← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 68

Sashe 30

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji na zuwa ya ture Haj Mara ya janyo matarsa ya rungume.

"Sannu Yasmin babu inda ke miki ciwo? kwanta bari na dauko miki jakar kayanki."

Sakato Haj Mara tayi ganin wannan abu yarinyar da bata fi sa'ar 'yarta ta biyu ba ta wani lafe a jikinsa ga tawul dinta yana reto ya kusa faduwa sai karairaya take shi kuma duk ya gigice.

Yana juyowa marin Haj Mara yayi "idan wani abu ya sami cikin nan sai na bata miki rai. Wannan rashin hankalin na gaji da dauka. Duk da nima nasan da laifina akan kyaleki da na rinka yi amma ki sani wallahi baki fi karfina ba"

Bayan Yasmin ta shirya ya sake hadasu duka a falo. Haj Mara sai kukan zuci ta rasa me yake mata dadi.

"Kamar yadda ku ka sani shekaru takwas rabon Babawo da kasar nan. Hajiya ta tura shi kasar waje nayi nayi harda ku nasa ku tambayeta amma tana ganin kamar cutar da dan cikina nake son yi taki fada mana inda yake. To Alhamdulillah Allah Yasa nasa an nemo min shi ta hanyar binciken account din da kika rinka tura masa kudi. Duk abinda Babawo ya zama a yau sai muyi hakuri mu rungume shi tare da fatan shiriya"

Haj Mara na jin haka ta mike tsaye "yana ina?"

Zuwanta Dubai uku inda ta tura shi amma bata samunsa. Idan ta matsa masa da tambayar yana ina sai yace tafiya ce ta kama shi. Abinda bata sani ba shine ko wata shida baiyi a Dubai ba ya koma Italy.

Sai bayan kusan rabin awa BB ya iso gidan. Haj Mara ta manta da batun kishiya danta da take ta kewa take jira. Karar bude gate taji ta fito cikin sauri Alh Sule ya girgiza kai. Wannan makauniyar soyayyar da take yiwa danta ba gata bane gare shi ko kadan.

Motar bata gama tsayawa ba ya duro waje ya yo kan Hajiyar tasa yana ihun murna.

"Yooo, yooo Hajjaju meen.....see my Maama looking gorgeous"

"Na shiga uku" Haj Mara ta furta a hankali kwalla na sauko mata.

Wai yau Babawo da take mugun ji dashi ne haka sanye da wani mahaukacin jeans mai mugun fadi duk an gutsire kansa da kyar ya wuce gwiwa. Ga takalma kamar wanda zai shiga daji farauta manya manya. Rigar fara ce ta dame kwanjin da ya tara abin takaici da bakinciki yana sanye da sarkoki, dankunne ga gashi yayi kalba har kafada.
******

Kusan minti goma da zuwan Dahiru layin gidansu Mawadda yana ta tunanin kiranta zaiyi yace yazo ko kuwa ya tafi daga baya ya kira yace zai zo?

Can dai wata zuciyar tasa ya kirata. Gidan da sauran 'yan biki amma saboda gajiyar da suka yi tana daki a kwance kan gado. Yaya da Ade suna ware kayan gudunmawa saboda idan basu hadasu wuri daya ba wasu sai su salwanta gida na taro.

Tana jin waya tayi zumbur ta tashi zaune ta dauka tare da ficewa daga dakin ta koma kitchen.

Sallama tayi ya amsa mata sai kuma duk suka yi shiru sai bugun zuciyoyi.

"Ina cikin layinku fa. Zaki iya fitowa mu gaisa?" Ya katse shirun nasu.

Abin yazo mata a bazata sai kuma ta fara tunanin me zata ce a gida.

"Kunya nake ji Yayanmu"

Yayi 'yar dariya "nima haka Mawadda"

Suka sake yin shiru kamar wasu sabon shiga.
"Ina zuwa" taji yace sai ya kashe wayar.

