← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 68

Sashe 60

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunanin rayuwa da yadda abubuwa suka kasance mata take yi har dawowar Dahiru.

Rufa tayi har ka don kada ya ga hawayenta sai ya zaci bacci tayi ya shiga wanka. Da ya fito har lokacin bata bude kanta ba ya zauna a gefenta ya dan ja bargon "wannan irin rufa iska na shiga kuwa?"
Rike quilt din tayi yana ja tana ja "dama idonki biyu kina jina?"

Shiru ba amsa ya zagaya bayanta ya bude bargon.

"Ka fita ka shirya" tace tana kara rikewa.

Budeta yayi da karfi "naki." Sai kuma ya bude baki hankalinsa a tashe "...Mawadda me ya sameki? "

"Bacci nake ji sosai kawai"

Ya bata rai "wane irin bacci? Kukan me ki ke yi?"

Gabanta ne ya fadi don kuwa bazata taba fada masa ba. Tun da can surutu ba dabi'arta bane bare yanzu da iyaye suka ja mata kunne akan kai kara musamman ma ta dangin miji.

"Na fada maka bacci ne"

Ya daga murya "Me tayi miki?"

"Wa?"

"Anti Furaira. Dama tun da zasu tafi na kula baki da walwala sai na zaci gajiya ce."

Kwantar da kanta ta sake yi akan filo "nace babu komai ko karya kake so nayi maka?"

"Mawadda ba wasa nake yi ba. Ko ki fada ko na koma gidan na tambayeta da kaina, kinsan kuma zan iya"

Tashi ta ga zaiyi ta riko hannunsa da sauri. Tasan abinda ya sakata kuka zai bata masa rai shiyasa da ya zauna sai ta fada masa abinda suka ce game da labulen falon. Sai da ta gama ya riko fuskarta a cikin tafukan hannunsa.

"Shagwaba ko Matar Dahiru. Da nine ke sai nace na gidanta na fada miki a bakin rimi aka kada masa kararrawa. Amma bari idan munje gidan sai ki rama"

Murmushi tayi ganin sakayawar tayi rana.

"Hankalina ya tashi sosai nayi zaton abin yafi haka. Shima idan munje baki rama ba zan rama miki da kaina"

Kwantar da kanta yayi a kirjinsa yana shafa gashinta. Tunawa yayi da ya ajiye su a gida Hansa'u ta biyo shi bakin mota tana cewa yayi hakuri yasan halin yayarta. Ya tabbatar abin da suka fada yafi haka kuma shine dalilin da yasata kuka ya kuma sa Hansa'u bashi hakuri. Bazai turasata ta fada ba amma zai rama ita kanta Fureran ranar da komai zai tabbata yana so tasan shine yayi hadin wannan auren don ta tuna me ta yiwa matarsa.

"Kinyi bacci ne?"

Dago kai tayi a hankali dama kunya ta hanata tun dazu ko shiryawa baiyi ba yazo ya zauna.

Ya dage gira "Shine kika wani kwanta min a jiki kamar kin sami bread"

Kunya taji zata janye jikinta ya sake riketa yana fada mata kalamai masu sanyaya zuciya cikin nutsuwa ya fara nuna mata dadaddiyar soyayyar da ya jima yana dakonta.
******

Dahiru ne ya fara tashi da asuba. Mawadda tana kwance a jikinsa tana baccin wahala. Godiya yayi ga Allah da ya bashi ita domin baya nadama ko kadan da irin son da yake mata. Duk wata kulawa da soyayya da ango zai bawa amaryarsa ya bawa Mawadda. Jin nauyinsa da girmansa ne ya karu a wurinta shi kuma ya sami damar tsokanarta son rai.

Tafiyarsu Tariwa ce tasha ruwa don yace yanzu ya fara angwanci babu inda zai je ta gama nacinta ta hakura ta koma tana zumbura baki. Sai akayi sa'a Baffa ma ya kira yace su hakura da zuwan yafi son tazo bayan an gama case dinnan ta dawo garinsu da martabarta.

