← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 68

Sashe 38

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

BB ne akan ruwan cikin Qareeba ya matse mata hannuwa babu sutura a jikinsa kamar a dakinsa. Da zafin nama Dahiru ya fizgo shi ya kai masa naushi. Qareeba na ganin ya dagata ta mirgina gefe tana wani irin kuka. Minti guda da sun kara basu shigo ba da BB ya kafa mata tarihin fyade itama. Yaci mutumcinta karshe tamkar wani dabba. Kayanta da hannu ya tsarge su bayan ya gama dukanta. Dahiru ko kallonta baiyi ba ya haye kan BB dukansa yake iya karfinsa.

A daidai wannan lokacin babu abinda yake hangowa sai Mawaddansa da ta taba riskar kanta cikin yanayi irin wannan. Hakan ya kara masa kaimi ya jibgi BB iya karfinsa don ko motsin kirki ya gagare shi.

Kukan Qareeba ya dawowa da Dahiru hayyacinsa yaji tana kiran Mummy. Juyawa yayi Dr. Tani tamkar gawa a kwance. Sai da ya karawa BB duka a ciki da kafarsa sannan ya tsallake shi ya koma kanta. Dagata yayi amma duk da haka ya runtse idanunsa daga kallon Qareeba yace

"Zaki iya saukowa?"

"Eh"

"Ki rufe jikinki ki sauko muje asibiti ina jin suma tayi."

Wani zumbulelen hijab na sallar Dr Tani ta zura ta biyo bayanshi tana tafiya da kyar ga jini yana diga a kasa. Ashe glass ne ya soketa daga jug din da ta fada a kai wahala tasa bata sani ba.

Da gudu gudu Dahiru ya fita yana kwalawa maigadi kira. Shima a guje ya taho ganin Dr Tani a kafadar Dahiru yana son bude bayan motarsa ya sakata amma hannunsa sai rawa yake yi.

Maigadi ya bude masa yana tambayar me yake faruwa sai ga Qareeba ta taho fuska ta soma kumbura lebe da hanci duk jini. Gaban motar Dahiru ya bude mata ta zauna sannan ya kalli Maigadin.

"Akwai mutum a dakin Hajiya sannan ka kira maigidan nan..."
Lekawa yayi ta taga yace da Qareeba "zaki iya gane asibitin Hajiya?"

Ta amsa masa yace da maigadin ya fadawa maigidan ya samesu a can sannan ya shiga ya tada mota.

Qareeba sai kuka take yi tana kiran Dr Tani wadda har yanzu bata motsi. Dahiru ko danja baya tsayawa saboda tashin hankali balle da ya ga Qareeba ta rike kirji tana tari jini na fita. Da taimakon Allah ya isa asibitin. Ya fita ya kira wani da ya ga kamar likita ne yace masa Dr Tani da 'yarta ya kawo. Ana jin sunanta mutane suka yo kansa aka dauko su.

Tambayarsa ake me ya faru duk ya gigice tsabar tashin hankali. Yafi so Dr Auwal yazo sai ya fara fada masa. Kusan minti shabiyar yana kai kawo a korido din dakunan da aka shigar dasu kafin wata likita mace ta fito ya tambayeta yaya ake ciki.

"Qareeba taji ciwuka a jikinta amma munyi nasarar cire gilasan da suka farfasa mata jiki. Sai kuma buguwa da su fashewar baki wanda zata sami saukinsu a hankali. Babbar matsalar dai bata wuce cikinta da aka taka...mtsw ko waye wannan dabba ta fishi hankali."

Cike da damuwa yace "yanzu dai zata tashi ko kuwa?"

Kallon ido cikin ido tayi masa "zata tashi amma yanzu haka theatre zamu shiga da ita"

"Ki ka ce kuma da sauki?"