Tunani ta fara me zaiyi ya kashe wayar sai ji tayi wani yaro yana cewa wai ana sallama da Baba inji Dahiru.

Gabanta ne ya fadi lokacin da Inna tace ace yana zuwa. Ita aka kira taje ta fadawa Baba ya fito yana cewa basuyi da kowa zai zo ba. Ita dai shiru tayi har ya fita. Yanzu jikinsa yayi lafiya sosai duk da shanyewar barin jikin amma yana zuwa gashi sosai yana iya tafiya da wasu abubuwan da kansa.

Daki Mawadda ta koma tana ta tunanin ya zata kasance.

Mal Fatihu yana fita Dahiru ya iso kofar gidan ya durkusa a gabansa. Har suka gaisa bai gane shi ba saboda kansa na kasa.

"Samari sai dai kuma ban waye ka ba"

Dahiru ya dago kai "Baba nine Da..."

"Dahiru? Laila ha illallahu kaine kuwa. Ikon Allah tashi tashi don Allah. Muje daga ciki"

Sosai mamaki ya kama Baba. Yana son Dahiru ko don yadda ya nuna soyayyarsa ga Mawadda a lokacin da ta rasa masoya.

Gyaran murya Baba yayi yana ce musu su gyara fa shi da bako ne. Ade ta kira Mawadda "yi sauri ki gyara dakin soro babanku yayi bako"

Dakin baya bukatar wani gyara saboda yau tun safe gyaran gida akeyi dama kujeru ne a ciki da dan tebur. Tana fita Baba ya shiga dashi yace ta kira su Iya su zo su ga bako.

Dahiru kunya ta rufe shi da ganin su Iya, Inna, Yaya da Ade. Dukkaninsu babu wanda ya nuna rashin jindadin ganinsa duk da yadda basu ji dadin irin rabuwar da akayi da iyayensa ba.
[08/01 8:32 pm] Biebie: *GUMIN HALAK...*💰13

*Batul Mamman*💖

Baba yana ta cewa ya zauna akan kujera amma Dahiru sam ya kasa yana mai jin nauyinsu a matsayinsu na iyayen Mawadda da kuma mutanen da kanwarsa ta bada gudunmawa wurin tarwatsa abin da ya rage musu na farinciki.

Su kuwa kowa murmushi yake yi da sake ganinsa a lokacin da suka cire tsammani. Gashi alamu sun nuna ya samu sukunin rayuwa wannan ma kuma abin farinciki ne garesu.

Iya baki har kunne tace "Dahiru ka zama babban mutum iyali fa?"

Kai ya sake sunkuyarwa Yaya tana dariya tace "Ni Haule! shekarun nan basu sauya maka hali ba ashe. Wannan kunyar tana nan"

Dariya suka yi masa sai Iya ta hau kiran Mawadda wai ta zo su gaisa da Dahiru.

Faduwar gabanta ya tsananta ta fito sanye da hijab da bai karasa gwiwarta ba akan dogon skirt din dake jikinta. Daga bakin kofa ta rakube saboda falon ba wani girman kirki gareshi ba mutanen ciki sun cika shi. Ita kunya Dahiru kuma ganin idon su Baba a tare suka ce

"Ina wuni" ta fada da sassanyar muryarta shi kuma da tasa muryar mai amo daga can kasan makoshi.

Abinka da tsofaffi Innar Fatihu da Iya suka kalli juna suka murmusa.

Dariya su Baba suka yi ganin su biyun sunyi duru-duru sai aikin sunkuyar da kai. Shi Dahiru mamakin kansa ma yake yi saboda a zatonsa ya dade da dena jin kunya irin wannan ashe da gaskiya Yaya bata tafi ba. Tun a baya ya rasa wane irin tasiri ganin Mawadda yake yi masa wanda yake hana shi fadin duk wani zance da ya tsaro a gida zai fada mata. Ita kuma dama kunyarta ma da rashin magana bazasu bari tayi abin arziki ba.

