← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 68

Sashe 36

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nasan kina son Dahirun nan Mawadda bazanyi muku katsalandan ba har sai naga yadda ta kasance. Ki sani dai ni masoyinki ne mai burin kyautata rayuwarki. Ina fata zumuncinmu ya dore ba wai kawai tsakanin likita da patient ba"

Taji dadin saurin fahimtarsa don bata jin zata juri fama da maza biyu akan abinda duka babu lallai su samu. Sun jima suna hira kafin wata nurse ta shigo tace ya bar mutane suna jira fa.

*****

Hira Dahiru da Attahir suke yi suna tsara bikin Attahir din da yake gabatowa nan da wata uku.

Ango yana ta zumudi suna lissafin nawa za'a ware domin hada lefe da sauran abubuwa. Ga kama gida da yake son yi shima basu gama zabar unguwa ba.

Attahir ya nuna masa hoton wasu akwatuna masu kyau da yake son zaba cikinsu.

"Ba don ka tsaya ruwan ido ba kaga kamata yayi komai muyi tare. Akwatunan nan so nayi na saya mana iri daya amma kada a saya har su fita yayi baka tsayar da mata ba tuzurun Haj Mama"

Dahiru yayi dariya "yanzu ma ai komai taren muke yi. Mata kuma kasha kuruminka Haj Mama ta kusa dena yi min korafin rashin aure ana kirana tuzuru"

Dundu Attahir ya kai masa yana cewa yaci amanarsa tunda bai sanar dashi da wuri ba. Labarin sake haduwa da Mawadda ya bashi domin kuwa amincinsu yasa ya sanar dashi rayuwarsa ta baya. Attahir na murna da wannan al'amari Dahiru ya sako zancen Anti Qareeba. Sunci dariya musamman Attahir wanda yaso kwarai ace yana wurin
"Da na wanke 'yar rainin wayo. Ni ka tabbata mamanta likita ce kuwa ba irin dafta dinnan da ake karawa gaban suna bace don ado?"

"Baka da kirki har asibiti gareta fa"

"To ai abin nasu ne ba ko kunya, gaskiya idan ka auri Qareeba sunan 'ya'yanka sorry. Tun wuri ma ka sani irin hadin zumuncin nan bazan yarda ba kada a cuceni a hada ni da jikoki 'yan ahirin"

Yana fada ya tashi a guje don Dahiru bayansa ya bi suna dariya. Haj Mama tana shigowa taja tsaki tana girgiza kai.

"Allah nagode Maka. Kattin maza maimakon su kawo min yaransu in rinka jin hayaniyarsu ina bari bari shine da kansu suke cika min kunne. Kodayake gara kai Attahir, wani yana nan sai sayen kaya da takalma yana kwalliya."

Dahiru yayi dariya yasan dashi take. Iyalin gidan nan suna kaunarshi suna nuna masa soyayya tamkar jininsu. Attahir ne yayi mata albishir da an kusa gabatar mata da suruka ai kuwa ta washe fuska tana murna.

Bayan fitarta ya matsawa Dahiru ya kamata su je ya ganta ya kara wasa mata dan uwansa don tayi saurin amincewa.

Tagumi Qareeba ta rafka tana zaune daga ita sai zani da tayi dauri ya leko ta kasa sai wata vest da hannut daya ya sabule. Ko wanka bata yi ba tun safe. Rashin mijin nan fa yana damunta sosai.

Dr Tani ce ta shigo dakin rike da leda ta dora mata akan cinya.

"Qareeba bana son wannan damuwa da kika shiga 'yan kwanakin nan"

"Kiji Mummy fa na rasa mijin aure ya bazan damu ba? Dashiru ya gujeni saboda wulakancin da kika yi masa da." Ta kare da tura baki.

