← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 68

Sashe 10

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shikenan ka jira mu tattauna dai kafin ka zartar da hukunci. Na fada maka ne domin ka fara dasawa zuciyarka hakuri tun yanzu."

Bai ce mata komai ba ya tashi ya fita. Yana son iyayensa kuma a shirye yake yayi musu biyayya amma fa sai inda karfinsa ya kare akan Mawadda. Abu daya ne yake masa yawo a rai shine yadda muke saurin manta alkhairin mutum da zarar kaddara mara dadi ta same shi mu guje shi. Wannan hali namu yana daga abin da yake cire mana tausayin juna. Mun mayar da kanmu mutanen da indai jifa ya wuce kansu to ya fada kan kowa ma bamu da damuwa.
******

Wani wawan duka ta sauke mata a cinya cike da al'ajabi tace
"Ke ki bari don Manzo!"

Ummiyo tayi saurin toshe bakin Rahane aminiyarta.
"To uwar karadi yi ihu kowa yaji"

Babar Rahane tana jiyo haka ta dawo bakin tagar dakin ta labe. Yo labe da leke a wurinsu ai ba komai bane. Balle kuma taji alamun gagarumin abu ne ya faru tsakanin Ummiyo da Rahanen don da ta shigo irin gaisuwar nan mike tayi mata ta wuce dakinsu Rahanen.

Mamaki sosai a fuskar Rahane baki na rawa tace "yanzu da gaske fyade aka yiwa Mawadda? Wallashi har ta bani tausai."

Babar Rahane ta ja numfashi a tsorace tare da dafe kirji tana kara kara kunne. Nan ta jiyo Ummiyo tana cewa
"Ki bar fadi mana Rahane kada a jiyo mu. Jiya Aden Mawadda har dakin Inna tazo ta roketa a rufe maganar. Da kyar na jira wayewar gari saboda na fada miki. Kuma fa Yayanmu Dahiru ya sani don ta bayansa ma na labe. Yanzu ban sani ba ko zai aureta"

"Allah Yasa kada yace ya fasa gashi kince ma tana asibiti baiwar Allah" cewar Rahane har da 'yar kwallarta saboda tausayin Mawadda.

"Don ba yayanki bane ki ke masa mugun fata? Ni dai gaskiya bana so ya aureta. Me zaiyi da 'yar iska. Rannan naji ance duk wacca aka yiwa irin haka ita ma shikenan ta zama irinsu. Kuma garin nan kinsan kowa gudunta zaiyi azo a tsani Yayanmu Dahiru. Ha'aan"

Babar Rahane tana jin haka ta janyo abin tatar koko daga igiyar shanya a zatonta mayafi ne. Makotansu ta shiga da sauri cikin dan kankanin lokaci ta labartawa matan gidan su hudu har da karin cewa Mawaddan tana asibiti an zubar mata da ciki.

Tuni gida ya dauka mata suka fara fita waje kowacce tana son kaiwa makusanciyarta labari.

Cikin abin da bai wuce awa biyu ba maganar nan tayi yawo fiye da zato. Mata da maza manya da yara da dama sun sani tunda safiya ce. Kusan ko ina zancen ake ta yi gashi a kowacce gaba labarin ya sami karin gishiri ya tashi daga fyade wasu sun kara da ciki wasu ma sun ce haihuwa tayi. Akwai wadanda suka dora da cewa dama tun tana garin ai kallonta kawai suke yi ana cewa tana da nutsuwa su kuwa sun san tana yawace-yawacenta ne kawai. Lokacin da Dahiru ya dawo ana ta binsa da kallo da yake bai kawo za'aji zancen ba ko kadan bai kula ba.

******

Ya fito da shirin tafiya gona saboda rashin samun lokaci tun ranar da Mawadda ta dawo gari bai gama cire kubewar da ya shuka ba wanda kusan duka gonar sun gama yado mai kyau. Idan ya cire Yayansa Bilya ne yake diba akwai masu kayan miya da suke karba a Kano. Sauran kuma Inna da Ummiyo suyi aikin busarwa da dakawa akai a sayar.

Sallama suka jiyo daga waje Inna ta amsa tace ana zuwa. Ummiyo ta shiga wanka bayan ta dawo ta sha fadan Inna. Danlami dama shi ba'a saka shi a lissafi dama.

Da fatanyarsa a kafada Dahiru ya fita. Sakin fuska yayi ganin wani abokinsa Ali.

Hankali a tashe Ali yace "Dahiru ashe kuma abin da ya faru kenan. Ina shirin fita wata makociyarmu ta shigo take sanar da Fiddausi saboda ta san kawaye ne da Mawadda. Yanzu haka na fito na barta tana ta kuka."

Gaban Dahiru ya fadi da kyar ya iya cewa "me aka ce ya same ta?"

Sai kuma jikin Ali yayi sanyi a tunaninsa Dahiru bai sani ba
"To ina jin dai a gida basu sanar da kai ba saboda ansan za ka shiga damuwa. Mu bar zancen nan bari na wuce"

Tunani Dahiru ya soma na inda maganar ta fito kuma mutane nawa ne suka ji.

"Ali dakata mana ba ka fada min me kaji ba"

A dan tsorace Ali yace "ba a ji mutuwar sarki a bakina ba. Nasan su Baffa zasu sanar da kai. Sauri nake Dahiru sai mun hadu"

Bai jira cewarsa ba ya bar kofar gidan a gaggauce. Shi kuwa Dahiru sosai hankalinsa ya tashi. Balle da ya hango kanwar Inna wadda suke kira Yakumbo tana nufo gidan da sauri ita da babban danta Liti.

