← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 68

Sashe 59

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Laushi ne dashi baka ji ba kamar auduga"

Dauko shi tayi daga kasan ta mika masa wai ya taba yaji laushin. Yana karba ya cilla shi wurin kofa.

"Indai laushi kike nema to kisha kuruminki na fishi. Yau don Allah in meye gurbinsa kinji"

"Kai bread ne?"

Tana fada ya taso yayi kanta tana dariya zata gudu ya janyota kan gadon ya danneta "nine bread din?"

Dariya take sosai "wasa nake yi Yayanmu"

"Sai fa kin dauki bread dinnan yau" yace yana sakar mata nauyinsa.

Nishi ta soma "wayyo Babana mijin Mawadda zai ballani, tsokanar da kake min zan rama amma na fasa kayi min rai tuba nake"

Kadan ya dagata amma yadda bazata iya tashi ba.

"Waye ni?"

"Mijin Mawadda mana"

"Ba kaninki ba ko yayanki ba?"

Sake sakin nauyinsa yayi tace "inaa da kenan, yanzu ka hada duka harda aboki da miji"

"To me zaki bani?" Ya kuma danneta.

"Me kake so? Wayyo kirjina Yayanmu nauyi gareka fa"

Dagata yayi suka tsaya ya nuna filon "kishiyan can nawa zaki dauke yau daya dai a barni na kwanta kusa da amaryata"

"Washhh, naji kuma dole na amince kafin ka rabani biyu"

Hancinta yaja yana tsokanarta reshe ya juye da mujiya. Tazo tsokanarsa abin ya koma kanta. Fada masa tayi ta gama girki da komai gara suyi wanka kada su Attahir su jirasu.

Wata atampa ta nuna masa a kayanta ya girgiza kai ta cigaba da nunawa yana cewa basuyi ba. Sai da ta nuna wani lace mara nauyi ruwan toka da digon ja yace shi zata saka.

Fita yayi ya bata wuri ta shiga wanka shi kuma ya kira lauyansu suna tattaunawa akan case din. Ya sanar dashi yadda suka yi da su Qareeba ta fada masa duka wani abu da ya bukata. Dr Tani da Maigadinsu zasu bada shaida tare dashi kansa Dahirun.

"Yanzu statement din matarka nake bukata duk da na samu wasu bayanai a police station din"

"Idan babu damuwa sai mu hadu ranar litinin in sha Allahu sai kayi mata tambayoyin. Mungode sosai"

"Aikina ne Dahiru. Allah Ya bamu nasara"
******

Daya saura gidajen biyu sun gama shiri. Dahiru da Attahir suna tsaye jikin motocinsu suna hira da tsokanar juna. Kusan minti biyar babu wanda matarsa ta fito.

"Wato da gaske dai idan za'a fita da mata sai anyi jira" cewar Dahiru

"Ga alama ka gani kamar sun hada baki. Shikenan muma mun girma. Yadda manya suke mitar jiran matansu yau abin yazo kanmu"

Dahiru ya soma dariya "sai yanzu ka girma ashe?"

"Ana shafa Fatiha nace to girma salamu alaikum"

Tafawa suka yi suna yiwa juna shakiyanci aka turo karamar kofar gate din da suke bari a sakaye.

Hayaniyar yara suka fara ji kafin Furere ta sako kafa tana cewa su shigo. Su biyar ne yaran harda ita da Hansa'u mutum bakwai.

Dahiru na ganinta ya hade girar sama da kasa. Dazu da safe lokacin da Mawadda take aiki a kitchen wayarta ce ta tashe shi ta sanar dashi zasu zo yini ita da yara. Tun a lokacin ya fada mata fita zasu yi kuma dama har gidan zasu je domin a basu girmansu na yayyensa. Tana jin haka ta tambayeshi yaushe zasu tafi yace suna yin azahar. Wato shine ta tare shi don kawai ta bata masa rai.

Har suka shigo ya kasa sakin fuska sai da Attahir ya tabo shi "meye haka ne Dahiru?"

