← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 68

Sashe 64

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har zuciya maganar ta daki Mawadda. Ta dade da yafe mata ko ince bata taba daukar abin a rai ba ko don albarkacin Dahiru tun a wancan lokacin. Idanun iyayensu ya sanya mata jin nauyi ta rungume Ummiyo ta barin jikinta "komai ya wuce Ummiyo don Allah kada a sake tada zancen nan."

Sai yanzu Ummiyo ta iya murmushi tun fitowarsu daga gida. Bilya ne ya daukosu a tasha don shi niyarsa yaje da kansa ko Danlami su daukosu sai wayar Baffa ya samu wai sun kusa shigowa gari. Shine yaje ya daukosu ko wanka baiyi ba. Yana kawosu ya koma gida batare da ya shigo ba.

Sai da Dahiru ya kula hankalin iyayen ya koma ga Ummiyo da Mawadda suna ta murmushin wannan shiryawa tasu.

"Wallahi Allah Innarmu ba haka ake yi ba" yace yana kankance ido fuskarsa na nuna alamun fushi yake.

Inna ta ware idanu tana masa kallon tambaya "me aka yi ba daidai ba?"

"Jiyan nan mota ta kwasheni ta wulwulani a sama sannan na fado na hadu da gaban mota da zafin kwalta" yana magana yana kwantatawa da hannu "amma shine kun shigo kawai kun biyewa waddan" ya nuna Mawadda da Ummiyo.

"Yanzu kai kishi kake da matarka da kanwarka? Wannan abin kunya da yawa yake" cewar Baffa.

Inna ta zauna a kusa dashi "da gaskiyarka Dahiru babu wani abin kunya. Ya ya jikin"

Saitin Mawadda ya kalla yana harararta "da sauki"

Baffa yace "abin naka harda jin baki."

"Ba fa kace min ya jikin ba har yanzu"

Duka dariya suka yi sai kuma hira ta barke tsakaninsu su uku a can gefe kuma Ummiyo da Mawadda ke yi tasu tana tambayarta game da 'ya'yanta.

Basu jima ba sai ga Attahir da Nawal da abinci. Rungume juna suka yi da Mawadda tana tambayarta mai jiki bayan ta gaisa da su Inna. Suna haka Marwanu ya iso shima da kayan abinci yace su Baba zasu taho anjima. Inna da Iya sunce sai sun biyosu ga kuma su Bilki duka sun baro gidajensu shine suka yanke shawarar sai kowa ya iso zasu taho tare.

Bai dade ba ya fita saboda dakin ya cika. A bakin kofa ya hadu da Danlami da matarsa suma da kayan abinci. Yana rike da kwandon abincin ita kuma ta goya Humaira. Tuni dakin ya kaure da hayaniya. Baffa ya fita daga waje ya bar Inna da 'ya'yanta.

Wata kumbular mota mai kyau ce tayi parking Qareeba ta fito. Tayi kyau sosai don kuwa taci kwalliya saboda tasan zasu hadu da Bilya. Idan bai zo ba ma jiransa zata yi. Tun asuba taso shiga kitchen Dr Tani ta korata daki wai zumudin yayi yawa. Bacci ya sake dauketa tana farkawa ta fada kitchen ta hada girki mai dadi domin farantawa kanin miji don ta sake samun shiga wurin yayansa. Ba yadda Dr Tani bata yi ba akan ta zauna sai shabiyu ta fito taki amincewa har kuka ta kusa yi.

A cikin kwando mai kyau ta jera komai wanda kwanukan Daddynsu ta debo batare da sanin Dr Tani ba. Har zata wuce ciki daga kasan bishiyar dake gefen inda ta ajiye mota a farfajiyar asibitin ta kula da wani dattijo ya kara karamar rediyo a kunnensa. Jini baya karya kallo daya tayi masa ta san matsayinsa.

