← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 68

Sashe 44

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sallama sai da aka bashi izinin shiga sannan Dahiru ya bude kofar dakin da aka nuna masa an mayar da Qareeba.

Tana kwance Dr Tani na bata tea gefe kuma yayunta ne. Najib ya matso kusa dashi fuskarsa dauke da murmushi "Dahiru bamu da bakin gode maka. Allah Ya saka da alkhairi"

Hannu ya mika masa Dahiru ya dago nasa da yake nannade da bandeji babu halin gaisawa.

Faisal da Safwan ma duka sunyi masa godiya Dr Tani ta tambaye shi me ya sami hannun cike da kulawa. Banda 'ya'yan cikinta duk duniya babu wanda ta taba jin ya kwanta mata tamkar ita ta haife shi kamar Dahiru.

Murmushi yayi "Targade ne amma an gyara. Zazzabi ne ya rikeni ban sami dawowa ba. Yaya jikin naku?"

Sakin fuska tayi "da sauki Dahiru"

Ya mayar da kallonsa ga Qareeba da ta kafe shi da idanunta daya da rabi "Anti Qareeba ya naki jikin?"

"Da sauki. Dahiru ba don kai ba da rayuwata ta zo karshe...."

Faisal yace "shhh Sis ki dena irin wannan magana"

Kuka ta soma yi har lokacin Dahiru take kallo "you are my hero Dahiru bazan taba mantawa da kai ba. Tun da na farfado nake neman me zance idan kazo na godiya na rasa"

Murmushi Dahiru yayi ya kalleta da tausayawa "gashi kin kirani Dahiru har sau biyu, ina ganin babu sauran godiya a tsakaninmu"

"Kuskure ne Ahirin my hero nake nufi" ta sake cewa itama tana dariya.

Gabadaya dakin suka sa dariya Dr Tani tana ta jan shi da hira anyi sabon da kuma wannan karon har ranta take nufi don Dahiru yayi mata abin da dole ne ma ta kaunace shi.

Zuwan Dr Auwal hirar ta chanja zuwa karar da ya shigar da kuma neman BB da 'yan sanda suke yi. Dahiru yayi alkawarin tsaya musu shaida a duk lokacin da aka neme shi.

Yadda ya dauki zafi sosai akan lamarin ya sanya Dr Tani tunanin ko dai da gaske yana son Qareeba din ne. Idan kuwa hasashenta gaskiya ne ta kuduri niyar Dahiru ko matansa uku zata bashi 'yarta. Ashe hakan take a wurin itama Qareeban. Soyayyar da bata taba sanin ana yi ba mai zafi ita ce ta kamata akan Dahiru. Kallo daban take yi masa yanzu. Kuma kamar Dr Tani ta ta'allaka taimakon da jin zafinsa da soyayya wanda shi kuma duk yana yi ne idan ya tuna Mawadda ta taba shiga wannan halin kuma tsaninsu ta karshe da zata taimaka musu taci amanarsu a kotu. Bashi da wannan burin, tunda Allah Ya dawo masa da ita har ana kirgen kwanakin aurensu dole ne ya nuna godiyarsa ta hanyar taimakon masu bukata.

*******

Yana barin asibitin Alh Sule da Haj Mara suka iso. An nuna musu dakin suka tafi jiki a sanyaye.

Haj Mara ce a gaba ta tura kofar Dr Tani ta hayayyako mata cikin bacin rai "Marakisiyya kada ki shigo dakin nan don baki da abinda zaki fada min"

Alh Sule ya biyo bayanta ya nufi Dr Auwal ya mika masa hannu yaki mika nasa sai ma kallon banza da yake binsu dashi. Jikin Alh Sule ya sake mutuwa, da mutumcinsa da komai da guda daya ya zame masa wake daya bata gari. Bai daddara ba yace "Dacta don Allah..."

