← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 68

Sashe 2

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wurin shadaya ta gama aikinta na safe har tayi wanka tana shafa mai taji 'yar wayarta na kara. Ta dauko kafin ta dauka duk da rashin boko yau da gobe ta gane sunan Baban Mawadda a wayarta saboda da ita Mawadda take kira su gaisa. Zuwanta Bebeji gidan surukanta kuma kawunta kwanaki da akayiwa autanta kaciya har Tariwa taje aka sanar da ita Mawadda tana Kaduna aiki. Bata ji haushi ba don tasan ba kiyayya bace tasa aka turata. Duka 'ya'yan Yaya dake dakin aure sunyi kafin a aurar dasu. Yadda tasan zafin nema bata so 'yarta ta zama mai matacciyar zuciya ba. Indai zata sami gidan mutanen kirki babu matsala. Aikin da sukeyi ba kwadayi ke kaisu ba sai neman halak kuma kowa da inda Allah Ya rubuta masa abincinsa. Yanzu da taga wayar a zatonta Mawadda ta koma gida ne tunda biki ya gabato.

Da sallama ta dauka sai taji muryar dan uwanta tsohon masoyinta Fatihu. Gaishe shi tayi ya amsa muryarsa a karye alamun damuwa.

"Sa'ade do Allah idan zai yiwu kizo gida cikin satin nan"

Zuciyarta ta harba a take hankalinta ya tashi tasan ba lafiya ba.
"Ita wannan din ina take?" Ta fada a sanyaye.

Sarai ya gane wa take nufi tunda bata fadin sunan Mawadda. Kallonta yayi dukunkune a jikin Yaya tana ta rawar dari. Asibiti zasu je dama saboda zazzabin tun jiya yaki sauka ga sambatu tanayi ko yaya taji sauti mai dan kara ta rinka buge-buge kenan tana neman agaji.

"Bata da lafiya ne yanzu ma asibiti zamu je." Ya amsa a raunane.

Mawadda daga kwance da ta fuskanci da wa ake wayar cikin kuka ta fara cewa "Ade kiyi min addu'a ji nake kamar zai biyoni. Kamar mutuwa zanyi"

Da sauri Baba ya bar dakin sai dai Ade ta riga taji. Kuka ta saka masa tana rokonsa ya fada mata wane irin ciwo ne yace sai tazo. Bai bari ma ta gama magana ba ya katse kiran shima damuwa da bakinciki suna kara baibaye shi.

Ade kuwa da kuka ta fita daga dakinsu hankalinta a tashe sosai. Cikin gidan ta nufa 'yan uwanta masu aiki sunata tambayar ko lafiya ta kasa amsawa. Tana shiga falo tayi sa'a Sakina ta fito cin abinci. Har gaban tebur din taje ta durkusa daga gefe tana sharar kwalla.

"Umman Abbati don Allah ina son tafiya gida. Yanzu baban Mawadda ya kirani bata da lafiya sosai" kuka ne ma yaci karfinta ta kasa bayanin yadda taji muryarta.

Cikin halin ko in kula Sakina tace "Tohhh wace Mawadda kuma?"

Tsabar tashin hankali yau har sunan 'yar ta fada ashe.
" 'Yata da nace miki zatayi aure jiya"

Dariya sosai Sakina tayi tana kada kai ta mike tsaye tana salati "Amma Ade kin raina min hankali. Jiya wato don nace kwana shida na baki na zuwa bikin shine zaki ce bata da lafiya. Nufinki na barki ki tafi ni da ganinki sai an gama biki sai kiji dadin cewa jinya kika tsaya ko"

Ade ta bude baki tana kallonta kafin ta daure tace "idan baki yarda ba ga wayar ki duba da kansa ya kirani duk da bama waya. Yarinyar nan cewa take nayi mata addu'a mutu....wai mutuwa zatayi" sai sautin kukanta ya karu.

