← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 68

Sashe 52

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna tafe suna taba hira a tsakaninsu mazan don Mawadda da Nawal kowacce ta fada duniyar tunani da fargabar sabuwar rayuwar da zasu tunkara a yau.

Yaya ce ta kira Dahiru da wayar Saifullahi tace Marwanu zai kai musu abinci daga gidan Rafi'a kada su saka matansu girki. Godiya yayi mata ta sake tambayarsa yaya 'yarta babu matsala ko.

Murmushi yayi yace babu ko ya bata ne sai taji kunya tace a'a. Ba'a dade ba sai Ade ma ta kira itama dai so take taji yaya Mawadda take ya maimaita mata yadda suka yi da Yaya a kunyace ta ajiye wayar da yace zai bata itama.

Murmushi yayi yadda suke son 'yar tasu ya burge shi da irin zaman amanar dake tsakaninsu kamar ba kishiyoyi ba.

Layin gidan nasu kusan duka sababbin gidaje ne harda titi har kofar gidan. Dakin maigadi dai babu kowa Dahiru ne ya bude Attahir ya shigo. Wurin ajiye mota zai ci motoci hudu ma ga borehole da katon tanki a jikin katanga daga karshen gidan.

Gidan nasu tun daga waje yayi kyau. Kofa ce daga can karshe a kasa ta karfe wadda ta nan bene ne kawai zuwa saman inda su Dahiru zasu zauna.

Suna fitowa kowacce ciki ya duri ruwa sai rabewa suke a gefe. Attahir yace " 'yar uwarmu Allah Ya bamu alkhairi bari mu shiga ciki"

Kanta a kasa tace "to mungode Allah Ya saka da alkhairi"

Nawal ta kalleta kamar tayi kuka ganin yadda mijin nata yake ta rawar kai duk ta firgice. To itama Mawaddan dauriya ce kawai ta kalleta tayi murmushin dole.

Dahiru ya kama hannun Attahir "Dan uwa Allah Ya saka da alkhairi"

"Ka ji ka da wani zance sai da safe kaji"

"Sauran sallolin yau an yafe maka jam'i ne?" Dahiru ya amsa yana tsokanarsa sannan kowa yayi gaba matarsa tana biye dashi.

*****

Da sallama ta shiga gidan wani hadadden kamshin turaren wuta ya ziyarci hancinta. Duka turarukanta hatta humra da kanta ta hada saboda yanzu ta gama kwarewa. Kullum jikinta cikin sassanyan kamshi yake yau da gobe sana'arta ta janyo hakan balle kuma tana amaryarta guda.

Katon falon nasu suka shiga wanda aka kawata da kayan alatu na zamani. Daga gefen inda kofar kitchen take harda dinning table da kitchen cabinet. Kalle kallen dai ba yau ba ta samu wuri akan kujerar mutum daya ta zauna a takure.

Kujerar gefenta Dahiru ya zauna ya mika hannu ya riko hannunta daya. Jikinta taji yayi sanyi fiye da yadda taji dazu da suka hadu ko don lokacin tana tattare da fargaba ne.

"Mawaddatan wa Rahma yau gaki a gidan Dahiru a matsayin matarsa. Babban burina ya cika ina fata zamu zauna lafiya mu rike juna tsakani da Allah"

Kanta a kasa tace "In sha Allah."

Irin kararrawar nan mai sallama ce ta doka sallama a falon. Daga wajen kofar hawa saman Dahiru ya saka saboda kada a buga basu ji ba idan kofar saman a rufe take. Mike yayi yace mata yana zuwa. Fita ta ga yayi bai dade ba ya dawo rike da kwandon abinci.

"Marwanu ne ya kawo"

Hannunsa na dama ta kalla har yanzu da kumburi ga dukkan alamu yana masa ciwo ta tashi ta karbi kwandon ta ajiye a kan dinning table.

