← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 68

Sashe 33

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Me kuma take nema ya tambayi kansa. Kamar yaji shi ta sake cewa ya daure yazo. Baya son jan magana da ita kawai yace yaji sai ya taso daga office.
Babu sallama ya ajiye wayar ya juya abinsa ya kwanta.

Zuwa wayewar gari ya ma manta da wayar Qareeba harkokin gabansa kawai yake yi sai tunanin Mawadda da haduwar da zasuyi anjima.
*****

"Kin tabbatar da abinda ki ke fadi kuwa Qareeba?" Cewar Dr Tani cike da doki.

"Sosai Mummy zaki ganshi ma da kanki don yace yana tasowa daga office zai zo" Qareeba ta amsa tana dariya.

Dr Tani ta jinjina kai "Allah Sarki ashe shine rabon naki lokaci ne kawai baiyi ba. Dama ance matar mutum kabarinsa. Sai ki tashi a soma hada masa abinda zaici tunda daga office zai biyo"

Hannu Qareeba tasa ta rufe fuska wai ita kunya ta tashi tayi hanyar kitchen tana kiran mai aikinsu tazo ta tayata aiki.

Dr Tani kuwa zuciyarta fes tana murna da wannan sa'a da Qareeba tayi.

Dahiru na fitowa akan hanyarsa ta komawa gida yana tsaye wurin danja Qareeba tayi ta kiransa. Kallon wayar yayi sannan ya tuna jiya yace zaije. Agogo ya kalla yaga akwai sauran lokaci zai iya lekawa gidan nasu shap-shap ya koma ya shirya yaje wurin Mawadda. Yadda ya santa da naci idan baije ba kiransa zata yi tayi kamar yadda take masa da idan zata bashi aiki Abinda baya so kenan.

A falon Dr Auwal aka jera masa komai na tarar bako don Dr Tani tace dole a karrama shi yadda ya dace.

Qareeba ce a gaba yana biye da ita zuwa falon duk yabi ya takura saboda yadda yaga abin babba ne. Taci kwalliya sosai gashi yau shine har falon maigida.

A dofane ya zauna ya kasa sakin jiki. Sai da ta zuba masa lemo a kofi ta mika masa sannan ta zauna a kujerar kusa dashi. Haka ya rike kofin shi bai sha ba shi kuma bai ajiye ba yana jiran karin bayani.

Kusan minti biyar babu wanda yayi magana. Sai Qareeba ce tayi ta mata tace

"Baka ce komai ba?"

"To me zan ce ni da ki ka kirani"

Kai ta sukunyar tana wasa da yatsunta "kayi hakuri da jinkirin da aka samu na rashin fahimtarka da nayi a wancan lokacin."

Kansa ya shiga duhu ya kasa gane inda ta dosa yace "ban fahimceki ba."

"Ka tuna wata rana da na tambayeka me ka ke kiran masoyiyarka?"

Idan ma anyi haka gaskiya ya manta amma don a sallame shi da wuri yace ya tuna.

Murmushi tayi ta sake matsowa yadda zasu fuskanci juna da kyau.
"A lokacin abinda ka fada dariya ya bani. Kace wai kana kiranta Qulqulatil Qurabati. Sai bayan ka tafi rannan nayi dogon nazari ashe dani kake ban gane ba"

Da sauri Dahiru ya daga hannu "Dakata Anti Qareeba nifa na kasa fahimtarki"

Bayani tayi masa dalla-dalla kuwa. Bayan ta nutsu tayi tunani ta gane daga sunanta ne ya kirkiri wancan suna alamu na cewa yana sonta.

"Nasan a lokacin rashin kudi da wayewa yasa ka boye min soyayyarka. Amma yanzu tunda na fahimta na amince kuma Mummy is happy da hakan" tayi fari da ido tana sunkuyar da kai.

Wannan abu yafi gaban dariya a wurin Dahiru tausayi ma ta bashi. Banda shirme irin nata wane abu ta ga yayi da zai nuna yana sonta ko kuma duk tsabar son auren ne yasa kanta toshewa irin haka.

