← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 68

Sashe 49

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Gabadayanku babu wanda bazan iya kora ba kun san haka ba tun yau ba. Yarinyar nan a gabanku aka kawota kowa ya sani duka ne kadai aka yi mata wanda ya janyo mata surgery har biyu. A wane dalili ne zaku rinka yawo da magana kaf clinic dinnan kowa cewa yake yi raping dinta aka yi"

Wani nurse ne da Qareeba ta taba yiwa haukanta a gaban maman budurwarsa tazo asibitin ta jefa shi cikin muguwar kunya ya kekashe idanu yace "Doctor sai dai fa ayi hakuri kowa ya sani case din rape ne ake ta wani rufa-rufa. Nasan dani ake saboda Qareeba taji lokacin da nake bada labari"

Wasu cikinsu harda dariya suna yi kasa-kasa ran Dr Tani in yayi dubu ya baci. Likitoci biyu da suka duba Qareeba lokacin ta kalla mace da namiji da shi ma nurse din tace.

"You are fired! Ni zaku ci wa amana ku batawa yarinyata suna ta rasa miji"

Mamaki ya kamasu domin ko kadan su likitocin basu su ka fitar da zancen ba. Namijin ya cire whitecoat dinsa ya bugata da kasa.

"Asibitin ma da kike yin kudi da guminmu amma kin kasa biyanmu halak dinmu yadda ya kamata? Meye bama yi domin cigabansa amma albashinmu bai taka kara ya karya ba. Mtswwww" ya juya a fusace.

Cikin kankanin lokaci wurin ya kaure da surutu. Da gangan ma saboda samun dama da yawansu suka yi ta cewa anyi fyaden kuma magana yanzu suka fara. Kusan mutum hudu ta kora daga aiki harda kukanta ta gurgura Qareeba dakinta.

Asibitin ko ina maganganu ke tashi hatta dakunan patients. Gashi ta kori likitoci biyun da suke on call a lokacin shiyasa komai ita ake kira.

Su Dahiru sun iso asibitin dukkansu suka shiga reception suna kiran azo a taimakawa Ade. Dr Tani kai ya dau chaji kamar zata zare gashi yau mutane da dama ake ta kawowa.

Da gudu gudu ta sauko ance mata emergency idonta ya sauka akan Dahiru. Sakin fuska tayi kamar ba ita ba.

"Dana daga ina haka ba yau ake kawo amarya ba? Ko ka biyo ganin Qareeba ne"

Ade ya nuna mata batare da ya amsa ba "ki duba mamana faduwa tayi har yanzu bata farfado ba"

Matsowa tayi da sauri ta nuna daki aka kaita aka kwantar. Ta duka kanta tana tambayar me ya sameta Iya ta rike mata hannu tana kare mata kallo "DaftaTani?"

Dr Tani ta gyada kai ta dago ta kalli Iya kamar ta san fuskar nan.

Bata yi aune ba taji an shako wuyanta ta baya. Tana juyawa Yaya ta watsa mata yatsu biyar ta rike kumatu a gigice. Baba bai ce komai ba haka Inna domin sun ganeta suma.

Dakin yayi tsit suna mamakin wannan abu. Dahiru Yaya ta kalla idanu rufe da bacin rai
"mu bar asibitin nan tun kafin Sa'ade ta farfafo ta sake sumewa saboda bakinciki"

Cikin tsananin mamaki yace "Yaya kun santa ne?"

Baba ne ya nunata "Dahiru wannan matar ita ce ta bada shaidar karya a kotu aka saki yaron nan gashi yau a karo na biyu ya sace Mawadda a ranar aurenta"

Dr Tani tayi mugun kaduwa. Iyayen Mawadda ne yarinyar da ta canja duka evidence dinsu na asibiti karshe aka kori karar BB.

