← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 68

Sashe 11

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bilki, Hasiya, Nana da Jamila sune manyan 'ya'yan Yaya da ke dakunan mazajensu. Ga mamakin iyayen suna shiga gida suka samesu duka su hudun. Jamila ita ce sakuwar Mawadda kuma babbar aminiyarta don ba karamar shakuwa bace tsakaninsu. Sirrin da basa iya fadawa kowa a waje suna yi da juna. Da kuka ta tari Yaya tace tun la'asar suka zo dukkansu labari ya riskesu gashi sun je gidan Malam wato kakansu babu kowa. Kannensu kuma suna makaranta lokacin shiyasa basu san a wane asibitin aka kwantar da Mawadda ba.

Daga Yaya har Baba hankalinsu ba karamin tashi yayi ba. A ina suka ji har suka taho duka su hudun. Biyu ne ma a Tariwa wato Bilki da Jamila. Hasiya da Nana kauyukan da suke aure suna makotaka da Tariwan ne.

Zama suka yi Yaya ta basu labarin komai. Sunyi kuka kamar me suna takaicin dare yayi da a lokacin zasu tafi asibitin.

Kafin Baba ya tambayi inda suka ji wannan labari sai yaji sallama. Shi yanzu gabansa har faduwa yake yi idan yaji ana sallama dashi.

Haka nan ya tashi ya fita. Makocinsa ne da suka hada katanga. Musabaha suka fara yi sannan yace "Mal Fatihu haka ake zaman tare kuma abu irin wannan ya faru ba don gidan Mal Isiyaku ba ashe da bazan sani ba."

Wani irin sanyi ne ya soma ratsa Baba na tsananin shiga damuwa. Suna can asibiti ashe kowa ya gama sanin me suke boyewa. Kuma a rasa daga ina magana zata fito sai daga bangaren wanda yake tunanin ko yaya zasu rufa musu asiri. Shikenan tasu ta same su a garin nan. Basu da sauran mutumci kuma sai yadda hali ya yiwu.

A hankali ya iya cewa "kayi hakuri hankali na ne ba a kwance ba domin dawowata kenan ma gidan"

"Eh ai na kula shiyasa nayi saurin kiran sauran abokan arziki don duka fa mun damu. Wunin yau sur maza da mata zuwa muke ta yi gidan nan babu kowa."

"Mungode bari na shiga ciki kaina ke ciwo sosai" bai jira amsarsa ba ya koma ciki.

A nan ya sami Yaya tana kuka tana sanar dashi basu da sauran sirri an gama tozarta su a garin nan.

Da wannan damuwar gidan Baffa da na Baba suka kwana kowa da abin da ya dame shi.

Da safe da wuri suka shirya da su Bilki , masu goyo suka kintsa yaransu suka fita. Baba yaso ganawa da Baffa amma a yadda ransa ya baci yasan za'ayi batacciya ne kawai.

Fitar su Baba ke da wuya Baffa ya karaso gidan. Da ga waje wasu mutum biyu suka sanar dashi yanzu suka tafi bakin titi da iyalinsa zasu tafi asibiti. Abin duniya ya ishi Baffa ya juya gida jiki a sanyaye.

Nanatawa yake a ransa Ummiyo bata kyauta masa ba. Babu abin da ya kai kima da mutumci a wurin babba gashi ta zubar masa da nasa da kaikayin baki.

Bayan ya koma ba dadewa Dahiru ya shiga rumfarsa yi musu sallama shi da Inna. Idan ya sami yadda yake so baya sa ran wuce sati daya. Sun bi shi da addua da fatan alkhairi ya sabi jakarsa ta viva yayi waje.

*****
Su Baba sun isa asibiti suka samu 'yan sandan nan sun dawo kamar yadda suka yi alkawari. Mawadda na kuka Iya ta tursasata akan ta bude ciwukan jikinta kamar yadda mai hoton ya bukata domin a dauki shaida. Wannan wane irin tozarci ne BB ya janyo mata. Likitan da ya duba ta shine ya fadi wuraren da ya ga ciwo kamar shatin belt a bayanta, cinya da kuma fuskarta da bata gama daidaituwa ba. Da suka fita haka 'yan uwanta suka zagayeta suna ta koke-koke. A wannan halin Iya ta fice sadaf-sadaf ba tare da sun kula ba ta bi bayan Likitan.

Ko zama baiyi ba ta shigo tare da rufe kofa. A hankali cikin sigar rada ta soma magana tana kuma yi masa alama da kada ya daga murya shima.

"Dan nan ka fada min gaskiya ka tabbatar Mawadda ba wai haihuwa ce tayi ba fyade ne kawai"

"Me zai sa kiyi tunanin haihuwa tayi? Jikarki budurwa ce da tsautsayi ya afka mata"

Sake rage murya Iya tayi sannan ta fiddo zanin Mawadda da ta dauka da sunan za ta wanke "Likita ka taimaka ka duba min ita sosai. Tun jiya na kula idan ta jima a zaune ta tashi wurin sai yayi lema. Yau dai na dauki zanin sansana ka ji.."

Saurin kawar da kansa yayi ganin da gaske Iya tura masa zata yi a gaban fuskarsa.

Ko a jikinta yadda yayi ta sake juya zanin "nayi zaton haihuwa kadai ke kawo yoyon fitsari"

Ba arziki Likita ya tashi "yoyo kuma? Kai muje dai na sake dubawa"

Tare suka fita Iya tana biye dashi har dakin. Nos ya kira ya bukaci kowa ya fita da ga shi sai Mawadda da Nos din ya kalleta cike da tausayawa. Yarinya karama tana ta fuskantar matsaloli da kuruciya.

