← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 68

Sashe 47

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Inaaaa bukulun hirar soyayya zaka yi min ta ganka taki sakewa dani. Malam kowa yaji da kansa kawai. Ni da kake gani idan na hau saman nan sai nayi sati baka sani a ido ba"

Nan fa aka sami nayi suka rinka tsokanarsa karshe dai yace abu daya ya amince ayi. Shine zai dauko Nawal zuwa gidan Baba Prof shi kuma Attahir ya dauko masa Mawadda.

*****

Alh Sule yayi tambayar har ya gaji ya zubawa Haj Mara idanu.

Tamkar wata zararriya haka ta koma tun ranar da ya saketa a Kano. Ya dawo gidan da baiyi tsammanin samunta a cikinsa ba ya ganta a birkice. A zatonsa zafin saki ne kawai yake damunta shiyasa ya fita harkarta gabadaya. Tunda ya saketa duk wasu tarkacensa yake hadawa zai mayar da komai Abuja inda Yasmin take.

Yau ya dawo gida cikin dare ya sameta a falo zaune da daurin kirji sai dankwali da ta yafa a kanta. Dauke kansa ya yi daga gareta yasan wani salon jan magana take. Shi kuwa jira yake ciniki ya fada ya sayar da gidan. Dole ta tashi lokacin ko bata so.

Shan gabansa tayi ta mika masa wayarta ya kalli yarinyar da take jiki ya dago cikin rashin fahimta
"wace ce wannan din?"

"Mawadda ce Alhaji" tace tana kuka "Babawo sai da ya nemo yarinyar nan shine ya turo min sako wai mu fara shirin tarbar amarya. Ko dai yana da tabin hankali ne ban sani ba?"

Fasa wucewa yayi ya koma ya zauna yana fuskantarta.
"Marakisiyya idan kina kaunar Babawo irin son da musulunci yake so ki yiwa danki to ki fada min inda yake idan kin sani na dauko shi."

Sai yanzu ta dan saki rai "za ka yi masa visa ko China ne ka tura shi sai na bishi tunda nima yanzu babu auren."

"Babu inda zaije sai ya amshi laifinsa na yiwa 'yar mutane fyade. Idan case din Mawadda kun rufe shi ai na Qareeba babu yadda zakiyi"

Tashi tayi a tsorace "Alhaji yaron nan jininka ne meyasa baka kaunarsa? Idan muka tafi nayi maka alkawarin ko Nigeria ya dena zuwa. Ta yaya zan rayu idan aka rufe shi?"

Gani yayi zata bata masa lokaci ya tashi abinsa "tunda kina da kudi sai ku tashi sama idan kun ga dama. Soyayya daya ta rage min tsakanina dashi itace addua, bayan haka bazan kashe kaina akansa ba."

Wayarta ya fizge ya tafi da ita. Sai san yadda yayi ya tura masa sako da ita ya janyo shi gida.

Haj Mara ta dade a tsaye tana tunanin mafitar da take jira guda daya. Ita ba kudi ba sannan babu Babawo. Sai dai ta sani duk abinda Alh Sule zaiyi musu danta yana da gadonsa.

Wanka Alh Sule yayi ya fito wayar Haj Mara tana ringing. Da sauri ya dauka yayi zaton Babawo ne yaji muryar agent dinsa da suke harkar gidaje da filaye. Mutumin bai jira anyi magana ba yake sanar da cewa ta duba wayarta ko alert ya shigo ciniki ya fada sun sayi gidan a miliyan tara da rabi saboda cinikin a kurarren lokaci yazo.

Alh Sule ya kasa shiru "Badau nine Alh Sule bata kusa. Wane gidan kake nufi ne"

Yayi dariya "Ah ranka ya dade barka da dare. Gidanka na anguwan dosa da tace ka bada umarnin a sayar zaka hada ka sayi wani babba na bayansa."

Kasa ya sauka da sauri bata nan ya koma dakinta tana zaune tayi tagumi. Yana shigowa ta tashi ya yi niyar marinta ma ya fasa don takaici.