"Akwai internal bleeding a cikinta tana bukatar surgery yanzun nan"

Tafiya tayi ta barshi nan a tsaye cikin rudani. Zai shiga dakin da Qareeban take likitan dake tare da Dr Tani ya fito. Yace ta farfado amma jininta yayi mugun hawa. Suna wurin Dr Auwal da su Najib suka karaso. Dukkansu Dahiru suke kallo suna tambayarsa me ya faru.

Dakin da Dr Tani take ya nuna musu su ka shiga duka. Tashi tayi tana kukan ina Qareeba aka ce ta kwanta aiki za'ayi mata yanzu. Hankalinta ya sake tashi ta fara wani abu kamar mai farfadiya dole nurse tace su fita aka sake taruwa a kanta.

A wajen dakin Dahiru ya sanar dasu abinda ya gani. Dr Auwal yayi baya saura kadan ya fadi yana salati Safwan ya rike shi. Faisal ne yace basu ga ta zama ba ya kira Maigadi akan ya rufe gidan zasu zo da 'yan sanda ya fada masa ai mutumin ya gudu. Yaso tare shi yayi kansa da mota dole ya bashi hanya.

"Zancen da nake maka yallabai ya balle kofar gate din" ya karasa da tambayar ya masu jiki.

Kowa cikin damuwa yake likitoci biyu da nurses suna ta shige da fice a tsakanin dakunan har aka fiddo Qareeba wadda fuskarta ta gama hadewa don kumburi zuwa dakin theatre. Zama suka yi jigum har aka fito da ita bayan awa daya.

Ranar sun ga tashin hankali mara misaltuwa. Dr Tani sai allurar bacci aka yi mata saboda jininta yaki sauka kuma ta sawa kanta damuwa da rashin ganin Qareeba. Awa uku Dahiru yayi a asibitin sai da ya fuskanci kamar komai ya daidaita ya fito da alkawarin zai koma washegari.
*****

Bakin motarsa yaje amma jikinsa sai rawa yake yi da kyar ya shiga ya bar asibitin.

Tuki ya rinka yi sai ganin kansa yayi a layin su Mawadda. Ita kadai yake bukatar gani a lokacin a yadda hoton BB da Qareeba suka zauna a kansa. Tunda yake bai taba ganin masifa irin wannan ba. Karin tausayin Mawadda ne ya mamaye zuciyarsa da babu wanda ya kai mata dauki kamar Qareeba har aka rabata da mutumcinta.

Takwas na dare ta dan gota ya kirata. Tana dauka muryarsa gabadaya ta canja yace "don Allah ki fito ina waje"

Tashi tayi zaune ba shiri saboda yanayin da ta ji muryarsa kuma ya katse kiran. Kwakwalwarta ce ta shiga tunanin ko lafiya ta dai saka hijab ta sanar da Yaya yazo ta fita.

A zatonta yana kofar gidan sai ta hango motarsa a inda yake ajiyewa karkashin wata bishiyar darbejiya a kunne. Tasan ba haka suka saba ba ciki yake shigowa amma dai bari taje ta gani.

Kansa ta gani ya kwantar akan sitiyari saboda ya sauke glass din tayi sallama. Yana dago kai gabanta ya fadi. Tashin hankali da damuwa ne karara a tattare dashi.

Kallonta yayi yace "ki koma ciki dare yayi."

"Bangane in koma ciki ba daga fitowa ta" tace tana kara matsowa jikin motar.

"Tafiya zanyi kinga dare yayi. Dama ganinki kawai nake son yi"

Giya ta ga ya saka zai tafi ta zagaya daya bangaren da sauri tayi sa'a a bude motar take kawai ta shige.

Bata san irin dauriyar da yake yi ba a wannan lokacin. Yadda jikinsa yake babu kwari haka zuciyarsa tayi rauni sosai. A sanyaye yace
"Meye hakan?"

Ta riga ta san akwai matsala har ta soma kwalla tace "kai zan tambaya, ka fada min ko ma mene ne don Allah"

Jikinsa ta kula rawa yake yi ya hade hannuwansa a kokarinsa na boye mata. Tsoro ne kawai ya sake kamata ta soma kuka.