"Malama Mawadda dubaki zan sake yi"

Kukan nata ma ya kafe sai zafin zuciya. Tunda tazo ake bankada mata jiki ko ta ina. Wannan kadai ya isheta bakinciki. Ba musu ta kwanta inda yana daga gefe ya umarci Nos din da ta duba masa ita ko akwai danshi a tare da ita.

Gabanta ne ya fadi jin furucinsa. Tabbas kwana biyu bayan faruwar al'amarin nan gareta ta tsinci kanta da digar fitsari wanda bata iya rike shi idan yaso fita. Ko kwakkwaran motsi tayi sai taji alamunsa batare da kuma tana cikin matsuwar fitsarin ba. Tayi iya kokarinta wurin ganin tana rike shi kamar da amma abin yaci tura. Gashi bata sanar da kowa ba ta yaya aka gane?

Dubawar farko Nos din ta tabbatar masa da abin da suka zo nema. Hakan yayi matukar daure masa kai yayi 'yan rubuce-rubuce bayan Mawadda ta amsa tambayoyin da ya yi mata sannan ya fita.

Kusan awa uku a tsakani ya turo aka kira masa Baba. A lokacin dama suna sanar da su Iya maganar da ta bullo a gida kusan kowa ya san sirrin da suke boyewa a dalilin fitar maganar daga gidan Mal.Iskiyaku. Suna kuka suna bawa juna hakuri ya fita ya barsu.

Kasan babbar rigarsa yasa ya goge hawayen da yake barazanar zubo masa sannan ya shiga karamin ofishin likitan.

Waya ya ajiye ya dubi Baba cikin damuwa
"Baban Mawadda kayi hakuri da abin da zan fada maka"

Cikin Baba ya nemi kullewa a firgice. Me kuma ya faru yanzu.

"Ina jinka Likita"

"Bayan dan bincike da nayi da kuma amsoshin da Mawadda ta bani ina zargin ta kamu da lalurar rashin rike fitsari saboda raunin da jijiyoyinta suka samu har karfinsu ya ragu"

"Nufinka dai yoyon fitsari ta kamu dashi?"

"Eh... to! Ba na ce ba saboda abu ne da sai anyi dogon bincike da gwaje-gwaje. A takaice dai Baba yarinyar nan sai kun sauya mata asibiti. Ku kaita cikin Kano asibitin Malam Aminu Kano ko kuma asibitin Murtala. Mu nan bamu da kayan aiki sosai kuma rashin bata kulawa da wuri kan iya haifar mata da babbar matsala a gaba"

"To nagode" Baba ya iya cewa ya mike jiri na dibarsa. Banda fyade da ciwukan da aka ji mata saboda duka harda yoyon fitsari kuma. Ina zai saka kansa? Ina yake da kudin kaita asibiti a Kano?

Da wannan tunanin ya koma wurin iyalinsa. Bilki ce take tilastawa Mawadda cin abinci Iya tana basu labarin yadda suka yi akan kunu jiya da Dahiru.

" Idan taki ci ku aika a kirawo shi ku ga cin abinci da neman kari"

Dariya sauran sukayi ita kuwa sai murmushin kunya. Da Baba ya shigo kiran Yaya, Ade da kuma Iya yayi waje domin sanar dasu sakon likita.

Yaya da Ade suka soma salati Ade tana matsalar kwalla. Iya bata yi mamaki ba domin tayi zargin haka tun da ta kula da danshin take bari a wuri idan ta tashi.

"Ku koma ciki ba kuka zaku yi ba Allah zai kawo mana mafita" Baba yace yana juya musu baya saboda yadda zuciyarsa take neman gaza daukar wannan bakon lamari.

"A'a Fatihu gara mu san me muke ciki tun wuri tunda Likitan ma haka ya bada shawara. Ke Ade ina so ki saurareni da kyau. Gidan da kike aiki zaki samu ki koma ko gobe ne ki sanar da matar matsalar da ake ciki ko zasu ranta miki kudin ko da ba kyauta ba."

Tana maganar Ade ta soma girgiza kai "gaskiya bazani ba Iya"

Duka Iya ta kai mata a kafada "ji min sakarci fa. Kina so kice min kinfi karfin rokon taimako ne ko me? Indai baka dashi to ka yarda baka dashi din ka nema a wurin wanda ya fika. Kice rance ba kyauta ai dai bashi hanji ne a cikin kowa"

Hayaniyar yaran nasu ce ta fara yawa daga dakin Yaya sai ta fake da zata tsawatar musu ta basu wuri. Batah jiran karin bayani tasan suna bukatar kebewa don a shawarta yadda za'ayi.

Bayan ta shige Iya ta murmusa tana binta da kallo "Wallahi Fatihu matarka ba dai sanin ya kamata ba."

Yau wace rana Iya ta yabi Yaya.

Shiru yayi bai ce komai ba sai tunani da yake yi ta ina zai sami kudi shi ba wata kadara ba balle ya sayar.

Iya ta sami wuri akan wani benci ta zauna tana kallonsu duk hankalinsu a tashe.

"Duk wani so da zamu nunawa 'ya'ya fa ya bi bayan jajircewa wurin nema musu lafiya. Kyautatawar da muka yi muku da kuruciya ita take janyo jin kai tsakanin mu daku idan mun girma. Yanzu meye naki na cewa bazaki je ki ranci kudi a wurin matar da kike yiwa aiki ba? Mutum me da har yana da wani sauran jiji da kai ne idan bashi da kudin kulawa da dansa? Kwantar da kai ake yi gaban masu kudi idan kina son jindadin zama dasu"

Cikin kuka Ade ta labarta musu yadda suka rabu da Sakina. Hatta Baba ransa ya baci balle Iya. Sun jajantawa juna yadda masu kudi basu dauki hakkin talaka a bakin komai ba.
Chapter 11 · 0% Book details