"Anti Qareeba..."

"Ka dena kirana Anti duk da nasan mu sa'anni ne kada ka damu kusan abinda yake tashe kenan yanzu auren sa'anni"

Gani yayi idan ya barta ta cigaba da wannan tunanin lallai ya cuceta. Gara kawai ya yiwa tufkar hanci tun ba'aje ko ina ba.
[08/01 8:32 pm] Biebie: *GUMIN HALAK...*💰14

*Batul Mamman*💖

Nutsuwa yayi sosai ya fuskanceta hannuwansa a hade kamar mai roko yace "don Allah idan daga ranar da muka fara haduwa zuwa yau nayi misleading dinki...uhmmm idan nayi wani abu da zai nuna miki ina sonki ne kiyi hakuri ba niyata ba kenan. Ina da..."

Katse shi tayi da sauri "kada kayi tunanin nafi karfin zama da kishiya, ko kadan wallahi. Ni bani da matsala kaima shaida ne. Matarka da yaranka duk zan zauna dasu da zuciya daya."

Girgiza kai yayi don ya fuskanci abin nata na gaske ne "Anti Qareeba!"

Idanuwanta ta ware a kansa "ni dai gaskiya bana son Antin nan"

"To Malama Qareeba ki tsaya ki gane me nake cewa. Ni Dahiru bani da mata amma ina da wadda nake so. Tsakanina da mutanen gidan nan ciki kuwa harda ke bai wuce mutuntawa ba albakacin zaman da nayi daku a baya"

Hawaye ne ya soma wanke mata fuska. Ita bata san ya shiga ranta haka ba sai da ta kula nema yake yace baya sonta.
"Dashiru kada kayi min haka...duk tsahon lokacin nan da banyi aure ba ban taba kai kaina ga namiji ba gudun irin haka. Yanzu ma ni na sani kana sona tsoron yadda iyayena zasu dauki maganar kake yi ko?"

Ikon Allah. Da Hausa yake mata magana amma kamar ma tana sane take kin gane me yake nufi.
"Kinga ki kalleni da kyau nine Dahiru mai shara da wankin gidanku na da"

Daidai lokacin Dr Tani ta iso kofar falon. Ta kasa hakuri so take ta ji da kunnenta don ta fara shirin gaske 'yarta tayi miji.

Hankalin Qareeba a tashe ta zamo daga kan kujerar da take kamar zatayi masa durkusu irin na me neman taimako.

"Ni mummuna ce ne?"

Tausayi ta soma bashi ya girgiza kai.

"To ko ina da wata nakasa da ban sani ba? Don Allah ka amince Mummyna ta dena kukan rashin aurena. Wallahi zan zauna da ko mata uku ne ni dai kawai ka amince. DAHIRU...SONKA NAKE YI"

Shiru yayi ya kasa magana yayin da Dr Tani ta toshe bakinta ta bar wurin don kada su ji kukan da take yi.

Sai da yaga ta dan sami nutsuwa ya soma yi mata magana "Anti"

Harara ta galla masa yayi dan murmushi "Malama Qareeba akwai girmamawa tsakaninmu bazan iya kiran sunanki haka nan ba. Kiyi hakuri Allah zai kawo miki naki mijin. Ni ina da wadda zan aura in sha Allah nan da lokaci kankani. Ina kara baki hakuri akan kuskuren da nayi bisa rashin sani har kika yi zaton soyayya ce. Allah Ya bamu alkhairi"

Kofin da ta bashi wanda ko kurba daya bai yiwa lemon ba ya ajiye ya fita tana ji tana gani. A wurin ta kife ta shiga rera kuka. Ta rasa menene aibunta da maza suke gudunta an rasa me tsayawa magana tayi nisan zuwa kunnen iyaye ma.