Ade ce ta fara tashi ta sake tado zancen iyali.

"Dahiru kayi zumunci mungode sosai. Ka gaishe da su Innarka don Allah. Kuma ina fata za ka kawo mana abokan namu ko kawaye mu gansu."

Gani yayi duk sun zuba mishi idanu yasa hannu ya rufe rabin fuskarsa yana kallon Mawadda da ido daya batare da sun gane ba

"Ade babu iyalin nan fa sai dai ku saka mu a addu'a"

Da sauri Mawadda ta dago kai don tsakani da Allah bata taba kawowa haka zai ce ba.

Baba ne ya fara yi masa fadan me ya zauna yi duk shekarun nan. Ya tabbatar dai ba ra'ayin su Mal Isiyaku bane.

Daya ban daya suka fice Mawadda ce akan gaba. Yaya ta kirata dakinta tace ta hada masa abin tabawa ta kai masa. Shiru bata motsa ba har Yayan ta tabata

"Ko baki so zuwan nasa bane?"

Kwalla taji ta taho mata ba shiri kuma mara dalili kawai ta fada jikin Yaya ta sa kuka. Nan da nan ta rikice ta zaunar da ita a bakin gado tare da sakaya kofar.

"Mawadda nasan zuwan Dahiru zai dawo miki da abubuwa da dama kamar yadda na tabbatar shima zai ji hakan. Amma ki barwa Allah komai tunda bamu ma san dalilin zuwan nasa ba yanzu. Goge idon maza ki tashi kada ya zargi komai"

Ajiyar zuciya kawai take saki ta tashi ta dauki tray din bayan Yaya ta hada da kanta. Sallama tayi sai da ya amsa ta shiga. Yana nan zaune a kasa har yanzu. Kusa dashi da ajiye tray din ta koma gefe da 'yar tazara tsakaninsu ta zauna a kasan itama.

Kayan cikin tray din ya kalla amma hankalinsa ya tafi ga muryarta da yaji alamun tana rawa yace "cikin wadannan kayan akwai wanda ki ka yi da hannunki?"

"A'a" ta amsa a takaice kanta a kasa.

"To na koshi" ya fada yana dan tura shi gefe.

Ji tayi hankalinta ya dan tashi "ko babu abin da ka ke ci a ciki?"

"Ko daya. Kinga mu bar wannan maganar kukan me ki ka yi daga zuwana?"

Da sauri ta dago kanta za ta musa ya shiga kada mata kansa.
"Kinyi kuka Mawadda. Kuma nasan cewa nine silar zubar hawayenki"

Ai kamar yace hawaye ku fito idanunta suka cika da kwalla suka fara saukowa da duminsu.

"Assha Mawaddatan wa Rahma ko bakiyi kukan nan ba nasani cewa ban kyauta ba an rabani dake a lokacin da muka fi bukatar rarrashin juna. Su Baffa..."

Kuka take sosai amma hakan bai hanata dakatar dashi ba "Su Baffa akan gaskiyarsu suka rabamu"

"Duk da a lokacin babu abin da ki ka fi bukata daga duk wani mai sonki sama da ya kasance tare dake ba tare da kyama ko ganin laifi ba?" Magana yake cike da takaici da bakinciki. Yanayin muryarsa kadai zai fallasa ciwon da yake nukurkusar zuciyarsa wanda ya dade yana dannewa.

Cikin wani irin yanayi mai ban tausayi tace "Yayanmu, ni kadai nasan menene a kasan zuciyata amma ina so ka sani ko kadan babu fushi da kai ko su Inna"

"Kenan ko yau na fito zaki aureni?" Ya jefa mata tambayar a bazata.

Murmushi tayi don son ta bagarar da zancen "ni bazan taba aure ba"
Chapter 30 · 0% Book details