← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 68

Sashe 1

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[03/12 23:02] Meela Adeel: *GUMIN HALAK...*馃挵3

*Batul Mamman*馃挅

Jirgin safe Alh Sule Chanji ya biyo yana ta tararrabin me zai tarar a gidan. Da shigarsa ko sama bai hau ba yaje dakinsa ya huta yayi wurgi da jakarsa da babbar riga ya sake ficewa. Baya ya zaga dakin BB yana kwala masa kira rai a bace.

Haj Mara tana ji ta fito da sauri don tasan zuciya irin ta mijinta. Kafin ta karaso ya banka kofar dakin BB yana bacci yaji wani mugun bugu domin kuwa da kafa mahaifinsa ya haure shi a ciki.

"Tashi mutumin banza wanda bai san inda ke masa ciwo ba. Yanzu Babawo har kayi girma da wayon danne mace ka gwada mata karfi? Lalacewar taka har ta wuce ace kana bin mata sai dai ace kana yiwa mata fyade? Ni kuwa me na rageka dashi? Tarbiyya ko ilimin boko dana addini"

Tuni BB ya koma bayan Haj Mara yana rike da cikinsa da ya kulle saboda harbin da ya sha. Alh Sule bai hakura ba ya sake yowa kansa tayi saurin tarewa.

"Haba, haba Alhaji! Kashe min yaro zakayi akan wata mai aiki"

Dariyar takaici yayi dama ita akan 'ya'yanta musamman BB kowa bai isa ba.

"Dole kice haka mana tunda ita mai aikin uwarta ba nakuda tayi ta haifeta ba. Nuna tayi a bishiya suka tsinkota ga dukkan alamu" ya fada tare da juyawa zai fita sai kuma ya dakata "ki sameni a mota muje asibitin na dubata. Idan taji sauki har gidansu zamuje kuma wallahi ko kunki ko kunsu Babawo sai ya aureta"

Haj Mara ta tafa hannu alamun dama na fada dinnan "Ahaf ai na sani, to ka makaro don tun jiya na mayar da ita kauyensu"

A harzuke ya juyo zuciyarsa na tafarfasa.
"Kika yi me?"

"Nace tana gidansu. Haba ka shigo babu neman karin bayani duk zaka hatgitsa mana gida. Abin nan duk rashin fahimta ne"

Tsayuwarsa ya gyara yana kallon yadda take wani kare danta kada yayi yunkurin dukansa
"To fahimtar dani"

"A dakin nan na ganta kwance shine nayi zaton wani abu ne ya sameta. Sai da na bincika ashe sata tazo yi masa shi kuma sarkin zuciya yayi mata duka. To ni bazan iya zama da barauniya ba shine na mayar da ita"

Daga bayanta BB ne yake dariyar shakiyanci jin mahaifiyarsa tana gilla karya. Alh Sule yayi murmushi mai ciwo
"Kinga dan naki ma dariya yake miki saboda yaji kina sakin kwai a gabansa. Kukanki lokacin da kika kirani ya isheni hujjar da zance yanzu karya kike yi. Ki gama kwana-kwanar kizo muje garin nasu. Idan mun dawo sai kiyi min bayanin dalilinki na fita ba da izinina ba"

"Alhaji!"

Bai saurareta ba ya fita ta bi bayansa da sauri. A bakin bene ta same shi zai hau sama

"Ko aurena ne zai mutu bazan taba kaika garinsu Mawadda ba. Na riga na bata kudi har dubu ashirin ga kayayyakin sawa. Magana ta riga ta mutu sai dai a kiyayi gaba kawai"

Rasa abin cewa yayi. Wai dubu ashirin. Ko dubu dari biyu ta basu ai bazai zama fansa ga mutumcin 'yarsu da aka zubar ba. Ransa ya kai kololuwar baci har ya rasa matakin dauka. Yasan Mara bata da kirki amma baiyi zaton harda rashin hankali da tunani ba.

