safwan ya kece da dariya "Hmmm baki ganshi bane tare muke yana bakin kofa bari na shigo dashi"
Chapter 28 · 0% Book details