Kankance ido Sakina tayi ga masu aikin gidan suna saurarensu.
"Nafi karfin ki kawo min shirme irin wannan na yarda. Idan lokacin da na baki ne yayi kadan kije zan kara miki ya koma kwana goma ince ko ya isa"

Kan Ade har sarawa yake ba don fargabar halin da 'yarta ke ciki ba yanzu sai tsabar wulakancin uwardakinta. Wai shin duk abinda ya shafi rayuwar masu aiki ba shi da mahimmanci? Su ba mutane bane kamar kowa. Basu isa su kawo uzuri ba sai a nemi bin diddigi saboda kawai an rainasu? Da wata mai fada ajin ce tana kawo uzurinta za'a karba kila har a bita garin nasu don neman suna. Iyakar bacin rai tana jinsa a wannan lokacin.

" 'Yata ta cikina zan yiwa sharrin ciwo don ina son zuwa gida? Ba ni na kawo kaina ba har sai nayi haka idan tafiya nake son yi?"

"To wa ya sani ne? Ku maganarku ai ba abar yarda bace. Daga magana dake jiya yau zance ya sauya"

Juyawa tayi zata koma daki ta hada kayanta ta tafi Sakina ta dakatar da ita.

"Idan kika tafi kada ki dawo don a satin nan zan nemi wata"

Ade ta share hawaye "To Allah Ya baki daidai dake. Idan nayi miki wani abu saboda yanayi na zaman tare ki yafe min. Na barku lafiya."

Fita tayi Sakina tana jin kamar tace ta dawo amma har ranta gani take kawai karya take yi. Sai da ta tattaro kamai nata ta dawo falon tayi sa'a tana nan

Tace "Albashina nazo karba na watan nan zan wuce"

Sakina ta tafa hannu "wannan kuma kinyi kadan wata bai kare ba"

Ba tsoro a zuciyar Ade bare kara tunda tayi a baya ansa kafa an shure.
"Yau kwananmu goma sha tara da karbar wancan albashin. Na iya kwanakin da nayi aiki zaki bani"

Mai shararsu Sakina ta nuna da yatsa tace ya kira mata sikuriti tana ganin Ade abin nata harda wulakanci kuma.

Jakarta ta gyarawa zama dama sauran manyan suna bakin kofa guda biyu "basai an kirasu ba zan tafi. Amma ina so ki sani ba kullum ake kwana a gado ba. Zabin Allah ne ya kawoki nan ba iyawarki ko dabara ba. Hakkina kuma ki rike zan karba ranar da baki da kudin biyana."

Tana kaiwa nan ta fita sauran masu aiki suna biye da ita wasu na bata hakuri wasu na mata fatan alkhairi. Godiya tayi musu ta sabi kayanta tayi waje.

Har ta isa tasha tana mamakin hali na wasu masu kudin. Indai haka kudi yake sa zuciya ta bushe daga tausayin na kasa bata fatan samun wannan arzikin. Arziki irin wanda zai sa wani ko wata ta tafi da ita a rai kwatankwacin yadda ta tafi da Sakina tana mai jin zafi tare da neman sakayyar Allah akan yanayin zaman da sukayi.
******

Lokaci yana ta tafiya har uku da rabi kanin Baba da yake da akori kura ta daukar itace bai iso ba. Gudun tonon silili Baban ya nemi alfarmar ya kaisu asibiti yace dama yana hanyar zuwa garin yau. To gashi nan shiru har yanzu. Shima yana can ashe duk ya damu sai dai babu yadda ya iya yana jiran cikon kudinsa daga wurin wanda ya kaiwa iccen. Da kudin zaisa mai a tsohuwar akori kurarsa sannan ya hadowa iyalinsa cefane. Tun safe yake gidan ance maigidan bai tashi daga bacci ba shine fa yake ta jira. Daga karshe hakuri ya kira dan uwansa ya bashi saboda bashi da halin tahowa a ranar. Ya kuma san tunda Mal Fatihu ya nemi alfarma lallai ciwon Mawadda ba na wasa bane.