"Ashe barauniya ce ke ban sani ba sai yau. Waye ya baki izinin sayar min da gida?"

Ta ware masa idanunta babu alamun nadama "wanda yace danka ya yashe ni ya kwashe min kadarori. Wannan gidan kuma da na sayar idan ka mutu a cire a gadon Babawo ince ko shikenan"

"Shikenan kuwa Marakisiyya. Zanje na kwanta sai da safe"

Kallonsa tayi da mamaki "au shikenan kawai zaka ce?"

"Banda abinki tsawaita magana da mahaukaciya baki ganin bata lokaci ne?"

Baki bude ya fice ya barta tana cizon yatsa.

******

Ranar juma'a da yamma akayi taron Mother's eve da Haj Mama ta shirya. Taro ne na gogaggun 'yan boko amma matar nan ko kadan bata nuna kyama ko kaskanci ga dangin Dahiru ba.

Kayansu yayar Attahir ce ta basu iri daya su biyun. Shiyasa suna karba suka sayawa amaren nasu material iri daya da ya dace da nasu kayan. Dinki ma awo kawai suka nema don so suke yadda zasu saka komai iri daya matansu ma haka. Hatta jaka da takalmi da su dankunne iri daya suka saya musu.

Karfe hudu da rabi a kofar gidansu Nawal tayi musu. Baya ta shiga kawarta zata biyota Attahir yace mazaunin daya amaryar ne su a hadu a venue.

Shi da Dahiru suna ta hira kunya ta hanata magana har suka isa Tunga daukar Mawadda.

Tayi kyau ba kadan ba Rafia ta rakota har mota gabadaya fuskarta a rufe da mayafin kamar yadda aka shigo da Nawal.

Sun fara tafiya motar shiru a hankali ta bude fuskarta kadan ta tabo Nawal.

" 'yar uwa bamu gaisa ba"

Itama ta bude nata ta mikowa Mawadda hannu "cikina ke kadawa Sis"

Kasa-kasa Mawadda tace "ke nima haka fa kunya da tsoro nake ji. Amma kinyi kyau sosai" ta kare da murmushi.

Nawal tace "kema haka, a waya nayi ta miki surutu yau kema kunyarki nake ji"

Dariya suka yi a hankali suka sake rike hannun juna.

"Ehem, ehem.....ya kake gani idan muka wuce gidan dasu tun a yau? Sai su kwana a kasa mu kuma mu hau saman. Gobe ana daura aure kowa ya tafi gidansa" cewar Dahiru yana kyaftawa Attahir ido.

Ya amsa masa da cewa "shawara tayi fa dadina da kai kenan saurin fahimta kamar ka shiga zuciyata"

Idanun Mawadda da Nawal suka kwalalo kowacce ta rikice.

Attahir ya kara da cewa "ina jin yunwa mu fara biyawa ayi cefane sai mu wuce yau girkin amare zamu ci."

Tafawa suka yi shi da Dahiru.
"Idan an nemesu sai muce mun tafi honeymoon"

"Me??" Su Mawadda suka ce a tare.

Kusan tare Dahiru da Attahir suka waigo suna kallon bayan suna musu dariya.

"Ashe duk kuna da baki. Kun shigo kun ki kula mu kuna hirarku ku kadai"

Mawadda tayi murmushi "haushi kuka ji kenan"

Nawal tace "mu suke so mu fara lallabasu muna amare"

Attahir ya amsa maganar Mawadda "Ina batun jin haushi bayan hirar taku bata wuce mallakar miji"

"Fada musu dai su san mun san komai" Dahiru ya taya shi

Nawal ta hada ido da Attahir da yake tuki ta madubi tace "wasu matan dai banda mu"

Dahiru yace "ke dai 'yar uwarmu Nawal abar kaza cikin gashinta"

"Da ka bari na figeta dai mu ga masu shan kunya" inji Attahir.

