← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 68

Sashe 32

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaisawa yayi da 'yan uwansa maza yayin da ya dauki yarinyar wajen Danlami ta bata wuce shekaru biyu ba yana mata wasa. Shi kuma Bilya ya fita waje amsa waya.

Hansa'u ta shigo fuskarta tasha kwalliya saboda tun dazu da ya kira Bilya yace zai zo itama yayarta ta sanar da ita ta shirya yau duk tsiyarsa sai sunyi zance. Yadda yake yiwa yarinyar hannunsa wasa ne ya bawa kowa mamaki. Ba wai mutum bane mai girman kai ko wani abu makamancin haka. Sai dai duk wasansa da yara baya dadewa zai mikawa iyayensu. Yau kuwa har dokin wuya ya yiwa Humaira mai sunan Innarsu.

Furaira ta kalli Hansa'u wadda ta shagala wurin kallonsa kamar wata tsohuwar mayya.

"Kin dai gani maigidan naki yana da son yara sai ki dage zubin farko ki watso masa 'yan biyu"

Danlami ya soma dariya "zubin farko kuma kamar kwasar adashi? Enjiniya ashe kun daidaita da Hansy baby bamu da labari"

Siddiqa matar Danlami ta watsa masa wata muguwar harara.

Kashe mata ido yayi "Maida wukar Hajiyata yau tsokana nake ji. Kinsan sabon kamu ga dukkan alamu an lasa masa tsohuwar zuma a inda yake"

Hansa'u ta hau harararsa balle da Dahiru yayi banza dasu duka sai murmushi da yake yi shi kadai. Hakan yasa su tunanin ko budurwa yayi.

Furaira taji haushi ta kalli Bilya shi da ba ruwansa.
"Lokaci yayi da zamu san a wane matsayi Dahiru ya ajiye min kanwa. Saboda shi ta dawo gidan nan kuma taki sauraron kowa amma kana kallo yake wulakanta ta. Idan yana tunanin saboda wani abin hannunsa ne ai ya san irin masu kudin da suke zuwa wurinta take kin fita."

"Kada in katse miki hanzari amma mai guri tazo duk wasu masu tabarma ko masu son shimfidawa sai su nade. Tauraruwar Yayanmu Dahiru ta dawo ga dukkan alamu da haskenta don Allah ki sararawa yarinyar nan ta fitar da wani cikin masoyanta" cewar Danlami.

Kowa zuba masa ido yayi banda Dahiru wanda ya shiga danna waya kamar baya wurin. Bashi da niyar wulakanta Hansa'u amma ya tabbatar da biyu Furaira ta nacewa son ayi auren. Sannan ko da can ba sonta yake ba.

Furaira tabi Danlami da kallo kafin ta iya cewa "yarinyar nan da aka yiwa fyade kake nufi Danlami?"

Ya gyada kai shi kuwa Dahiru wannan kalma ta fyade ce ta kular dashi ya tashi ya fice ko sallama babu.

Rai a bace Furaira ta fita daga falon itama ta bar sauran cike da mamaki. Fitar Dahiru ta tabbatar da zancen Danlami. Wayar Inna ta kira tayi sa'ar samu kuwa ta sanar da ita ashe Dahiru yana tare da Mawadda duk tsahon lokacin nan shiyasa yaki aure. Harda karin cewa a bincike shi a tabbatar ba aurenta yayi ba bada sanin kowa ba.

Hankalin Inna ya tashi tasa yaron makotansu ya danno mata sunan Dahiru ya kira. Lokacin shigarsa gida kenan tace masa gobe komai dare idan ya taso daga wurin aiki yazo tana nemansa taji komai tsakaninsa da Mawadda daga wurin Furaira.

Baiyi mamaki ba sanin halin matar yayan nasa shima hakurin zama yake da ita. Ya dai kudurce niyar wannan karon ba gudu ba ja da baya. Duk wata soyayya da yake jin ta kwanta har ya kasa kula wasu matan ta dawo daga ganin Mawaddatan wa Rahama.