Hayaniya ta tayar da Ade abin mamaki Dr Tani ta gani a kusa da gadon. Da sauri ta tashi tana zubar hawaye ta gama jin me suke cewa tace
"Karasani ki ka zo yi yadda ki ka watsa mana rayuwa shekarun baya? Ku kaini gida gara na mutu da ta tabani"

Bacin ran Dahiru bazai misaltu ba. Idanunsa tamkar gauta sun kara kankancewa. Wani mugun kallo yake yiwa Dr Tani wanda ya karasa razana ta soma ja da baya don a ganinta wannan kallon nasa kadai ya fassara mata zai iya karar da numfashinta a duniya batare da yayi nadama ba.

"Dahiru ka tuna zaman da muka yi a baya kayi hakuri ban san kuna da alaka ba. Ka gani yadda nima yazo ya yiwa 'yar uwarka Qareeba"

Fuska babu alamun annuri yace "kina nufin mutumin da na hana ya yiwa 'yarki fyade shine wanda ya yiwa matata a shekarun baya?"

Ta zaro ido "matarka kuma?"

"Mawadda nake nufi ko kin manta sunanta yadda kika manta cutar da kika yi mata da iyayenta?"

Jikinta yayi mugun sanyi ta gyada kai. Dahiru kamar ya zare haka yake ji a wannan lokacin. Kusan kowa a dakin tsoron yanayinsa yake ji.

"Ban taba nadamar taimako ba musamman idan musulmi na yiwa. Amma a yau Dr Tani nayi, naji a raina ina ma ban je gidanki ba a wannan ranar yadda ya dandanawa Mawadda bakinciki inama ya yiwa taki 'yar kiji yadda su Ade suka ji. Kina babbar makiyata ace nayi zaman aiki a gidanki...Ya Allah" wasu zafafan hawaye ya goge.

Attahir ya yunkura ya riko hannunsa ya kwace da karfi ya daga zai mareta.

Tsawar Baba Prof ce ta dakatar dashi "DAHIRU!!! Bamuyi maka wannan tarbiyar ba kada ka yarda ka daki matar wani"

Sauke hannunsa yayi zuciya na tafasa ya sake matsawa daf da ita har lokacin ta kasa magana sai faduwar gaba.

"A yau na auri Mawadda kuma a yau BB din da ya kusa yiwa taki 'yar fyade ya saceta bayan abinda yayi mata 8 years ago. Kiyi addu'a Tani, ki tsananta addu'a domin ni Dahiru Ishak nayi miki alkawari idan ya kuskura ya sake maimaita kusantar iyalina wallahi babu wanda ya isa ya hanani mayar da tsinannan asibitin nan naki toka kinji na fada miki. Sai na kona shi da duk wanda ya rage a cikinsa" ya kare maganar da kada yatsunsa biyu a gaban fuskarta suka yi kara.

Durkushewa tayi a kasa ta hada hannuwanta biyu "don...."

Attahir ya yatsina fuska ya kada mata yatsa "kada ki bata bakinki babu wanda zai yafe miki. If I were you zan sallami duk wanda yake asibitin nan don na san dan uwana baya magana biyu."

Tare suka fice da Dahiru iyayensu suna kallonsu sun kasa yi musu magana. A jikin bango Dahiru ya ga Qareeba tana wani irin kuka saboda sai a yau komai ya warware mata. Mummynta tayi karya ne kawai don tayi aure. Ko kallo bata ishe shi ba ya wuce ga wani bala'in zugi da hannun damansa yake yi saboda targadensa da ya fama.

*****

BB da abokansa suna ta sheke ayarsu sun yi biris da Mawadda da take bugun kofar iyaka karfinta kamar zata ballata. Kuka take yi haikan tana hadashi da Allah ya duba darajar aure ya saketa ta tafi.

Tafi awa daya tana bugu tun tana roko har ta koma fada da nasihar yaji tsoron Allah.