"Ni dai na aurar da yarana mata duka ban taba jin wani labari mara dadi game da mutumcinsu ba. Har izuwa yanzu Allah bai taba bani ikon yin lalata da 'yar kowa ba. To Alhamdulillah. Ke da danki ku jira sakamako. Shi sharri dan sakone. Idan ka aike shi ya isar da sako sai ya dawo gareka. Ki rubuta ki ajiye lokaci shi zaiyi muku alkalanci ke da shi da yarinyar da kuka cuta" daga haka ya haye sama abinsa sai karar kofa taji garam.

Tsaki tayi ko a jikinta. Tunda dai ya bar maganar aje a haka.

"Alkhairi zamu gani har duniya ta tashi mugun fatanka bazai bimu ba"

Babawo kuma aure zata masa kafin ya sake sakata a tsaka mai wuya.
******

*Asalin Mawadda*

Mal Fatihu Wali dan kauyen Tariwa ne ta cikin karamar hukumar Bebeji a jihar Kano. Sana'arsa dinkin hula wadda wani dan kasuwa a Kwari yake zuwa sara lokaci zuwa lokaci. Sai kuma 'yan garin wani zubin. Idan babu cinikin hular yakan taba noma da kiwo.

Auren saurayi da budurwa sukayi da Haule. Suna zamansu lafiya Allah Ya azurtasu da 'ya'ya mata har hudu ya dauki soyayya ya dorawa iyalinsa.

Wata rana kanwar mahaifinsa taje ta sami baban nashi da kuka tana rokon ya taimaketa yasa Fatihu ya auri babbar 'yarta Sa'ade. Koda ya tambayi dalili ashe wani ne daga dangin babanta yake neman aurenta iyayen suka hana saboda marainiya ce ba idon uba kuma a cewarsu babarta tana da farar kafa don suna aure komai nasa yaja baya ciki kuwa harda lafiya da tayi masa karanci har tayi ajalinsa.

"Yaya Wali yarinyar nan bana shekararta daidai har goma sha tara. Habaici babu irin wanda ba'ayi min. Shine naga nima ba 'yan uwa na rasa ba. Don Allah kasa baki Fatihu ya aureta tunda sauran duk ta girme musu shine dai zai dubi zumunci ya taimaki 'yar uwarsa"

Mal Wali yayi shiru yana nazari. Baya son shiga sabgar gidajen 'ya'ya saboda rike girmansa. Sai dai ganin hawayen 'yar uwarsa ya taba masa zuciya. Haka ya kwantar mata da hankali sannan ya umarci Fatihu da aurenta. An kai ruwa rana dai saboda shi Fatihu baya son matsawa matarsa tunda suna zaman lafiya. Ita kuma Sa'ade har yanzu Balarabe take so dan wan mahaifinta duk da rashin mutumcin da ake yiwa mamanta.

Haka dai akayi auren. Tsakaninta da Yaya akwai girmamawa sosai amma fa bata ragawa Fatihu ko kadan da farko. Abu na Allah zama yai zama sai gashi sun dinke tamkar tsofaffin masoya. Ba jimawa sai ciki nan fa soyayya ta karu. Ta haihu lafiya aka sakawa yarinya suna Mawadda.

Wata rana a lokacin Mawadda tana da shekara daya da rabi kawar Sa'ade tazo daga Misau inda take aure. Suna hira take cewa "Oh Sa'ade kamar ba ke bace mai cewa idan aka aura miki Fatihu sai kinyi ajalinsa in bai sakeki ba"

Sa'ade tayi murmushi tana cigaba da yiwa Mawadda tsifa "ke dai bari...."

Iya abinda Fatihu yaji kenan ya juya da ledar hannunsa mai cike da magwaro da aka bashi ladan aikin lodi da sukayi a gonar wani. Ganin Sa'ade ce da girki shine ya kawo ta raba yaji wannan mummunan kalami.

Baiwar Allah Sa'ade ta cigaba da cewa kawarta "....kullum nayi sallah sai nayiwa Iya addu'a saboda ita tayi sanadin hadani da Malam. Ina son shi..." ta rufe ido da tafukan hannayenta wai ita kunya.