Riga da skirt ne a jikinta ta kashe dauri mayafi a kafada. Gyara mayafin tayi ta janyo shi har ka a ranta tana cewa dole ta chanja wannan dabi'ar girma ya kusa hawa kanta.

Baffa bai kula ba hankalinsa yana ga labaran da yake ji sai ganin mace yayi a gabansa ta rufe rabin fuskarta.

"Baba ina wuni? Anzo lafiya? Yaya su Mama? Ya mai jiki kuma?"

Kallonta yayi tana ta jero tambayoyi ya amsa mata ba don ya santa ba "baiwar Allah wurin Dahiru kika zo?"

Murmushi tayi cike da kunya tace eh sannan ta tashi ta tafi. Ladabinta ya burgeshi ya bita da fatan alkhairi.

Daga waje ta fara jiyo surutu kofar a bude take ta kutsa kai da sallama tana mitar sun dami kaninta da surutu baza su barshi ya ji saukin jikinsa ba.

Idonta akan Mawadda tana zuba masa abincin da Nawal ta kawo. Dankali ne aka dafa sannan taka burgeshi ta kada da kwai da nama da kayan kamshi ta soya da kauri sai farfesun kaza.

Hannu ta daga ta dakatar da ita "ga nawa abincin nasan zaiji dadinsa faten tsaki ne harda yakuwa da ugu saboda yaji dadin bakinsa. Kuma kinga basai ya tauna ba"

Sam bata kula da Inna ba tayi zaton su kadai ne a matsayinta na matar Bilya to be ta isa tayi musu gyaran kuskure. Mawadda ta tsaya kallonta ta turo mata kwandon ta karbe plate din da ta gama zuba wancan abincin. Nawal ta hade fuska tsaf rai a bace tana kallon Attahir ya kawo dauki. Tasha wahalar girkin kuma ace bazai ci ba wanda akayi dominsa.

Dahiru da Danlami sai dariya suke yadda Nawal ta hade rai itama Qareeba ta sha kunu tana kallon Mawadda "bazaki zuba bane in zuba da kaina? Bawan Allah bai ci komai ba"

Yau dai ta karewa Anti Qareeba kallo kuma har ranta taji tana sonta. Nawal ta kalla "uhmm kinga Sis in ajiye wannan sai yaci da rana?"

Kusa da Inna Nawal ta koma "Inna don Allah ba nice na fara kawowa ba"

Ita Inna bata san wacece Qareeba ba itama Qareeban lokacin ta kula da ita ta zube a kasa a gabanta cike da kunya. Dakin ya kaure da dariyar yadda tayi harda Nawal mai fushi.

Ta gaisheta a mutumce Inna tana tambayar wace ce ita Dahiru yace Anti Qareeba. Dama Mawadda na gefenta ta kuma janyo hannunta sai da tayi kasa itama a hankali tace mata "kiyi mata bayani sosai"

Bata san Mawaddan ma kunyar Inna take sosai ba ta dago ta kasa cewa komai. Kyakkyawan mintsini ta kaiwa Mawadda a dantsen hannunta taji zafi ta hau susa ta kuma fahimci sakon "Inna idan Allah Ya yarda fa Yayarmu zata zama"

Qareeba ta saki yalwataccen murmushi Inna ta kalleta ta koma kallon yaran nata da alamun tambaya. Danlami yace "Yayanmu Bilya"

Kai wannan abu yayi mata dadi don fuskarta ta nuna sai ta wayance da cewa bari taje su wuce gidansu Mawadda da Baffa dakin ya cika. Attahir ya mikawa Danlami mukullin motarsa "ka kaisu"

Qareeba tace "yanzun nan nasha mai ina da full tank gara ya dauki tawa"

Inna tace sun gode babu damuwa zasu tafi a ta Attahir. Jikinta yayi sanyi ko batayi maraba da ita ba.

"Inna nima 'yarku ce don Allah ku dauki tawa"

Sai da Inna tayi da gaske ta yarda su tafi a ta Attahir ta bi bayan su Mawadda aka raka su har mota.