Saurin gyara fuskarsa yayi "babu komai zamu dan bata muku lokaci matar Yayanmu Bilya ce"

"Na gane ta"

"Dan bani minti goma su gaisa da Mawadda sai mu tafi"

"Haba Dahiru don Allah kuyi zamanku gobe ko wata ranar sai kuje."

Karasowa suka yi Hansa'u tana tafiya kamar ta karye saboda kwarkwasa.

"Ango kasha kamshi kace gara da muka zo yau din tunda fitar bata yiwu ba"

Attahir ne ya masa kallon yayi shiru ya daure yace tazo su hau saman.

Yana bude kofar Mawadda tana yafa mayafi ta rike kunnuwanta "sorry"

Kallon mutanen da suke shigowa tare dashi tayi ta saki fuska duk da bata sansu ba ta ajiye mayafin a hannun kujera.

"Baki muka yi haka? Sannunku da zuwa"

Wurin kofar taje da fara'arta tana cewa su shigo su zauna.

Hansa'u ta tsura mata idanu kamar ta cinyeta har sai da ta tsargu.
"Ba baki bane. Matar yayansa ce da 'yaranta ni kuma kanwarta ce"

Murmushi Mawadda tayi "Allah Sarki ku zazzauna mana bari na kawo muku lemo yau akwai rana"

Anti Furere ta hakimce akan kujera "Allah Yasa da sanyi dai"

Mawadda bata tanka ba ta wuce kitchen. Hansa'u da Anti Furera suka bita da na mujiya. Riga da zani ne a jikinta na lace da gani yana da tsada. Rigar tayi mata kyau sosai ta fiddo da surarta wadda take tafiya da Dahiru duk sanda ya kalleta. BB kansa wannan jikin ne ya fara kwadaita masa ita. Bata fiye tsayi ba don bata cikin layin dogaye ma amma surar jiki da kyaun fuskarta suna daukar hankalin mutane da dama.

Tana tafiya Dahiru yace "Anti ba na fada miki zamu zo ba?"

"Dahiru korata zakayi daga gidanka? Ikon Allah sai kallo. Yau kayi arziki kayi aure dole ka wulakantani"

Kallo ya bita dashi na takaici bai iya bata amsa ba ga yara a wurin. Mawadda ta fito musu da lemuka masu sanyi da ruwa. Sai cake da snacks din da Nawal ta miko mata. Itama tuwon da tayi haka ta dibar musu ta bata idan sun dawo babu mai yin girki.

Zama tayi ta sake gaishe da Anti Furera ta dauko kofuna zata tsiyaya musu lemon.

"Da kin bari kowa ya dauki roba daya zasu iya shanyewa"

Tayi murmushi "to shikenan"

Hansa'u ta dauki remote ta kunna TV ta shiga canja tashoshi. Rai a bace Dahiru ya tashi ya koma daki. Duk wannan.abin yasan ana yi ne kawai don yayi magana. Rigarsa ya cire yayi jifa da ita daga shi sai dogon wando da singeleti ya kwanta ya soma kiran Mawadda.

Tana zaune a kasan kafet suna ta hayaniya su da yaran babu mai kula ta taji yace "Babyna"

Yadda suka tsura mata ido da mamaki itama shi din ne ya kamata.

Hansa'u jiki yayi mugun sanyi kamar tayi kuka dama tana ganin Mawadda ta raina kwalliyar da tayi.

Anti Furere ta soma fada "wane irin abu ne wannan nazo da yara za'a bata musu tarbiya."

Da sanyin jiki ta tashi ta tafi. A kwance yake ya daga hannu yana mata alamar ta taho ta bata rai "Yayanmu so kake ka bani kunya?"

Sai da ya taso ya rike hannunta ta zauna akan gadon sannan ya kwanta ya dora kansa a cinyarta abin yazo mata wani iri.

Dago kai yayi yana kallon fuskarta "kiyi hakuri to. Anti Fureran ce sai da haka."

"Saboda me?"