Bakin Dr Tani ta doke "shashasha karshenta ma Dashiru kika rinka kiransa a gabansa ba dole ya gujeki. Yanzu dai bude ledar nan ki duba"

Ihun murna ta saka bayan ta bude . Material ne mai matukar kyau da tsada. Kamar yarinyar da aka yiwa kyautar bazata tace
"Mummy nawa ne?"

Zama Dr Tani tayi sannan cikin murna itama tace "ki tashi kiyi wanka ki kai dinki. Next week sunday Babawo zai zo wurinki. Ya dawo kuma da maganar aure"

Sakin kayan tayi "Cabdi sai kace wata mara aji Mummy? Sai da ya gadamar dawowa za'ace yazo neman aure. To ni na wuce ajinsa wallahi Dashiru nake so ki fadawa Daddy kawai"

Ranta ya soma baci don Qareeba bata san yadda ta zubar da nata ajin bane saboda nema mata miji.
"Dahirun me, har nawa yake kuma me ya taka? Banda ma lalura shi har zai taba yin arzikin da zamu roki alfarma wurinsa ne?"

Har ranta Qareeba bata so ana fadin abu mara dadi ga Dashirunta yanzu. Daukan kayan tayi ba don taso ba ta ajiye akan gado ta shiga wanka.

Da ta shirya ta fito ma kana ganinta kasan an bata mata rai. Dr Tani bata son biye mata dama ina su ina Dahiru dan mutan Tariwa. Kawai dai taso amfani dashi ne lokacin da babu kowa. Ita ba wai kudin su Haj Mara ne ya dameta ba kamar son 'yarta tayi auren da zai bawa duka danginsu 'yan bani na iya mamaki. A yanzu ansa musu ido kamar su kadai suka fara haihuwar 'yar da ta rasa miji.
******

Yadda Attahir ya matsawa Dahiru dole ya kira Mawadda ya sanar da ita zai zo da dan uwansa su gaisa.

Tana kwance tana hutawa sanda ya kira. Taji dadin jin zaizo don kwana tayi tunaninsa da kuma tunanin maganarsu da Baba. Ya zama dole ta yaki zuciyarta ta dakatar da alakar da take tunanin zata kare a ciwon zuciya. Shawarar Dr Imran zata bi da yace ta yawaita addua amma duk da haka zata yi kokari wurin janye masa.

"Sai ana magana dake ki shiga tunani. Shirun na mene?" Dahiru ya fada don ya fara ganeta da yawan tunani yanzu.

Mikewa tayi kafin tace "tunanin saurayina, sai dai kazo zan baka labari yau zance naje"

Sai da ya fito daga falon ya iya amsawa yadda yaji wani bala'in kishi ya taso masa abin har mamaki ya bashi.

"Me kika ce?"

Muryarsa ta fahimtar da ita yadda yaji sai kuma ta soma karaya.
"Asibiti naje ba na fada maka ina zuwa checkup ba"

"Mawaddatan wa Rahma!"

"Na'am inji larabawa"

"Bana son wannan wasan don Allah da gaske zance kika je? Likita ne saurayin naki?" Yayi magana cikin cijewa.

Sosai ransa ya baci da kishin da ya rufe masa ido. Bai jira ta ansa masa ba ma ya nanata mata zuwansu yanzu ya kashe wayar.

Hannunsa yasa ya rike bakinsa da habarsa idanunsa suka kankance. Karshe ya koma ya dafe saman motar Attahir da hannuwansa biyu ya dukar da kansa yana kallon kasa.

Attahir da yaji bai dawo ba ya fito ya sameshi a haka. Kafadarsa ya dafa hakan yasa shi juyowa suna kallon juna.

"Me ya faru?" Attahir ya tambaya don kallo daya zaka yi masa ka gane baya cikin nutsuwa.

