← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 68

Sashe 31

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ji yayi kamar ta zuba masa ruwan zafi maganar har kasan zuciyarsa ta daka "Mawadda zakiyi aure, zaki haihu, zakiyi farinciki kamar kowacce mace. Ke dai ki shirya don da gaske dawowa nayi na yaki duk samarinki a karo na biyu a sake sa mana rana."

Inama ace bata taba sanin wani Babawo ba kaddara ce kawai ta rabata da Dahiru yau da tafi kowa farinciki da kalamansa. Sai dai kaddara ta riga fata a yadda take jin kanta ta sani da matukar wahala ta iya rayuwar aure ko da kuwa iyaye da dangin mijin sun karbeta hannu bibbiyu. Wasu hawayen ta soma yi tun tana gogewa har ta kyalesu kawai tana shessheka yayin da Dahiru ya zuba mata idanu yana mai kara tsanar fasikin da yayi sanadiyar lalata mata rayuwa haka.

Sai da tayi mai isarta ta dago idanu duk sunyi ja kamar gauta. Dahiru yace ta taimaka ta sake masa magana da Baba amma ta dawo magana yake son yi masa a gabanta.

Gaba na faduwa ta tashi tana tsoron kada yayi wata maganar da ta shafi aure don bazata yarda a sake maimaita irin abinda ya faru baya ba. Tunda iyaye basa so magana ta kare.

Tare da Baba suka dawo yana zaune akan kujera su biyun a kasa. Dahiru ya soma bashi hakuri akan yadda abubuwa suka kasance a baya.

"Hanani auren Mawadda bai yi min ciwo kamar baza labarin da Ummiyo tayi ba. Nasan lokaci ya ja bazaku so ayi ta tada maganar ba amma tsahon shekarun nan babban burina bai wuce na ganka na roki gafararku ba. A dalilin fitar da maganar nan gashi an raboku da gida...." zuciyarsa tayi rauni sosai ya kasa karasa abinda yayi niyar fada.

Baba yayi murmushi irin na dattijan da suka san me suke yi.

"Dahiru ko da fitar maganar nan ko babu ka sani babu wani abu da zai hanamu tafiya saboda tun ran gini tun ran zane. Kuma banda abinka ma idan ka dubemu ka dubi kanka sai mu taro mu godewa Allah saboda a kowacce jarabawa ta rayuwa akwai alkhairi, ko dai mu fara girbarsa a duniya ko mu karbi sakamakonmu a lahira. Tabbas an cutar min da 'ya an bata mata rayuwa. Kai mu kanmu kamar yadda kake gani babu wanda al'amarin nan bai yiwa tabo ba. To amma me, a dalilin hakan ka fito neman ilimi don ka aureta ka tallafi rayuwarta ko ba haka ba?"

"Haka ne"

"Yau gaka ka taka wani matsayi wanda da hakan bata faru ba karshenta kunyi aure amma kila abincin da zaka bata ma sai an kai ruwa rana zai samu. Mu kuma da ko a kauyen kasan cewa ni talaka ne fitik yau gani a birni 'yan layin nan da yawa ma Alhaji suke kirana duk da banje ba" ya kare yana dariya.

Su ma murmushi suka yi wanda dama burinsa kenan. Nasiha mai ratsa jiki ya cigaba da yi musu akan hakuri da kaddara a kowane yanayi sannan ya tashi ya koma ciki. Yaya da Ade suka bishi daki suna son jin me Dahiru yace. Girgiza kai yayi yace mata duk halinku daya. Su kuwa suka matsa masa da tambaya ya samu ya kashe bakin nasu da yacewa Ade ta ajiye kunyar 'yar fari wannan abu har Innarsa sai ya fadawa. Ba shiri suka fita daga dakin suna kuskus kamar ba kishiyoyi ba.

A falon Dahiru ne ya mike tsaye yana gyara rigarsa. Itama Mawadda ta tashi ta matsa daga ciki ta bashi hanya ya fita ya tsaya daga gabanta ya dan daure fuska.