*****

Shirinsa na komawa gidansu Mawadda ya warware a dalilin kiran da Inna tayi masa. Shima kuma akwai maganar da yake son yi musu ita da Baffa. Izinin fita ya nema saboda baya son kwana idan yaje ya samu da kyar aka barshi ya tafi. Dashi akayi sallar azahar a Tariwa bayan yaci abinci ya zauna tare da iyayensa.

Baffa ne ya soma magana yace suna bukatar sanin gaskiya game da zancen da Furaira ta kawo jiya.

Dahiru ya warware musu komai tun daga katin auren Rafi'a da Danlami ya bashi zuwa yanzu harda sakon gaisuwar su Baba.

"Baffa na dade ina son muyi maganar su Baba daku Allah bai nufa ba sai yanzu. Ku iyayena ne kuma duk abinda kuka yi na hana aurena da Mawadda nasan kunyi saboda ni ne. To amma kada ku manta daku muka je asibiti likita ya tabbatar fyade ne. Ade tazo har gidan nan rokon rufin asiri Ummiyo ta tona. Daga wannan lokacin wane irin tozarci ne basu gani ba karshe harda kora daga garin nan. Baba barin jiki ya mutu Malam mai rasuwa kuma ga tsufa daga ranar da aka koresu bai kara haduwa da mahaifinsa ba sai jana'iza da yazo. Ku duba wannan al'amari babu wanda yafi karfin jarabawa irin wannan. Me zaisa don ta afka musu kowa ya juya musu baya? Wallahi har yau ana fyade kuma mace da danginta sune kadai suke fuskantar kalubale daga abinda bai zama laifinsu ba. Ina laifin wanda yake neman halak da guminsa Baffa? Maimakon a lokacin mu hada kai mu jajirce wurin kwato musu hakkinsu ta yadda gobe wani mai kudin zaiyi shayin yiwa 'yar aiki fyade sai aka juya musu baya. Wannan yana daga cikin dalilan da suke karawa duk wani mutum bata gari karfin gwiwa domin yasan indai yana da kudi idan yayi babu wanda ya isa dashi. Ko ban aureta ba a lokacin yaci ace mun tsayawa juna."

Yana magana Inna ta share hawaye tana kallon Baffa "ni dai na dade abinnan yana ci min rai amma kunya da tsoron yadda zaka dauki zancen yasa na kasa magana"

Shiru Baffa yayi kamar bazaice komai ba sannan ya nisa yace "Allah Yayi maka albarka Dahiru. Karshen mako kazo ka daukemu muje gidan Mal Fatihun"

Mamaki Dahiru yayi sosai yadda iyayensa suka yi saurin saukowa. Ya tsallake wannan saura kuma neman amincewar Mawadda ya sake tado da zancen aurensu.

Abinda bai sani ba shine duka iyayen nasa kowanne shi kadai ya dade da nadamar biyewa son zuciya akan abinda ya sami su Mal Fatihu amma sun kasa yiwa juna zancen. Batun yiwa 'yan aiki fyade wasu ma su dawo da ciki kuwa ko ba a garinsu ba suna ji sosai a makota amma har yanzu an rasa wani mataki da ya kamata a dauka domin dakile cutar da marasa karfi da akeyi.

Bayan la'asar ya sake daukar hanya cike da farinciki ya tafi. Zancen da suka yi da Inna a dakinta ya tuna yayi murmushi. Cewa tayi kada yayi gaggawar sake neman auren Mawadda har sai sunje sun fuskanci wace rayuwa tayi bayan rabuwarsu. Tado da zancen da tayi kawai yasa shi sanin cewa akwai yiwuwar amincewarsu kenan.

A gajiye sosai ya isa gida sai da yayi shirin kwanciya wurin karfe goma ya kira Mawadda.

Tana aikin hada turaren wuta saboda wasu amare biyu da zata fara yiwa gyaran jiki taji wayar. Hannunta ta goge ta dauka da sallama hade da faduwar gaba ganin mai kiran.

Amsawa yayi yana jin wata annashuwa tana ratsa shi.