Har suka isa wurin event din suna zolayar juna suka fito kana ganinsu kowanne ya dace da amaryarsa soyayyarsu ga juna bata boyuwa.

Ba karamin kyau suka yi ba komai nasu mazan da mata irin daya sai daukar ido. Kowacce amarya 'yan uwanta sun zo haka aka yi taro cikin mutumci aka watse da farinciki.

Washegari karfe goma na safe aka daura auren Attahir AbdulHadi da amaryarsa Nawal Ahmad akan sadaki naira dubu hamsin. Ko zama basuyi ba aka dunguma zuwa garin Tariwa.

Wani masallaci da Mal.Fatihu bai san dashi ba kafin ya bar garin babba nan aka taru. Duk yadda yaso ya daure sai da yayi kukan farinciki.

Maigari Muhammadu shine ya tsaya waliyin amarya yayin da ko ba'a fada ba Prof Abdulhadi shine waliyin ango. Bayan addu'o'i dimbin jama'a masoya da 'yan ganin kwaf suka shaida daurin auren DAHIRU ISHAK da MAWADDA FATIHU akan sadaki naira dubu dari lakadan wanda Baba Prof ya zaro daga aljihunsa batare da yabi ta kan kudin da Bilya yake kokarin mika masa ba dubu hamsin.

Dahiru hularsa ya janyo ya rufe fuska saboda da gaske kuka yake son yi. Lallai a duniya idan ka sami mai sonka domin Allah Kada ka yar dashi domin kauna ta fisabilillah ba kasafai ake samu ba.

Shi kuwa Prof Abdulhadi jama'ar da ya gani da zantukan da ya ji a waje ana cewa yarinyar nan ce da aka koresu. Yasan labarinta wurin Dahiru daga baya yaji yana sha'awar kara mata kima a idanun mutanen.

Maza dai basu wani dade ba saboda kada su makara yau za'a kai amare. Su Inna kuwa ana can ana taro gida da makota an cika makil abin sai son barka.
*****

Motoci hudu BB ya samo shi da abokansa 'yan duniya suka tafi gidansu Mawadda tare da Danmani. Motar da tafi kyau wadda a cikinta wani abokinsa ke tukawa yana gefe ita suke sa ran daukota a ciki. Sun gama shewarsu da iface-iface a gida wai yau BB yake ango.

Cikin jerin motocin daukar amarya suka shige abinsu suna jiran fitowarta bayan gama tsare-tsaren yadda zasuyi ko da lamari ya kwabe.

Ana idar da magariba akace su fito. Kuka Mawadda take yi kamar idanunta zasu fito tana manne da jikin su Iya an kasa bambareta. Kowa haka yayi kafin ya bar gida da kyar sai da Ade ta dake ta soma fada aka fito da ita. Atampa ce a jikinta riga da zani tayi matukar kyau sai katon mayafi an lullubeta ko fuska ba'a gani.

Suna fitowa guda cikin abokan BB yayi saurin zuwa inda Yaya da matar kanin Ade suka sakota a tsakiya yace ga motar daukar amaryar can. Waige suka fara suna neman Gwaggonin Dahiru uku da suke cikin gidan. Wadda ta fara fitowa ta kalli yaron tace kaine Attahiru yace a'a bai sami zuwa ba, ba don yasan waye Attahir din ba. Matar tayi dariya tace suje su shiga tunda akwai namiji a gaban tayi musu kadan motar. Ta cigaba da cewa dama ta fada da wuya su iya zuwa daukan amaren juna ana hada hadar biki. Motocin duka a layi suke harda ainihin na wasu abokan angon da ma Danlami a cikin motar Bilya shiyasa basu kawo komai ba ta tsakiyar suka je suka shiga wadda aka bude musu.

Zamansu ke da wuya Attahir ya shigo layin ta baya ya ajiye motarsa daidai kofar gidan yadda ba sai amarya tayi doguwar tafiya ba.
Chapter 47 · 0% Book details