"Duk kin bata abin"

"Me na bata?" Ta tambaya da mamaki.

"Duk tsahon lokacin nan haduwarmu ta farko ta kare a koke-koke. Ni ba haka na tsara ba gaskiya."

"Haduwa ta biyu ce ko har ka manta da jiya kazo?" Tace masa.

"Yaushe zan manta bayan hatta kalar lipstick dinki na jiyan da kike ta turo min baki ta glass yana nan har yanzu a idona."

Kunya ta kamata ta dukar da kanta saboda kusancinsa da inda take tsaye.

Shi kuwa ko a jikinsa ya cigaba da magana yana kirgawa da yatsun hannunsa
"Jiya ganinki kawai nayi. Yau neman yafiyarki nayi. Gobe zan so jin yadda rayuwa ta kasance miki. Jibi kuma idan mun sake haduwa sai mu gaisa in sha Allah"

Baki bude tace "yanzu gobe ma sai kazo?"

"Harda jibi in Allah Yaso"

Bai jira cewarta ba ya fita ta bi shi a baya sai dai iyakarta bakin kofar gidansu. Tana tsaya har ya isa ga motarsa ya shiga. Bayan ya daidaita ta yadda zai fita daga layin yayi mata horn tare da dago hannu sannan ya tafi.
*****

Haj Mara anci kuka an koshi. Babawo dan da ta kwallafa rai da duk wani burinta akansa shine ya koma haka.

Abinci yake ci hankali kwance yana yi mata hira don dakinta ta shiga dashi saboda ya zama abin kallo. 'Yan uwansa ma kallonsa suke yi balle kuma masu aiki. Karin bakincikinta Yasmin da take wurin ta gama ganinsa zata kara rainata. Gata tazo da 'ya'ya maza har uku kuma wai laulayi take yi. Kwafa tayi cike da takaici.

"Babawo yanzu ni ka kyauta min kenan saboda Allah?"

"Yo...yo ma Maama did I do anything to piss ya off?"

"Piss din u....," fasa zaginsa tayi ta sauke ajiyar zuciya "kaga Babawo yanzu wannan shigar rakwacham din da kayi kai ba dan daba ba, kai ba mafarauci ba sannan ba dan bori ba da me tayi kama? Gabadaya ka fita daga hayyacinka kamar wani kwancen hauka"

"To yi min baki in haukace" ya fada cikin fada-fada yana buga cokalin hannunsa cikin plate din sannan ya ture centre table din da ta jawo masa gabansa da karfi ya tashi tsaye.

Tsoro ya bata ta tashi itama kamar zata kamo shi ta mika hannuwa sai kuma ta mayar dasu.

"Yi hakuri ka zauna kaci abinci"

"Na koshi" ya amsa tare da fita abinsa.

Hawaye ne ya taho mata ta goge jiki a sanyaye.
******

Da daddare Alh Sule yaje dakin Haj Mara rike da hannun Babawo.

Tana zaune ta rafka tagumi abin duniya ya isheta. Ganinsu tare tayi saurin gyara yanayin fuskarta don bata so Alhajin yasan batayi farincikin ganin danta ba.

Wuri suka samu suka zauna sannan Alh Sule yace "Marakisiyya kinga illar yin gaban kanki da kika yi akan yaron nan ko? Yanzu wa gari ya waya daga ni har ke?"

Cikin masifa tace "Alhaji ai baka da asara ni kadai ta shafa. Kai da ka ajiye 'ya'ya maza har uku kila ga na hudu can a ciki da waccan dadiron taka"

Gajeren murmushi yayi "duk 'yan uwana maza sun shaida wannan aure sannab bata taba haihuwa dangina mata basu je suna ba. Ke kadai ce labari yazowa a kurarren lokaci"

Babawo ne ya tashi hade da buga hannuwa a cinyoyinsa yana kade wando "ni bara na kara gaba dama na dauka zaman nawa ne"

Kallon da Alhaji ya watsa masa ne yasa shi komawa ya zauna.