"Kiyi dai hakuri nasan zasuyi ya yin abubuwa don kiji haushi. Da biyu ne Hansa'u taso na aura"

Kallon idanunta yayi da suka nuna zallar kishi ya kuwa kankameta sosai ta hanyar zagaye kugunta ya cusa kansa wurin cikinta.

"Kada ki damu ke kadai nake so Mawaddatan wa Rahma. Na fada miki ne don kada ranki ya baci ko me zasu yi"

A hankali tace "to sakeni na koma kafin nayi laifin barinsu su kadai"

"Uhmm uhmm" yace yana kara matseta "ni mu zauna a haka"

"Don Allah"

"Kiss me"

Jikinta taji ya soma rawa tsabar kaduwa da kunya ta shiga ture shi "ba zaki tashi ba fa sai kinyi yadda nake so"

Cije lebenta tayi ya janyo kanta daidai fuskarsa ya shafa leben "wannan abin yana burgeni sosai" ya karashe da kissing dinta.

Kamar daga kofar dakin suka ji ana cewa "Kawu Dahiru Umma tana kiranka"

Firgigit suka tashi daga shi har Mawaddan yace "kin gani ko"

"Ba laifinsu bane kaine ka janyoni"

Doguwar riga yasa suka fita tare.

"Don munzo gidanka shine zaka mana wulakanci Dahiru?"

Mawadda ta nufi dinning table inda ta ajiye abincin da ta shiryawa su Haj Mama bisa umarnin mijinta.

"Yi hakuri Antinmu kirana akayi ta wayarsa ni tawa ta lalace. In kawo muku abincin nan kasa ko na barshi a nan?"

"Sauko dashi muna kallo muna ci"

Haka ta kai musu ta hado da plates suka ci suka sha ba godi bare nagode. Sai ma da suka gama Hansa'u tace wai zuciyarta tana tashi kifin miyar yana neman dawo mata. Mawadda tana yi mata sannu taje ta kawo mata cingam.

Zama tayi cikinsu tana hira da yara tunda su tasu suke daban.

Labulenta Furere ta nuna "laaa Hansa'u kinga irin labulen nan da muka gani a kofar wambai mutumin yace akwai kyau a ido sai rashin kwaliti shiyasa suke arha"

"Aikuwa shine. Tun dazu nake masa kallon sani"

Maganar ta yiwa Mawadda zafi sai share. Sunyi dabdalarsu a gidan har akayi magariba. Bayan ta sake yi musu girki sunci abinci tana wanke-wanke Hansau ta sake cewa tana jin tashin zuciya. Daga kitchen din ta fada mata inda zata duba a falon ta sake daukar cingam.

Anti Furera ta tashi tayi hanyar kitchen din "Ke kuwa da anyi magana sai ki ce aci cingam kamar wata tsohuwar karuwa"

Ko motsi Mawadda ta kasa don bakinciki itama Hansa'un da akayi dominta fuskarta ta sauya alamun rashin jindadi.

Ganin haka nata jikin yayi sanyi ta tura babban danta har dakin su tace ya kira Dahiru yazo ya kaisu gida. Duk da baiji dadin shigar yaron ba don a kalla shekarunsa kusan sha daya amma yaji dadin zasu tafi. Jeans da shirt ya saka ya fito.

Kowa ya mike burin kunya Anti Furera har kitchen ta shiga "amarya mu zamu tafi babu rakiya"

"Hannu zan dauraye gani nan"

Ta rakasu har kofar kasa da irin tarkacen gidan amare kayan zaki da na kwalliya da ta bawa yaran. Ta yiwa Dahiru adawo lafiya ta koma. Tana rufe kofar saman hawayen da ta rike tun da aka jefeta da wannan kalma suka soma zuba ba kakkautawa.

Da jan kafa ta koma ta gyare gidan tsaf tana aiki tana sharar hawaye. A ganinta fyaden da aka taba yi mata shine dalilin da yasa har Anti Furere ta iya danganta ta da wannan kalma.

Idanunta sun kumbura da ta fito daga wanka ko abinci bata iya ci ba ta saka rigar bacci mai kyau tayi kwanciyarta.
Chapter 59 · 0% Book details