Yana fita ya shiga motarsa ya furzar da iska tare da nannauyan numfashi. Haka kawai da can banda wulakanci babu abinda yake hadasu da mutan gidan musamman Mummyn tasu. Qareeba kuwa kamar wadda aka kawowa abin debe kewa da sa nishadi. Duk wata sharar shirmenta akansa take saukewa. Shine kuma yau ya zama masoyi don rainin wayo. Fita yayi daga gidan rai a bace yana ayyanawa a ransa yayi zuwan karshe kenan. Gidan Prof Abdulhadi yaje yayi rashin sa'a fitarsa kenan. Sun dan taba hira da Hajiya Mama daga nan ya fita ya tafi gida sai yayi magariba yaje wurin Mawadda.

*****
Kusan minti goma da fitarsa sannan Qareeba ta fita idanu a kumbure. A falo ta hadu da mamanta ta yi saurin sakin fuska.

Dr Tani ta daure kamar bata ji komai ba tace "yaya kuka yi har ya tafi ne?"

Ta hadiyi yawu da kyar "eh Mummy daga zuwansa duk wahalar aikin da muka yi wai yana sauri." Tana magana hawaye na zuba tana gogewa da hannu "haushi naji shine harda kuka"

Idanun Dr Tani suka ciko da kwalla ganin 'yarta tana kokarin boye mata damuwarta. Ashe Qareebanta ta girma.

"Kiyi hakuri kila aiki ya masa yawa ne. Jeki ciki ki gyara fuskarki hawaye yasa kwalliyar duk ta cabe miki"

Tana tafiya Dr Tani ta goge nata hawayen. Wane irin bakin jini ne da Qareeba ace har mai wankinsu na da, wai Dahirun da ta raina shine yake da bakin cewa baya sonta.
*****

Ta dukufa tana murjewa amaryar dake gabanta dilka Ade ta shigo dakin da suke aikin ta sanar da ita Baba yace Dahiru yana jiranta an sauke shi a falon soro.

Sunansa kawai da taji yasa jikinta yin sanyi har ta kasa samun kuzarin yin aikin yadda ta faro.

Amaryar wadda ta kasance kawarta ta Islamiyar da suke zuwa a unguwar tace cikin mamaki "Mawadda dama akwai ranar da zanji ance ana kiranki? Lallai yau akwai labari don sai na fadawa 'yan ajinmu tun wuri ma na sanar dake kada a tsokaneki kice na kai gulma"

Dariyar dole tayi "to uwar son labari dan uwanmu ne"

"Mayar dani yarinyar goye dan uwan ne zai tsaya a wancan falon bai shigo ya gaishe da kowa ba?"

Mawadda ta cigaba da murje mata jikin sai dai gaskiya aikin nasu akwai saura sosai. Ita da kanwarta ne amaren kuma basu zo da wuri ba. Kanwar aka fara gamawa har ta tafi yanzu nata baiyi nisa ba. Hannu tasa ta taya Mawadda ko fita abin baiyi ba ta dauko hijabinta ta saka. Duk yadda Mawadda tayi ta rokon ta zauna taki a cewarta taje ta saurari bakonta ita din ta gida ce gobe sai tazo da wuri tunda na sati zasu yi.

Bayan fitarta nuku-nuku Mawadda ta zauna yi har Baba da kansa ya sake magana yace taje mana. Ita gaskiya tana jin kunya don ta manta rabon da ta fita da sunan zance. Duk wanda yazo nemanta ba fita take yi ba dama Rafi'a ce mai zuwa sallamarsu.

Marwanu da Saifullahi duk basa gida yanzu. Daya yana ABU Zaria daya kuma yana Kazaure informatics da sai ta tura masa su kawai.

Ba wani shiri tayi ba ta dai gyara jikinta ta yafa mayafi ta tafi.

Innar Fatihu ta dubi Baba bayan fitarta "kada yaron nan fa yace zai sake dawowa neman aurenta a kuma komawa gidan jiya"

Iya tace "kuma na kula ita ma kanta tana son shi. Fatihu ko zaka dakatar dashi ne kada a sake fama mata tsohon ciwo a barmu da jinya"
Chapter 33 · 0% Book details