"Wai ni Mawadda zata cewa taje zance? Likitan da yake dubata saurayinta ne. Wallahi bazan iya sake rasata ba Attahir. Na sota sosai a baya amma yanzu ni bansan yadda zan kwatanta maka kaunar da nake mata ba. Ban taba son wata mace ba sai ita kaima shaida ne"

Motar Attahir ya bude suka shiga sannan ya kalli Dahiru "calm down bro, har ka manta rabonka da ita ne kake tunanin yanzu komai zai zo da sauki kamar ba'ayi ba?"

"Nayi zaton itama tana sona....na tabbatar ne ma. Baka ji yadda kalamanta suka tsaya min a rai ba"

Attahir ya jinjina kai "ashe haka kake da kishi Dahiru? Lallai Mawadda sai tayi a hankali"

Shiru kawai yayi Attahir yaja mota suka fita. Lokacin da yaji labarin anyi mata fyade abu daya ne a ransa wato aure. Sai dai yafi kowa sanin me ya jima yana dannewa har mutane suke masa kallon kamar mutum marasa damuwa a rai. Ko Mawadda baya son ta san yadda yake burin haduwa da mutumin da yayi mata fyade. Ko ranar da tace masa taje Kaduna da ya bagarar da zancen yayi ne kawai saboda yadda yaji abin zai fama masa tsohon ciwonsa. Soyayyarta da son sanyata cikin farinciki sune suke dakushe bacin ransa da kishin da yake damunsa game da kaddarar da ta sameta.

Suna fitowa daga gidan daidai lokacin Qareeba ma ta fito zata kai dinki. Dahiru ta hango jiki na rawa ta zuke glass ta soma kwala masa kira. Ganin bai ji ba yasa kawai tabi bayansu.

Attahir yana ta kwantarwa da Dahiru hankali kafin su tsaya a gidan mai ya sami nutsuwa sosai.

Ana zuba musu mai Attahir yana waje kusa da me zuban man yayin da Dahiru yake zaune ya kwantar da kansa jikin kujera hade da lumshe idanu.

"AHIRIN" Qareeba tace da karfi tana tsaye daga waje saitinsa.

A firgice ya bude ido yayi tozali da ita. Tsabar rudewa ma ya manta ina yake ya taso da karfi ya buge kansa. Dama gashi rai a bace abu ya tarar masa.

"Lahhhh Dashiru sannu kaji" tace da ya fito.

Attahir kawai ya gani a gefensu yana murmushi don tana cewa Ahirin ya zagayo ya kuma gane ko wacece.

Kin kulata Dahiru yayi Attahir yace "Anti Qareeba daga ina haka"

Habawa dadi kamar ta saka ihu ta rabe jikin mota ta rufe fuska da mayafi irin na jin kunyar nan. Dahiru kansa sai da yayi murmushi sannan yace.

"Mai kika zo sha kema?"

"A'a na fito zani wurin dinki ne na hango ku shine na tsaya mu gaisa" ta sake amsawa tana ta fari da idanu.

Attahir ya gimtse dariyarsa "ko dai dan uwana ya hure miki idon ne naga yana ta kadawa"

Dahiru ya watsa masa harara ita kuwa ta kuma sunkuyar da kai "Kai dai baka da kunya da alama. Dashiru ashe kana bawa 'yan uwanka labarina gashi har ya ganeni. Don Allah ka ajiye komai ka dawo su Mummy sun amince da soyayyarmu. Yaya sunanka ne?" Ta kalli Attahir.

Yayi dariya "Ni Attashir nake"

Sakin fuska tayi "sunanku kusan daya da My Man"

"Kut..." Dahiru yace tsabar mamaki wai my man, sai dai bai sami damar karawa ba Attahir ya sakar masa dundu a baya yana masa sannu wai ya kware. Shi kuma yana make tasa dariyar da tarin karya.

Duk ta rude "Man sannu wayyo me ya sameka haka? Attashir do something mana!"

Attahir dariya taci karfinsa Dahiru bakinciki ya turnuke shi zata tara musu mutane an fara kallonsu ya ma kasa magana sai biye masa da yayi yana duka bayan nasa.
Chapter 36 · 0% Book details