← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 68

Sashe 7

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana kunkuni ya kawo masa sai dai shima yayan nasa ya burgeshi sosai don yayi kyau. Tare suka fito sai da yayi alkawarin bashi kayan sannan ya barshi ya tafi shi kadai.

Sai da ya kusa zuwa gidan don har yana hangoshi sai kuma kunya ta kamashi. Me zaice mata idan ta fito? Garin yaya ma baiyi tunanin bari ta dan huta ba. Yana tsaye yana ta tunanin har aka soma kiraye kirayen la'asar. Dayake da alwalarsa can gefen bishiyar da aka zagaye da duwatsu yaje sukayi sallah harda babanta wanda yace ya karaso mana zai tura a kirawota. Shi dai Dahiru kunya tasa yayi ta lankwasa kai yana murmushi.

Mal Fatihu yayi murmushi shima "kai da ita kowa kunya zanga wannan zama naku Dahiru. Yanzu dai idan ka koma gida ka sanar da Malam yazo muyi maganar bikin nan don bana jin zan bari ta koma birnin nan gaba daya. Gidan aikin nata sunce tafiya zasuyi na wata uku babu kowa a gidan, dama kuma lokacin ai ya matso duka duka bana jin zai kai wata ukun ma a gaba"
[03/12 23:02] Meela Adeel: *GUMIN HALAK...*馃挵4

*Batul Mamman*馃挅

Kunya irin wadda basa jin sun taba ji a rayuwarsu ce ta saukarwa Baba da Yaya. Ade kuwa ko juyawa batayi ba ta yunkura zata kamo hannun Mawadda ta yanke jiki saura kadan ta fadi Baba yayi saurin tareta. A daddafe ta matsa jikin gadon duba marasa lafiyan sai kuka ya kwace mata. Kuka take bilhakki na tausayin Mawadda, na bakincikin yadda rayuwa take gara talaka sannan uwa uba ganin tamkar laifinsu ne ita da Baba da suka bar 'yarsu ta tafi aiki.

Shi dai Baffan Dahiru kunya yaji da suka biyo bayansu gashi sun samesu a wani yanayi da babu mai son a ritsa shi a cikinsa.

Likita ganin yadda jikkunansu suka yi sanyi yasa shi sake cewa suna bukatar dan sanda a gaggauta zuwa kiransu domin su sami damar bawa Mawadda kulawa.

Dahiru kallo daya ya yiwa Mawadda daga inda take rakube akan gadon ta rirrike karfen kamar ta shige cikin bango ya dauke kansa. Zuciyarsa ke wani irin harbawa saboda yadda ya ga fuskarta. Wani daci ya soma ji a wuyansa yayi saurin juyawa zai bar wurin.

Inna duk ta rikice itama ta dakatar da shi "ina kuma zaka tafi?"

Bai kalleta ba sai kallon Baba da yayi "zan je kiran 'yan sandan ne"

Baba yayi saurin fitowa "muje dama tafiya zanyi yanzu"

Fita suka yi tare aka bar sauran da kallon kallo a gefe kuma uwa da 'ya suna kuka mai ban tausayi.

Tafiyar kurame ce tsakanin Baba da Dahiru har suka sami mashin biyu suka hau. Ofishin 'yan sanda mafi kusa suka sauka kowa tunani ya baibaye zuciyarsa.

Da suka shiga 'yan sanda biyu ne a wurin karbar korafi. Daya yana ta sakace hakora ya gama cin tsire dayan kuma gyangyadi yake yi akan wani benci. Sallamarsu ma basa su ji an amsa ba.

Baba ya matsa jikin kantar ya tsaya yana duban mai sakace "yallabai barka da yamma"

Suturar jikinsu kadai ta tabbatarwa jami'in tsaron cewa da wuya wani korafin kirki ya kawosu da ya wuce na satar su akuya ko rikicin iyakar gona. Duk su zo suyi ta damun mutane da yamman nan talauci yayi yawa kowa zuciya a sama. Bai amsa shi ba sai kai da ya gyada alamun yana sauraron shi.