Dariya sukayi su biyun harda tafawa suna ta yabon mazajensu.

Fatihu kuwa bakinciki kamar ya kashe shi. Ashe duk zaman nan da son da yake mata ita kashe shi take son yi kila ta komawa tsohon saurayinta wanda akace yaki aure har yau saboda ita. Tsabar takaici har kuka yayi.

Da yamma ya dawo Sa'ade ta tashi ta dauko masa ruwa don bata ma san ya shigo dazu ba. Kwanon shan ya tankwabe a hannunta ya mika mata hannu.

"Kwanto min 'yata ki tafi gida na sakeki saki uku"

Gabanta ne ya yanke ya fadi ta dafe kirji sai kuka
"Malam me nayi maka haka da zafi?"

"Kinfi kowa sani. Kafin ki kasheni dai gara na sawwake miki kije ki auri wanda kike so"

Ta ma rasa gane kan zancen shi kuwa ya hauta da fadan ta fice masa daga gida kuma ta bashi 'yarsa. Bayani taso yi masa don duk yadda akayi yaji hirarta da kawarta ta dazu amma yaki saurara. Yaya tana ta bashi hakuri ya daka mata tsawa itama. Haka Sa'ade ta durkusa tana ta ban hakuri amma bakin alkalami ya bushe. Maganganun da ya rinka fada mata cikin bacin rai yasa ta kwance goyon ta dangwarar masa da Mawadda a kasa. Yarinya ta hau kuka ko kallonta batayi ba saboda zuciya ta fice. Yaya ta dauketa zata bita yace idan ta fita kada ta dawo.

Gidansu kawarta ta ta fara zuwa tana kuka ta sanar da ita yadda sukayi. Ta tausaya mata tare da yin tir da bakinta da ya tado zancen. Daga nan suka wuce gidansu Fatihu suka sanar da iyayensa. Rayuka dai sun baci ranar musamman nasa. Balle da akayi masa bayanin karshen maganar gashi yayi hukunci cikin fushi.

Da kyar aka shawo kan Sa'ade ta karbi 'yarta don tayi fushi sosai da abinda yayi mata. Bayan ta yayeta aka mayarwa Yaya ita ta rike hannu bibbiyu. Mawadda ce take kiranta Ade shine sunan a hankali ya bita.

Sai bayan shekara uku da mutuwar aurenta sannan ta sake aure da tsohon saurayinta dai Balarabe. Iya bata so ba kamar yadda iyayensa basa so don ko auren fari baiyi ba sai dai ya kafa naci. Kano ya kai matarsa inda yake aikin walda.

Da farko kamar abin arziki suke zaune kalau. Daga baya ta gane mijin nata maketaci ne. Dan kudinsa a cikinsa yake karewa. Yaci banza yaci hofi. Shine teburin mai shayi shine gaban tukubar tsire. Iyalinsa kuwa kullum suna fama da garau-garau.

Da wahala ta ishi Ade sai ta fara kitso. Kan kace kwabo unguwa ansan da zamanta tana samun 'yan canjinta. Ganin ta soma samun sukuni wanda shi a wautar Balarabe mace tayi ta kwantar da kai gaban miji yana hura hanci shine aure. Sai cewa yayi mata na cika masa gida. Kitson nata sai ya koma bin gidajen mutane nan ma yace ta fiye yawo ga yaransu ba kulawa sosai. Ta hakura ta koma wankau yace danshi ya soma kama gidansa kada sanyi yayi musu illa. Surfe da dakan su yaji yace karar daka tana saka masa ciwon kai. Tuni hakurinta ya kare tace dole ta fita nema ko don yaran suyi karatu. Rigimar yau daban ta gobe daban har dai auren ya mutu shine ta fara aikatau. Shi kuma sai yanzu yake ta neman shiri a mayar da auren taki
******
Chapter 1 · 0% Book details