Fada Alh Sule ya fara yi masa akan barin inda Haj Mara ta kaishi ya wahalar dasu wurin nema. Sannan ya dawo fada akan irin rayuwar da ya daukarwa kansa mara bullewa. Daga karshe nasiha ya koma yi da bada shawara akan idan bai chanja hali ba akwai ranar da duniya zata yi masa tofin Allah tsine kafin aje lahira.

"Kazo mu cigaba da aiki tare ni girma ya kamani so nake na huta. Idan Allah Yasa ka gane aikin sosai ma kai za ka cigaba da shugabanci a wurin"

Ba kunya Haj Mara tana murmushi tace "yanzu kayi magana Alhaji. Dama kyan da ya gaji mahaifinsa, ko ba komai shine babba cikin 'ya'yanka maza ragamar komai kamata yayi ta dawo hannunsa. Kaga da ya fara aiki sai ayi masa aure shikenan."

Tabe baki Alh Sule yayi yana girgiza kai "irinku ne mata wanda tun ranar aurenku kuke hasashen mutuwar miji a gaji dukiya. Allah shi kyauta wannan hali naki"

BB ya sake tashi don kansa har ya fara ciwo. Hayaniya idan ta wuce ta kida a gidan rawa to a kai kasuwa.

"Yo...yo Paapa ina da yarinyar da nake so magana kawai zakuyi da iyayenta"

"Alhamdulillahi kaji ma komai zai zo da sauki" cewar Haj Mara.

Shi kuma Alhaji ya fara tsoron ko cikin irin wadanda suka gama mu'amalarsu a titi ce ko wata baturiya.

Hade fuska BB yayi babu alamun wasa yace "Mawadda nake so Paapa. A nemo min ita nayi alkawarin riketa tsakani da Allah. Its a promise Paapa bazan karya ba" yana magana idanu na lumshewa.

Haj Mara tazo wuya a harzuke tace "Mawadda kuma??? Kai buhun ubanka Babawo. Kana da hankali kuwa?"

Alh Sule yayi dariya "kowa yayi zagi a kasuwa dai Marakiyya.." ya fita shima yabi bayan Babawo.

Yatsanta ta ciza don takaici. Wato da babanta Alh Sule yake saboda shine yayi sana'ar hatsi dan awo a kasuwa.

Kwanciya tayi tana ta juye-juye. Ace har yanzu Babawo bai manta da wata Mawadda ba. Ita ta dade da goge shafinsu ma a zuciyarta. Tsaki taja don da wuya idan bata yi aure ba yanzu. Yayi ya gama ya hakuri ya nemo 'yar mutumci a aura masa. Duk da tasan Alhaji yana dakinsa da matar da ya kawo hankalinta baya garesu yanzu. Burinta bai wuce kintsuwar BB ba.

A bangaren BB yana shiga daki fadawa yayi kan gadonsa yana tunani. Addu'a yake da fatan Mawadda batayi aure ba. Zai iya rantsuwa ya soma manta kamaninta sai dai ta zame masa kamar wani dafi a zuciya. Sonta yake ji a ransa burinsa kawai ya mallaketa a matsayin matar aure. Zaiyi kokarin mantar da ita duk wani bakinciki da ta kunsa a dalilinsa. Wani dan tunani yayi idan tayi aure fa.

"Kai inaaa ko tayi sai ta fito. Tawa ce ni kadai!" Ya fada yana jifa da filo daga kan gadon.

*****

Dahiru fa farincikinsa ya kasa boyuwa don duk wanda ya san shi dole ne ya gane cewa gabadaya yanayinsa ya chanja. Shigarsa gidan Bilya kenan ya samu Danlami da matarsa suna gidan su ma. Furaira na ganinsa ta kwalawa Hansa'u kira wai ta kawo masa abinci.
Chapter 31 · 0% Book details