Gajiya tayi ta koma bakin taga ta leka. Karfe ne ta waje ko ta sauke glass din babu damar fita. Bata ma san wace unguwa bace saboda a hanya rudewa tayi tana ta buge bugen kofa da magiya bata kallon ina suke bi. Ta dai kula wurin akwai karancin gidaje sai filaye da kango.

Iyayenta da Dahiru take tunani tana kara kuka. Ta san duk inda suke hankalinsu ba a kwance yake ba. Gashi tun a hanya su ka karbe mata jaka. Da suka iso ya zagaya zai daukota tace ya barta zata shiga da kanta. Banda tsoronsa da ya gama mamayeta tana kyamar ya tabata da kazantarsa tana matar Dahiru.

Kofar taji ana tabawa bugun zuciyarta ya karu.

BB ne ya shigo yasha wanka harda gyaran fuska ga shadda da hula yana ta kamshi. Ledar hannunsa yaje gabanta ya ajiye ta matsa baya da sauri ta sake mannewa da bango.

Murmushin gefen baki yayi mata "wai duk amarya sai ta yi pretending tana tsoron miji ne? Ni fa na sani kuna so tsabar gulma ce kawai ace muku nagari"

Bata ce masa komai ba ya dauko ledar ya bude kaza ce a ciki tana tiriri da kamshi.

"Ga fa abin arziki kazar amarci matso mu ci tun da zafinta"

"Ko maita nake yi bazan ci abin hannunka ba ko da yunwa zata kasheni"

Ya kada kafada "suit yourself" ya fara ci kamar shine mayen.

Bayan ya gama ya dauko juice a cikin fridge dake dakin ya tsiyaya a kofi ya haye gado yana sha.

Ran Mawadda ya soma baci ta yarda BB mahaukacin gaske ne da taji yace "amaryata yau fa daren farko me ki ka tanadar min?"

Neman makami take yi ido rufe bata samu ba yana kallonta ta gama dube dubenta ta gaji ta dawo tsakiyar dakin ta durkusa gwiwoyi a kasa "don Allah ka taimaka ka barni na tafi gida. Me nayi maka haka da zafi ka kasa hakura har kake bibiyata?"

Dariya yayi yana buga kafa "ashe zaki saduda my baby. Sonki nake yi amma saboda kwarewa wurin cin amana ki ka auri wani ba ni ba. Ga sadakinki nan ki dauka a waccan drawer din domin nima na aureki daga yau. Ki kwantar da hankalinki mu zauna lafiya"

"Baka da hankali ne?" Tace cikin daga murya.

"Kin tafi dashi kin barni da dakon sonki a raina. Mawadda ki karbeni a matsayin miji zan rike ki da gaskiya"

Me kuma zata ce masa tunda alamu sun nuna bashi da hankali ko kadan.

Tashi yayi ya fita bai dade ba sai gashi da kayan bacci.
"Daga ni sai ke muka rage amaryata kowa ya tafi yau an bar mana gidan kiyi wanka don yau ranarmu ce."

Bata yi masa musu ba ta karbi kayan ta shige bandakin. Rufe kofar tayi da mukulli ta zame a kasa ta rizgar kuka. Burinta ta bude ido ta ga Dahiru a gabanta. Tana nan zaune sama da rabin awa taji BB ya soma bugawa yana cewa ta bude.

Da farko kamar lallami ya fara sai gashi ya rikide yana zaginta ta uwa ta uba yana cewa hakurinsa ya kare.

Rasa wurin buya tayi ta gama tsorata tana jin numfashinta kamar zai dauke. Robar watsa ruwa ta dauko ta tsaya daga gefen kofar yana budewa ta rafka masa a kansa iya karfinta ta fita a guje tayi sa'a dakin a bude yake.

Kofar gidan an garkame ta kasa budewa ya biyo bayanta yana kiranta. Kitchen ta hango ta shiga babu kayan kirki a ciki da sauri ta rinka jan drawers tayi sa'ar dauko wuka.
Chapter 49 · 0% Book details