Suna zaune a falo ya hanata sakat duk inda ta motsa yana nan tace "yau babu inda zamu je kenan?"

"Haba Matar Dahiru a taimaka min mana. Saura kwana uku na koma aiki kuma dan lokacin nawa sai kin cinye shi a yawo?"

Har ta fitar da rai yana dawowa gida daga sallar la'asar yace ta shirya su fita.

Tunga ya kaita murna ta isheta kafin ya tsayar da motar ta kama kofa zata fita.

"Tsaya mana"

Ta dakata tana ta murmushi zata ga iyayenta kamar ta shekara basu hadu ba.

"Ba dadewa zamuyi ba saboda zamuje siyan wayarki."

"Yayanmu nagode" tace tana murmushi

"Rike godiyarki sai mun koma gida a gidan ma a daki, a dakin ma kuma..."

Hannu tasa ta toshe kunnenta ta fita tana dariya. Tare suka shiga gidan zo ku ga murna wurin su Yaya. Ade kam baki yaki rufuwa. Yau ga Mawadda tayi aure tayi fes da ita. Duniya bata ga dan kwarai kamar Dahiru ba. Bata fata Mawadda ta bata masa rai daidai da wuni daya. Sun sha hira Dahiru yana tare da Baba suna maganar shiga kotu.

Da zasu tafi Yaya har kofar gida ta rakota. Sai da Mawadda ta tare lafiya a gidanta ta sami nutsuwa sosai a ranta don duk shekarun nan tana baiwa kanta laifi a matsayinta na uwa gareta. Tana tsoron zargin mutane akan cewa nata 'ya'yan babu wadda ta taba fuskantar matsala makamanciyar wannan sai 'yar kishiya.

Kamar yadda yayi alkawari ita ya baiwa damar zabar waya. Ba wani sanin mai kyau tayi ba ta nemi ya tayata zabe. Waya mai kyau da tsada ya saya mata sannan suka wuce gida. Aka bude sabon shafin soyayya.
******

Barr Jibril Jibril (JJ) shine lauyan da zai karesu. Kafin Dahiru ya neme shi sai da yayi bincike sosai aka tabbatar masa da cewa yana da gaskiya da amana.

Suna zaune a ofishinsa su uku washegari yana yiwa Mawadda tambayoyi bayan ta bashi labarin komai tun daga farko. Tana yi tana kuka Dahiru ya rike hannunta ya matse "ina tare dake a kowacce gaba Mawadda, duk abinda kika san zai taimaka mana ki fada boyewar bazata amfanemu ba kuma ita ce take cutar da victims irinki"

Kai ta gyada tana kallonsa. Sun burge JJ sosai yace "anya na taba ganin masoya irinku?"

"Babu" Dahiru ya amsa masa yana murmushi "Wannan Dahirun da Mawaddansa su kadai ne"

Dariya suka yi su biyun kafin JJ yace "Mawadda asibitin da aka kaiki a Bebeji muna bukatar likitan idan zai yiwu yazo a matsayin shaida. Yaya sunansa?"

Nan fa daya ita bata san sunansa ba, kamanninsa ma ta wuya ta tuna. JJ yace babu damuwa tunda sun san a wane wata ne da shekarar zai taimaka musu wurin gano shi da sauki.

"Sai kuma 'yan sandan da suka zo suka sa hannu aka karbeki. Mal Dahiru idan mun gano su kuma munyi sa'a akwai hotunan da suka dauka akwai yiwuwar muyi amfani dasu a kotu domin samun biyan bukata"

Mawadda tayi saurin kallon Dahiru cikin tashin hankali. Idan bata manta ba harda su baya da cinyoyi inda shatin belt din BB ya fito duka an dauka. Sauran kuwa fuska ce da wuya.