Dan rissina kai yayi duk kuwa da cewa mutumin ko baiyi da dashi ba to lallai kaninsa ne na can baya ya dan rage sautin murya a kunyace ya soma magana
"daga asibiti muke mun kai yarinya ance sai mun zo da dan sanda za'a duba ta"

Tsinken ya ajiye sannan ya gyara zaman hularsa duk cikin nawa da nuna halin ko in kula da damuwar da ba tasu ba "to kai dattijo da baka san lalurar da sai anje damu da wadda ba sai munje ba?"

Dahiru zuciyarsa ta fara tafasa dama ya lafiyar kura ransa a bace yake tun dazu ga wannan mutumin yana musu magana a wulakance. Kafin yayi magana Baba ya cigaba

"Yarinyata ce aka yiwa fyade.." ya karashe kalmar a hankali saboda kunya.

"Babbar magana kai Nalado tashi wannan aikinka ne. Ka bisu asibitin bayan na gama daukar bayanansu."

Lalube ya soma yi a aljihu wai yana neman biro. Can dai ya tambayi wanda ya kira Nalado shima yace babu. Suna ta dibi-dibi duk su biyun wayar Dahiru ta soma kara. Ganin sunan mahaifinsa yasa shi tsorata ya kara a kunnensa da sauri.

"Dahiru kuyi sauri jikinta yayi mugun zafi har tana sambatu. Likitan ya taimaka zai saka mata ruwa"

Da yake waya ce techno mai dan karen kara Baba ya gama ji. Hankalinsa gabadaya ya tashi Dahiru ya tambayi dan sandan biro kadai ne babu yace eh babu ko kunya. Fita yayi yana gudu ya rasa wace hanya zai bi ya sami kantin da zai sayi biro. Daga can tsallake ya hango wani shago da ledojin ruwa, daga kafar da zaiyi takalminsa ya tsinke ya fadi fuska a kasa saboda da hanzari ya motsa. Ko kulawa baiyi ba ya tashi yana kade jikinsa zaiyi gaba wata mota fara kirar marsandi tazo tayi pakin a gefensa tare da buga hon. Abin mamaki sai ga 'yan sanda kusan bakwai sun fito daga cikin ofishin wanda tun dazu yake tsit sai mutum biyun da suka gani.

Duk wurin motar suka nufo DPO dinsu ya fito daga ciki. Yana kallon Dahiru yace wannan fa sai ga Bala wanda yace babu biro ya yo gaba da sauri.

"Yallabai yanzu zan dauki bayanansu. Case din fyade ne zamu je asibitin. Bawan Allah koma ciki muyi sauri"

Baba da Dahiru suka saki baki wato wulakancin da gangan aka yi musu ko don an ga basuyi kama da masu arziki ba.

Kamar yadda ta basu labari haka Baba ya labartawa Bala suka dunguma har Nalado suka bisu asibitin saboda ganin idon DPO da baya wasa da aiki.

Da isarsu ba bata lokaci aka gama abinda za'ayi suka shige da Mawadda wani dakin daban. Iyayen maza sunyi jigum matan na kuka. Inna kuwa hakuri kawai take basu lokaci-lokaci sai ta kallo Dahiru. Sam ta kasa gane a wane hali yake ciki. Shi kadai yasan yadda yake ji a ransa sakamakon wannan tashin hankali.

Su sergent Bala suna jira a fito da ita idan zata iya magana tayi musu bayani sosai idan bazata iya ba su dawo washegari.

Kusan minti arba'in suka dauka kafin likitan da nos suka fito.

"Ina mahaifiyarta" cewar likitan yana binsu daya bayan daya.

Ade tayi saurin nuna Yaya duk da har kasan ranta a matse take taji me yasa ake neman mahaifiya.