Har lokacin yana tsaye "bari na nemo plates to tunda kin karasa min wannan ladan"

"A'a barshi zan duba" tace tana dan waige. Plates ne masu kyau da cokula, kofuna da jugs a cikin kitchen cabinet din da yake manne a bango daga bayan table din komai a jere yadda ya kamata. Budewa tayi ta dauko plates biyu, da sauran kayan bukata ta ajiye.

Gani tayi ya ja kujera daya ya zauna tace "in zuba maka?"

Ya tsareta da ido ganin jikinta ya soma rawa amma tana ta kokarin boye masa "ki zuba mana dai"

"Na'am?" Tace a sanyaye tana mai fargabar kada ta fara wannan abin don tunda ya tsayaba wurin table din taji zuciyarta ta tsinke.

"Kinji me nace ko yau ma kurumtar ce ta tashi?"

Cije lebenta tayi tana karfafawa kanta gwiwar kada ta tsorata yaji babu dadi shi kuma ya kawar da kansa yana mai tuna maganar da Inna tayi masa jiya bayan daurin aure. Ita ma kuma Yaya ce ta fara yi mata bayanin yanayin da Mawadda kan shiga idan ta kebe da namiji na tsoro da firgici.

_"Dahiru kai ba bako bane game da sanin wacece Mawadda. 'Yar shawara zan baka ka sani cewa soyayya daban sha'awa daban. Duk son da take yi maka kasan kaddarar da ta afka mata a baya har yanzu tana iya tasiri a kanta. Idan kana son samun nutsuwa da kwanciyar hankali a gidanka ka fara neman kusanci da yarda daga matarka kafin ka bijiro mata da wani abu daban. Ina fata ka fahimceni. Idan kaje mata lokaci guda tana iya alakanta hakan da wannan lamari na baya ku zo kuna samun sabani"_

Wannan sune kalaman Inna gareshi kafin ya baro Tariwa. Ya gamsu da su dari bisa dari ya kuma san cewa hakan shine zai sanya shakuwa a tsakaninsu.

A plate daya ta zuba musu abincin dayan kuma ta zuba soyayyan naman kaza.

Kallonta yayi ya sake kallon abincin "kin tabbata zai ishemu? Ina jin yunwa sosai"

Bata ce komai ba ta kara musu. Tana gamawa ya sake hada komai a cikin kwandon "bari na kaiwa su Attahir"

Jin haka tayi murmushi saboda tayi wannan tunanin sai dai kuma tsoron kada ya zama kaiwar akwai takura.

Inda ya barta ya dawo ya sameta. Kujera yaja ya zauna sannan yace ta zauna ganin ta tana tsaye har lokacin.

"Matarmu kinsan me nake so dake?"

Ta girgiza kai a hankali tana jin alamun hawaye mara dalili.

"Don Allahi ki cire komai a ranki ki saki jikinki. Ban aureki domin na takura ki ba duk da nasan cewa da wahala idan kowacce amarya ba haka take yi ba. Amma kinga mu special case ne."

Yadda yake daga gira yasa ta murmushi tace "kamar yaya?"

"Kinga dai ke da rana tsaka kika tare, gashi ango ya shigo ko kullin kazar al'ada babu. Sannan kin shigo gidanki babu irin kwalliyar nan ko inji kamshiki tun daga kasa"

Kallon kayanta tayi mayafin duk ya yamutse shi kuma ya nuna mata fuskarta a jikin wayarsa ta kode idanu zuru-zuru. Ita kanta ta bawa kanta dariya wai amarya kenan.

Turbune fuska tayi cikin shagwaba "ai kasan me ya janyo hakan"

"Na sani shiyasa nace miki komai namu daban ne. Saboda haka nake so daga yau har ranar da tayi miki ki dauke ni a matsayin yayanki, kaninki ko abokinki. Duk wanda kike so ki zaba. Ni kuma zan jira ki zuwa lokacin da kanki zaki dawo dani miji."

Sunkuyar da kai tayi ya ga hawaye ya diga akan tafin hannunta.