"Kalli 'yata Alh Sule. Dubi yadda Qareeba ta koma a dalilin danka"

Daga shi har Haj Mara sun tsorata da ganin Qareeba. Jikinta ya sha bandeji fuska kuwa sai kayi mata farin sani zaka ganeta saboda kumburi.

Gaban Haj Mara ya fadi har wani jiri ta soma ji saboda yadda ganin Qareeba ya tuna mata da maiaikin da ta tsani jin sunanta da labari a kanta.

Matsawa tayi jikin gadon "sannu Qareeba"

"ALLAH YA ISA ANTI MARA"

Kowa sai da ya kalli Qareeba yadda ta daga murya ta sake cewa "bazan taba yafe miki kuma ina addua duk wata masifa ta duniya ta fadawa Babawo"

Turus ta tsaya tana bin mutanen dakin da kallo "Tani kina jin Qareeba za ta yi min rashin kunya"

"Rashin kunya ta wuce wannan dan akuyan da yazo ya kaita har gadon mahaifiyarta zaiyi mata fyade? Idan baki fita daga dakin nan ba zaki ga rashin mutumci irin wanda baki taba tsammani ba"

Ja da baya tayi wai yau ita Haj Mara wadda maza da mata suke tsoro itace matar da ta rainawa wayo a baya take fadawa magana haka.

Alh Sule zai yi magana Dr Auwal yace dashi "kaga ka dauki matarka ku tafi kawai zamu hadu a kotu idan an kamo shi."

"Ba don wayarka ba ko da wasa bansan abinda yake faruwa ba Dacta kayi hakuri muyi magana"

"Babu fa abinda zaku ce da zai sa mu janye karar nan"

Haj Mara tace "Allah ko? To bari kaji in fada maka idan baku janye ba Dr Tani sai ta rasa wannan aikin da asibitin saboda shaidar karya da tayi a kotu."

Tsananin bakinciki ya kama Alh Sule "yanzu ina kokarin shawo kan matsalar kina kawo wani zancen banza daban"

Ido a soye tace "Yo me ya rage min Alhaji? Ka tsaneni ka tsani dana. Gara tun wuri na fada mata idan tana son ganin bayana ne sai dai mu ga bayan juna."

Dr Tani ta tako gabanta kamar me neman wani abu sai ji suka yi ta taske Haj Mara da mari dakin gabadaya ya dauka. Dago kai tayi a kufale Dr Tani ta sake kara mata a dayan kumatun

"Marakisiyya ni dake shege ka fasa. Da kika ganni nan ko zanyi bara na rantse da Allah sai naga karshen dan mahaukacin yaron nan naki. Kudi ne dai kike takama dashi ko? Kin dade da sanin daga gidan da na fito nafi karfin tunkaho da dukiyar gaibu dukiyar miji. Idan kin cika ki tareni gaba da gaba in kudi ne zai bada nasara a kotu kin sani na fiki, idan kuma shaidu ne to dama a tafin hannuna kike."

Tsananin mamaki da gigitar mari yasa ta rike kumatun duka biyu "ni ki ka mara?"

Dr Auwal ya dubi Alh Sule "ka fitar da matarka daga asibitin nan haka Alhaji"

Matsawa yayi daga kusa da ita kamar wata abar kyama "Ina ganin lokaci ne yayi da zanyi abinda ya dace game da ita. Marakisiyya kin tuna lokacin da na fada miki akwai ranar da zaki girbe duk tsiyar da kika shuka? "

A matukar tsorace tace "Alhaji kada ka sakeni don Allah"

"Alfarma daya zanyi miki mu koma Kaduna tare ki kwashe kayanki zama dake bashi da wani amfani sai tarin bakinciki"

Kallonsa ta jima tana yi kafin ta hade rai sosai "a gaban makiyana ka wulakanta ni me zai sa na bika, sakina nawa kayi min?"