Ajiyar zuciya likitan yayi "ki shiga wurinta ko zamu samu ta dena kukan nan don mutum daya nake bukata a dakin. Sannan gaskiya kunyi sakaci wannan abu ya wuce kwana uku ga dukkan alamu ciwo yana neman zame mata wani abu daban. Sauran bayani Baba muje nayi maka"

Yaya da Ade suna kallon juna kowacce na son tafiya wurin Mawadda. Inna tana kula dasu duk suka bata tausayi. Wannan bakar ranar kada Allah Ya nuna min ta fada a zuci.

Yaya da sanin ya kamata ta nemi wuri akan bencin da yake jingine da bango ta zauna "Sa'ade jeki ki rarrasar min ita tun jiya nake fama taki shiru"

Allah sarki dama a dofane take da sauri tayi gaba tana share hawaye.

Mawadda tana kwance tana hawaye taji an turo kofar dakin tana kara keyyyy ba karamin tsoro hakan ya bata ba. Tuna mata yayi da lokacin da BB ya shigar da ita dakinta na gidansu ya kulle. A firgice take gabadaya har Ade ta karasa gaban gadon.

"Ade..."

"Shhhh kukan ya isa haka."

"Gwara in mutu da wannan ..."

"Kada na sake jin kina zancen mutuwa. Shikenan kuma saboda Allah Ya dora miki jarabawa sai ki karaya lokaci guda? Tunda kukan bazai amfana mana komai ba ki daure babu abinda muke bukata yanzu sai samun lafiyarki"

Shiru tayi tana wata irin ajiyar zuciya mai karfi. Cikin dan kankanin lokaci bacci ya soma fizgarta kanta na cinyar Ade. Dama likitan ya sa anyi mata allurar bacci.

Ko minti goma bata cika ba ta tashi a gigice harda ture Ade don ta manta waye a gurin tayi waje. Allurar jikinta ta karin ruwa ta cizge harta ji mata ciwo ga jini yana diga. Mafarkin BB take yi yana kokarin danneta. Jikinta har tsuma yake yi lokacin da taci karo da Dahiru ya dawo daga siyo musu ruwan alwala saboda gabatowar magariba. Su Yaya duk sunyi kanta ana kokarin hanata fita.

A can ofishin likita ya yiwa yan sanda bayanin su dawo washegari saboda bata cikin hayyacinta sosai. Bayan fitarsu ya soma yiwa Baba fadan kai yara aikatau da suke yi.

Baba yayi murmushi mai ciwo yana da bayanai da yake son yiwa likitan akan matsalarsu amma yanzu ba muhallin hakan bane. Likita ya cigaba da yi masa bayanin cewa ciwukan jikinta sun basu dukkan wani taimako da ya dace. Babbar matsalar shine tabon da aka yiwa zuciyarta sai sunyi hakuri kuma sai an daure. Yanzu bazasu gane girman abin ba sai taji saukin ciwukan jikinta.

Suna wannan tattaunawar ne suka jiyo ihunta. Tare suka fito da sauri tana neman fita Dahiru ya saki ledojin hannunsa ya kamota. Jin namiji ya tabata ta sandare cikin murya mai ban tausayi tace
"ka rufa min asiri BB ni ba 'yar iska bace aure za'ayi min. Kayi hakuri don Allah"

Dahiru bai san lokacin da hawaye suka zubo masa ba a yayin da Ade da Yaya suka rikota suna ta koke koke. Baffa da Inna ma abin yayi matukar shigarsu suna kallo aka mayar da ita dakin.

Ba su suka sami kanta ba sai bayan isha da aka kara mata wata allurar da magunguna bacci mai mugun nauyi yayi awon gaba da ita. Sai a lokacin suka fara batun tafiya.

Baba yace Ade tazo su tafi don yasan zuwa yanzu Iya ta sami labarin zuwanta gari gashi bata je gida ba. Shima nasa iyayen dole zasu ji daga wurinta da kuma yara da suka tura musu daga makarantar allo su zo su tada hankalin rashin sanin me yake faruwa.

Ba don taso ba sai don kara da kawaici ta bisu suka tafi.
Chapter 7 · 0% Book details