*****

Sun dawo dakin suna hira Mawadda ta zuba masa faten dakin kuwa sai kamshi don yaji kayan hadi. Da zafi sosai sai ta ajiye akan fridge ta sake dukawa zata dauko kofi Furera ta shigo tana faman yatsina. A wulakance ta yiwa Dahiru ya jiki harda karin cewa ya auri wahala.

"Ace tun kafin a shafa fatiha ka gagara kwanciyar hankali ina dalili. Yanzu har an fara harin rayuwarka"

Mawadda tayi shiru tana jin zafin maganganun da Furera ta cigaba da yi. Dakin duka tsit yayi kowa yasan da wa take dama. Dahiru baya son yi mata rashin kunya a gaban su Attahir da Ummiyo sai yace da Mawadda ta bashi ruwa ya fara sha.

Jiki a sanyaye ta zuba masa ta dago ta kusa buge bowl din faten Ummiyo tayi saurin daukewa tana cewa "hankali dai Yayarmu"

Furera na kyalla ido ta hango mene a cikin bowl din ta mika hannu ta karba babu kunya.

"Faten tsaki kayan marmari bari muji..." ta ciko cokali da naman da aka yanka kananu fal a ciki ta kai baki. Dadi ya ratsata ta lumshe idanu "Allah Ya tsaga rabona da haka zaku barshi ya bushe a zubar. Mara lafiya ko don gaba Mawadda abinci kadan ake zuba musu idan sun bukaci kari a kara daga baya."

Wannan zubar da mutumci nata ya kular dasu amma Qareeba nata ran yafi na kowa baci amma tana mata kallon mara kan gado ta sassauta murya tace "Ahirin wace wannan ne?"

Bai amsa ba Bilya ya shigo. Ba karamin kyau yayi da kayan jikinsa ba kufta da wanda na wani lallausan yadi baki sai hula. Ya tsaya a waje magana dasu Baffa da zasu tafi shiyasa bai shigo da wuri ba.

Furera tana shan faten tana ganinsa tace da Mawadda "shima ki zuba masa yana sonsa sosai. Ni bani da jimirin yi ne kawai"

Kallon kallo ake a dakin yadda ta shigo hannu na dukan cinya take nuna iko akan abinda ba nata ba. Da bacin ranta suka fito da Bilya don tun dare da ya fada mata yayi zaton zata yi girkin zuwa asibitin. Da zasu fito yaga babu komai a hannunta yayi magana tace tasan zaa kai daga gidan Baba Prof da gidan su Mawadda. Rai a bace yace duk fadin Kano shine yafi cancanta da Dahiru yake da hakki akansa tunda shine babba. Duk wanda ya kai kara yayi musu. Sai tayi mirsisi abinta ta shige mota.

Qareeba tunda ta ganshi haukan matar da take tunanin 'yar uwarsu ce kawai ya dena damunta ta sunkuyar da kai bayan kowa ya gaishe shi itama ta gaishe shi.

Yaji dadin ganinta sosai kuma yadda yayi tunanin jin tsoron Furera ta sani sai abin baizo masa a haka ba.

Attahir da gayya yace "Anti Qareeba ki zuba masa mana"

Furera tana ta kalkale bowl din da cokali yana ta fitar da sautin kwal kwal ko a jikinta. Sai shine ma yace a koshe yake. Ai da kunya yazo dubiya dubiyar ma ta kaninsa ga matansu a wurin ya hau cin abinci duk da yadda ransa ya biya don da yunwa ya fito saboda bacin ran baa yiwa 'yan asibiti abinci ba. Hararar Furera yayi jin tace a kara mata "tashi mu tafi yanzun nan akace hayaniya tayi yawa a dakin zasu zo suce kowa ya tafi"

Dahiru ya kalle shi ya kalli Qareeba "Yayanmu baku gaisa da Anti Qareeba ba har zaku tafi."
Chapter 64 · 0% Book details