Tun kafin ya gama bayani Baba yaji idonsa yana neman tara kwalla. Daga zuwan Mawadda zuwa yanzu kwana biyu kacal bai san adadin hawayen da ya zubar ba. Bakincikin halin da suka tsinci kansu yake yi saboda talauci. Yau da shi wani ne da tuni 'yarsa tana asibiti ana bata kyakkyawar kulawa shi kuma yana can ofishin 'yan sanda tare da dan iskan da yayi mata fyade fada sai inda karfinsa ya kare. Yanzu kuwa samun lafiyarta kadai ne a gabansa. Tsoronsa bai wuce firgicin da take yawan shiga ba da sambatu.

Har kofar gidansa achaba ya ajiye Ade da kayanta niki-niki. Tana ta adduar samunsu basu riga sunje asibiti ba. Kafin ta gama sauka Baba ya fito yana ganinta gabansa ya fadi. Baiyi zaton zata zo yau ba. Yanzu me zaice mata? Jikinta a sabule ganin yanayinsa itama ta tambaye shi ko sunje asibitin.

Har wani kwarjini tayi masa na dole da kyar ya iya cewa mota ce babu. Ainihin abinda ya hana samuwar motar garesu dama bai wuce yana gudun fita titi nemanta ba. Yasan duk wanda ya ga ya kawo mota kofar gidansa zai sha tambayoyi. Kauye kuma da bin kwaf baza'a dade ba yasan gaskiya zata fito a tsangwami 'yarsa.

Dan acaban Ade ta roka akan zata biya shi ya samo musu mota a bakin titi. A ranta tana cewa abinda zai hana Malam zuwa neman mota da kansa saboda lafiyar 'yarsa ba kadan bane.

Shi ya tayata daukar kayan ta shige gaba na dukan uku-uku. Tana sallama Mawadda ta fito tsakar gidan kamar an wurgota ta rungume Ade. Yau dai babu kunyar 'yar fari saboda yadda ta ganta ta fige fuskar nan kamar ba tata ba don ma ta fara sabewa.

Yaya ta fito suka gaisa a mutumce tana shimfida mata tarbarma don yaran duk sun tafi makarantar allo. Yaya kunya ta kamata rashin sanin me zata fadawa Ade. Ita kaddarar sai akan 'yar amana ta fada duniya zaginta zatayi kawai ace sakaci ne don ba 'yarta bace. Nata yaran babu wadda tayi aiki a gida irin wannan sai 'yar kishiya.

Ade tana ta rarrashin Mawadda tana kuma son tambayar me yake damunta amma ta kula daga Malam har Yaya babu wanda yake son mata bayani. Ba jimawa Baba ya shigo yace su fito mota tazo.

Duka su ukun suka fito dama Yaya ta fadawa sauran yaran idan sun dawo gidan babu kowa su tafi gidan kakaninsu. Tashin motar sai yayi daidai da zuwan Dahiru da leda a hannunsa ta kayan dubiya. Ya tabbatar su Baba ne a motar hankalinsa duk ya tashi ko jikin Mawadda ne. Yayi sa'a dan acabar bai tafi ba ya tambayeshi ina zasu je yace yaji kamar suna cewa asibitin Bebeji.

Bai tsaya wata-wata ba ya koma gida ya sanar da iyayensa. Inna har tausayi ya bata don tasan irin so da shakuwar dake tsakaninsa da Mawadda. Abinda zai baka mamaki shine duk son da suke yiwa juna idan an zauna hirar fa bata wuce yaya mutan gida, ya karatu lokacin tana zuwa makarantar allo da ta dare, ya aikin gonar da yake yi da 'yan buga bugarsa tsakanin Tariwa da Bebeji. Daga nan sai dai idan an hada ido yayi murmushi ita kuma ta sunkuyar da kai.
Chapter 2 · 0% Book details