Barr JJ ya kula da yanayinta "sai ta kure zamu nuna idan mun sami karancin shaidu masu gamsarwa. Fatanmu Allah Yasa su ma suna nan"

Dahiru yace babu damuwa wannan case din ba da wasa suka fara shi ba saboda haka zasu bada goyon baya yadda ya kamata.

Ta cigaba da amsa tambayoyi ta bada numbar Dr Imran a nan take Dahiru ya kira shi ta bayyana masa matsayinsa da dalilin kiran. Baya gari akayi auren shiyasa baiji labarin saceta ba. Shima dai ya amince duk bayanan da zasu tabbatar da gaskiyarta da magudin waccan shari'a zai tattara kafin a neme shi.

Mutane na karshe sune su Garwashi. Dahiru ya fada masa halin da ake ciki yace zasu zo solidarity wajibi. Abin yayi masa dadi yace idan babu damuwa yana son ganinsu washegari zai fada musu inda zasu hadu tare da barrister domin daukar nasu bayanan.

A hanya yana tuki da hannu daya dayan kuma ya rike hannun Mawadda yake fada mata yana so ta yiwa su Garwashi abinci gobe.

"Amma fa ba a gida zamu hadu ba. Ina tunanin me ya kamata nayi musu ne domin gyara rayuwarsu. Ba don su ba da bansan a wane hali muke yanzu ba."

"Yayanmu mutane da yawa sun kuntata mana a rayuwa kuma da yawa sun kyautata mana. Idan na tuna hakan sai in kara jin imani a zuciyata. Komai na Allah yana tafiya bisa tsari ne"

Gabansa yake kallo yana yi mata magana "Shiyasa karbar kaddara ga mumini yake cikin shika shikan imani. Kinga yau mun wayi gari ma'aurata sabanin wadanda da munyi aure shekara takwas da suka wuce bazamu zama haka ba. Munyi kuka mun kuma yi hakurin rashin juna cikin talauci da rashin ilimi. Yanzu kuma mun zama mallakin juna cikin rufin asiri da ilimin"

Kallonsa take cikin so da yarda "Allah Ya saka maka da dukkan alkhairi Mijin Mawadda. Babu inda zanje in kasa fadin ina sonka saboda kai abin so ne. Kaine babban arzikina a wannan duniyar. Allah Ya bani kai a aljannah"

Ya dauki lokaci maganganunta suna masa yawo a kansa ya rasa amsar da zai bata saboda tsabar farinciki.

"Allah Ya kaimu gida lafiya in baki tukwicin wannan addua"

"Ni dai na yafe bacci ma nake ji" ta kakalo hamma.

Ya rike haba "Oh yarinyar nan me kike tunanin ina nufi?"

Tuni ta dago tsokanarta zaiyi tace "ba tausar da kace zaka yi min da safe kake nufi ba? Kai me ka zata ina nufi?"

Dariya yasa "shikenan duk mu wayance kowa eya rike nasa a zuci"
******

Dahiru da Attahir suka je wurin Barr JJ a wajen office dinsa sai ga su Garwashi da mukarrabansa su Loba boy. Sunci abinci harda santi wanda aka zuba musu a pack yace sako ne daga Mawadda.

"Ayya da bata wahalar da kanta ba. Yo meye amfanin famili ne banda abinka? Mu fa yanzu mun zama surukanka tunda akwai alaka ta jini tsakanin kakaninta da matar Kawun Loba boy"

Attahir ya soma dariya "hakane dan uwa kuma gashi dole mu rinka yiwa juba solidarity"

Garwashi ya mika masa hannu suka tafa "ashe kaima duk famili dinne Allah Wallahi....to dai yanzu ya ake ciki kada fa muje daga bada shaida a rufta damu gidan maza ko kuwa gayis?"

Dahiru ya kalli JJ cike da damuwa ba zai so aikin alkhairinsu ya juye a kamasu a matsayin 'yan daba ba.

"A lokacin ba ku bashi wani information da zai cutar da ita ba. Sannan baa tuhumar ku da komai so ina ganin babu matsala in sha Allah"

******
Chapter 60 · 0% Book details