"Kina so muyi fada ne?"

"A'a"

"Na soke kuka a gidan nan daga yau. Idan kika kuskura na kamaki kina kuka zaki sha mamakin abinda zanyi"

Goge hawayen tayi ya taso ya dagota tsaye sannan ya rabata da jikinsa ya daga waya "hoton tarihi zanyi mana"

Hannu biyu tasa ta rufe fuskarta "naki wayon wallahi bazanyi kyau ba"

"Zakiyi mana" yace yana ta daukarsu tana kaucewa har ya sami wanda duka su biyun suke dariya.

Zama suka yi cin abincin ya dauki cokali da hannun hagu yana satar kallonta "ni gashi hannun daman yana ciwo, hagun kuma ban wani iya amfani dashi sosai ba"

Sam bata kawo me yake son yi ba tace "daurewa zakayi Yayanmu nasan kana jin yunwa"

Marairaicewa yayi "sosai ma amma kinsan Annabi SAW yayi hani da cin abinci da hannun hagu"

Ajiye cokalin da ta rike tayi ta dago kai "lalura ta kori komai Yayanmu"

"Haka ne amma kinsan lalura shine idan babu yadda zakayi gabadaya. Ni kuma a misali kinga ina tare dake"

Dariya ta shiga yi ta gano me yake nufi "daga zuwana gidan nan ko awa daya banyi ba zaka bani aiki?"

"Wane ni? Wai dama ina tunanin ko a matsayin yayata ki dauki kanki sai ki daure ki bani. Kinsan idan nace kanwata kanne akwai tsiwa kila ki rinka bani ba yadda nake so ba. Amma yayye mata akwai kirki"

Da fargaba Mawadda ta shigo gidan amma yanzu Dahiru yasa ta soma sakewa batare da ta ankara ba.

Roko da magiya harda cewa zai fasa cin abincin yayi a dole ta amince zata bashi. Lomar farko sai da ta rufe ido saura kiris ta tura masa a hanci ya riko hannun. A haka dai aka ci abincin sai da ya koshi ya tashi sannan ta iya ci don ko loma daya ta kasa yi a gabansa.

******

Motsinsa take ta ji a kitchen da ya shiga bayan ya gama cin abincin. Bai fito ba har sai da ta gama sai gashi yana wani sunkuyar da kai.

"Uhmm ruwan zafi ne babu na wanka amma na kunna miki heater. Ni kuma sai na dora a kitchen saboda kada na makara sallah"

"To" ta amsa masa tana dukar da kai.

Sai da yayi murmushi sannan yace "baki fahimceni ba, ruwan yayi zafi amma kinsan saboda hannuna bazan iya saukewa na kai toilet ba"

Ji tayi kamar ta shige kasa saboda kunya maganar take bata. Dahiru kuma yasan idan yana mata haka bazai bata damar tsawaita tunani akan abubuwan da suka faru ba balle ta shiga damuwa.

Ya sake kallonta yana shagwabe fuska "in dauko bokitin ki juye min?"

Kafin ya motsa ta tafi hanyar dakunan. Na farkon ta shiga ta ga babu toilet ciki amma tasan ta ga wani a falo. Sai ta bude dayan dakin. Yana da girma yayi matukar kyau da kayan da aka jera mata. Kamar yadda ta zata akwai bandaki a ciki ta shiga ta dauko bokitin a ranta tana ta tunanin wai haka ake yiwa amare ko kuwa dai ita ce daban. Ita fa duk labaran da take ji ranar da aka kai amarya tamkar sarauniya take komawa don mulki. To ita me yasa Dahiru yake yi mata haka? Babu amsa tunda bazata iya tambayarsa ba.

Ruwan ta juye ta kai masa ta ajiye yace mata za ta iya jira na heatar bandakin yayi zafi saboda akwai wuta. Kuma wai yana gama fada sai ya fara sosa kai.
Chapter 52 · 0% Book details