"Yayanmu kana ganin ban cancanci sanin damuwarka bane?"

Ba niyarsa yasata kuka ba. Hasali ma zuwa yayi don a tunaninsa ganinta ne kadai a wannan lokacin zai kwantar masa da hankali. Sai dai abin ba haka yazo ba. Ji yayi ya tsani kansa a baya da ya kasa gama tanadin aurensu har aka tura ta aikatau.

Runtse idanu yayi "ki koma ciki kada wani ya ganki a motar nan Baba bazai ji dadi ba"

"Wallahi bazan fita ba sai ka fada min ko kazo mu shiga ciki" tace tana hade rai.

Ya dago kai ya kalleta ta sake daure fuska.

"Naji fito muje".

Sai da ya fita sannan itama ta fito suka shiga ciki gabanta yana ta faduwa bata san me zai ce mata ba.

Sun zauna akan kujeru suna fuskantar juna duk ta kosa taji me zai ce.

"Ki yi hakuri da rayuwarki ta baya Mawadda, kiyi hakuri da talauci yasaki fita neman halak, kiyi hakuri da yadda talauci yasa aka danne miki hakkinki a kotu. Mawaddatan wa Rahma! Kiyi hakuri ni Dahiru banyi komai domin taimaka miki ba a wancan lokacin. Idan mutumin nan yana da rai ina fata Allah Ya hadani dashi ko sau daya ne...." muryarsa ce ta karye alamun yana boye kuka.

Maganganunsa da yanayinsa suka sake daga mata hankali. Yana magana tana hawaye zuciyarta tana tuna mata da kuncin da take ta kokarin mantawa. A tsorace tace "ka fasa aurena ko?"

Girgiza kai yayi "nan da kwana tara zaki zama mallakina in sha Allahu"

"Ka tayar min da hankali ka fada min abinda yake damunka mana. Me ya kawo wadannan maganganu?"

Da ace an daura aurensa da ita babu abinda zai hana shi rungumeta a wannan lokacin. Abinda yake zuciyarsa ya fada mata "Rarrashi nazo nema a wurinki Mawadda. Naso ace kin zama matata zaki iya rungumeni ki kwantar min da hankali. Ki rikeni kice komai mai wucewa ne. I need you a matsayin mata ba budurwa ba saboda a yau zuciyata ta hadu da mummunan tabo. Sai yau na gama fahimtarki da rayuwar da kika yi kina jinyar jikinki da zuciyarki"

Gabadaya ta tsinke da lamarinsa ya kara dagula mata lissafi. Tashi tayi zata fita yace ina zata je.

"Baba zan kira, na gaji da wannan juya maganar taka ka ki fahimtar dani yadda zan gane." Durkusawa tayi a kasa hawaye wani na bin wani a kumatunta "zan rarrasheka amma sai na san mene ne matsalar"

Bashi da zabi da ya wuce sanar da ita abin da ya sami Qareeba saboda baya so ta koma cikin gida kowa ya gane tayi kuka. Sai dai kafin ya gama labarin Mawadda tayi kuka har ta godewa Allah. Shima dauriya ce da rashin son nuna gazawarsa a gabanta tasa ya rike nasa hawayen.

"Ban taba ganin dabbanci irin wannan ba. Ba kasarmu ba duniya gabadaya tayi sake wurin karuwar fyade yanzu ya wuce kan 'yan mata harda yara kanana. Ke da ki ka taba fuskantar wannan abin zaki fini fahimtar halin da Anti Qareeba take ciki."

Kanta kawai take iya kadawa ta kasa cewa komai.

"Bakincikina ba akanta kawai ya tsaya ba. Ina tausayin duk wata mace babba ko karama, budurwa ko me aure da marasa imani cikinmu suke tozartawa ta hanyar yi musu fyade. Ina takaici idan na tuna ranar da hakan ta sameki karshenta bacci nake yi ko cin abinci. I was not there for you Mawadda ba haka naso ba."

"Ba laifinka bane"
Chapter 38 · 0% Book details