"Da karfinki ki ka dawo naga alama"

Tayi 'yar dariyar da sautinta ya sake jefa shi cikin wani yanayi mai dadi "Karfi kamar wata 'yar dambe?"

Ajiyar zuciya taji ya saki har tsigar jikinta ta tashi "da gaske nake, ban san ta yaya zan kwatanta miki yadda nake ji game dake ba yanzu. Tunda na hadu dake shekaranjiya na kasa ganewa SO ne, KEWA ko duka biyun ne a tsakaninmu"

"Yayanmu!"

"Na'am"

"Kayi hakuri kada muje nan. Ni da kai yanzu wa ne da kanwarsa." Yadda tayi maganar mai ji zai fahimci akwai ciwo a tattare da ita wanda take kokarin dannewa.

Hakan ya taba zuciyar Dahiru sosai yasan tana kokarin boye damuwarta ne kawai don babu yadda zatayi "haka kika zabar mana? Mu koma wa da kanwa?"

Kai ta gyada kamar yana kallonta.

Yace "to naji amma idan mun tashi mu kara da zama abokan sirrin juna. Ke kanki kin sani abinda yake tsakaninmu mai girma ne. Kinga ina da abubuwa da dama da nake son baki labari Mawadda...Nace miki yau zan zo naji yadda rayuwarki ta kasance kema amma da ki ka ji shiru babu ko cigiya"

"To kayi hakuri"

Yasan akwai aiki a gabansa indai yana son ya dawo kamar da ko ma fi a wurinta yadda zata bada kai bori ya hau. Lallabata zaiyi a hankali ya sake cusa kansa. Ya iya hakurin shekaru takwas ma basu hadu ba bare yanzu.

Tambayarta yayi cikin sigar wasa "Gobe nazo?"

"Uhmm" ta iya cewa kawai. Saboda muryarsa idan yayi magana yanzu jinta take har ranta. Anya zata jurewa wata alaka tsakaninsu idan ba soyayya ba? Ita kanta tana mamakin yadda ya dawo cikin rayuwarta yake neman wargaza duk wani shiri da katanga da ta gina tsakaninta da maza.

"Nagode Kanwarmu Mawadda" ya fada a hankali yana jan kowane harafi.

Haka nan taji tana son yasan tayi ilimi itama yanzu shiyasa tayi masa sallama da turancin da ko lokacin da tayi firamare a garinsu yasan bata iya ba "Sweet dreams Yayanmu Dahiru"

Ai kuwa ba karamin dadi yaji ba da mamaki sai da yayi da gaske ya iya cewa "mafarki na daya ne. Naki. Kuma yanzu kin hana tunda bai kamata wa yayi mafarkin kanwarsa ba. Amma duk da haka bari na kwanta da kyakkyawar addu'a kila nayi sa'ar ganin wadda zata zama matata don aure nake so wallahi"

"La ila ha illallahu" tace tana dariya kasa kasa sannan ta kashe wayar kafin ya sami damar sake magana.

Dariya yayi ya gyara kwanciyarsa "you can't escape easily adorable Mawadda".
******

Cikin bacci yaji waya ya farka. Shadaya da kusan rabi lokacin. Ko bai gaji ba yanayin aikinsa yasa ya koyi baccin wuri. Bai gane nambar ba amma ganin wayar ta katse an sake kiransa shiyasa ya dauka. Yana kara wayar a kunne yaji ance

"Ahirin..."

Takaici ne ya kama shi yaja siririn tsaki. Mutum daya ke kiransa da wannan sunan kuma muryarta yaji. Sai dai bai ga wani dalilin komai kankantarsa ba da zaisa ta kira shi a wannan lokacin.

Cikin zakuwa Qareeba ta sake cewa "Ahirin kana jina? Safwan ne nayi ta nema ya bani number dinka da ka bashi lokacin da kazo wayarsa a kashe sai yanzu na same shi"

"Naji, naji ya akayi?"

"Hmmmm dama magana ce nake so muyi idan da hali gobe sai kazo gida ko ni nazo office dinka. Duk wanda ka zaba is okay with me"
Chapter 32 · 0% Book details