"Babu sauran zama tsakaninmu"

Su Safwan da suke gefe suka yi zuru zuru suna kallonsu. Dr Tani ta tabe baki ta koma ta zauna sai Dr Auwal ne ya iya cewa yayi hakuri su tafi tare.

Shima harara ta buga masa ta fice kamar zata tada kura. Alh Sule ya kwantar da kai duk da yadda yake ji ya cigaba da basu hakuri "idan rufe Babawo ne zai kawo karshen fitinarsa Dacta zan baka dukkan goyon baya. Dana ne kuma wallahi ina son sa amma bazan zuba masa ido ya cigaba da lalata 'ya'yan mutane ba."

Fita yayi bai tarar da Haj Mara ba ta sami tasi ta tafi tasha. Mota daya tayi shata sai da ta zauna ta shiga kuka sosai. Dreban yana ta tambayarta ko lafiya bata tanka masa ba ya gaji ya rabu da ita.

Har gida ya kaita ta ciro kudinsa ta bashi ta shige maigadi yace ina Alhaji harara ta bashi amsa. Kayanta taje ta hada wanda zata iya hadawa a lokacin ta duka karkashin gado ta dauko kit dinta. Komai mai mahimmanci kama daga kudade, gwal da takardu suna ciki.

Daukar mutumci tayi masa saboda tasan yana da nauyi sai taji abu sakayau. Zuciyarta ta harba ta dire shi akan gado hannu na rawa ta bude. Kasa ta fadi wanwar saboda tashin hankali. Fanko haka ta same shi ko kura babu.

"BABAWO!!!!"
******

Biki ya gabato inda Haj Mama da Baba Prof suka nuna bajinta sosai. Su wannan ne bikinsu na karshe saboda Attahir ne auta. Shima kuma Dahiru shine karshen aure a nasu gidan kannensa biyu sun riga shi. Saboda karamci da dattako ko a jikin katin Mother's Eve an rubuta sunayen angwaye biyu, Attahir da Dahiru. Wannan abu yasa masa kara son mutanen da jin nauyinsu. Yadda baya gajiya da yi musu godiya da addu'a haka ma su Inna da Baffa. Su kuwa sai dai su ce da na kowa ne baka san wanda zai ji kanka ba nan gaba.

Kowane ango an bashi katunan da zai kaiwa dangin amaryarsa saboda wurin taro sai da kati ne. Babbar 'yar Baba Prof ita ta dinka musu kayan da zasu saka iri daya. Karshe Dahiru har hawaye yayi yana ta addu'ar kada Allah Ya bashi ikon cutar dasu ko daidai da kwayar zarra. Ya san yadda zamani ya canja yanzu sai ka taimaki mutum ya zame maka alakakai. Ka nufe shi da kyakkyawar zuciya idan ya sami sukuni kaine mutum na farko da zai bakantawa musamman idan naka karfin ya kare. Wani ko labarinsa ma bazaka kara ji ba likkafa taci gaba. Saboda irin wannan hidima da ake yi musu Inna da Baffa suka ce ko bayan ransu idan Dahiru ya butulcewa wannan iyali basu yafe masa ba.

Sannan fa suma ba'a barsu a baya ba. Buhun wake uku, kwandunan tumatir da tattasai da albasa wanda kila har a gama bikin ba sai sun nema ba haka suka kawo musu. Ga su gero da kabewa tuli guda. Lallai kyautatawa abar so ce kuma babban tsani na samuwar farinciki ga mai yi. Babbar bukata ka nufi Allah da kyakkyawar zuciya babu gori ga wanda aka kyautatawa kuma babu saka tsammanin za'a ramawa kura aniyarta.

Zuwa yanzu Mawadda da Nawal sun kulla zumunci da juna duk da basu taba haduwa ba amma suna waya har hotunan juna sun gani. Su ma kowacce nata dangin suna ta shiri ne domin fita kunya.
Chapter 44 · 0% Book details