Tare suka shiga gidan bayan ya gaisheta tana binsa da kallon tausayawa. Sun gaisa da Inna ta dan bata rai.

"Yanzu saboda Allah magana irin wannan sai dai naji a waje? Ba don Liti ya fita siyo siga ba wani yayi masa jaje shikenan..."

Inna ta dakatar da ita itama nata gaban na faduwa "wace maganar?"

Yakumbo ta sake kallon Dahiru "zancen Mawadda mana ance anyi mata fyade wai harda ciki suna asibiti an zubar ne ko zata haihu ni ban ma gama gane zancen ba na fito"

Tafa hannuwa Inna ta soma tana sallallami "wane munafukin ne ya fito da maganar nan harda karya? Nasan dai su Haule bazasu dauki wuka su dabawa cikinsu ba. Sa'ade kuwa har dakina ta biyoni jiya tana rokon rufin asiri"

Yakumbo ta gyara zamanta "kice maganar dai gaskiya ne. Mu dai mun shiga uku duka-duka yaushe aka yiwa 'yar gidan Audu maikifi gashi zaman garin nan yazo ya gagaresu."

Inna dai har zufa ta soma yi saboda tashin hankali. Dahiru ya sami jikin bango ya jingina ransa na tafarfasa. Ummiyo tana fitowa da bokitin wanka a hannu taji Liti yana karin bayani.

"Wanda ya fada min yace wai a bakin kanwar Dahiru aka ji maganar shine duka kusan kowa a shiyarsu yaji. Ina jin haka nace to ko Ummiyo ce, ba tana kawance da yarinyar nan Rahane ba"

Da sauri Ummiyo ta lallaba ta koma bandakin tsoro ya cika ta. Amma Rahane ta cuceta yau ina zata saka kanta.

Hannu Inna ta dora a ka tana kiran ta shiga uku. Dahiru yayi fam yana cewa ina take. Suna wannan halin Inna tana yiwa Yakumbo bayanin ainihin me ya faru sai ga Baffa da Danlami.

Tun daga waje yake fada abin da ba halinsa ba yana kiran Inna. Ganin Yakumbo a gidan ya kara tabbatar masa da abin da yaji.

"Me yasa ku mata baku da hankali, babu rufin asiri sannan ba kwa tunani sam. Saboda Allah abu ya faru jiya amma har ya baza garin nan lokaci guda."

Hakuri Inna ta soma bashi yace tayi shiru kafin rai ya kara baci
"Ko inda zani ban karasa ba Danlami ya riskeni yana tambayata gaskiyar zancen da abokansa suke yi kan yarinyar Mal Fatihu. Ban gama al'ajabi ba Bilya da yake nesa ma ya kira yana tambayata. Wai kanwar matarsa ce ta kira 'yar uwar ta sanar da ita. Me yasa zaki yi min haka do Allah?" Ya kare fadan yana kallon Inna.

Duk jikinta yayi sanyi hakan ya kara konawa Dahiru rai. Wato Ummiyo ce jiya yaji motsinta shine kuma tana ji ana yiwa mahaifiyarsu fada tayi shiru.

Hanyar bandakin ya kalla sai ya ga sawu da danshi. Ta fito kenan ya fada a ransa. Baiyi wata wata ba ya fada bandakin Inna tana ya dakata sai gashi ya fito da Ummiyo da daurin zani har kirji da kuma wani da tayi lullubi dashi.

A gaban iyayen nasu ya soma sauke fushinsa a kanta inda ya fara dukanta kamar wanda aka aiko.

Baffa rabuwa yayi dasu zuciyarsa na kuna. Allah Ya sani baiyi niyyar cigaba da shirin auren Dahiru da Mawadda ba. Amma wannan rashin hankalin na Ummiyo ya janyo dole sai ya sake tunani.

Yakumbo da Inna suna ta fada amma Dahiru bai bar dukan Ummiyo ba. Da kyar Liti da Danlami suka kwaceta bayan ya tumurmusata a kasa. Tashi tayi da kyar tana kuka Baffa ya hauta da fada. Abu ya tarar mata ta rasa yadda zatayi sai hakuri take bayarwa.

Tsabar bacin rai yasa Dahiru ficewa daga gidan ya barsu da tunanin mafita don barna dai an riga anyi.

Sai can yamma ya dawo yana zuwa ya hau wanki. Kayansa masu dan dama-dama ya wanke Inna jiki duk a sabule saboda fushin Baffa tace ina zai je yake ta wanki da shiri.

"Kano zan tafi gobe wurin Yayanmu Bilya."

"Me zaka je yi Dahiru" Baffa ya tambaya.

"Kwanaki yace na sami gurbin karatu a BUK wanda ya nema min nace bana so noma zanyi. To gashi bukatarsa ta taso zan bincika idan har yanzu ban makara ba ina son inje."

"Ai gara kayi karatun kafin nan an kashe wannan gobarar ma" in ji Inna.

Girgiza kai Dahiru yayi "Inna ba zama zanje yi ba don ina dawowa idan ta fito daga asibiti nake so a daura auren sai na tafi da ita. Zan nemi aiki ko na karfi ne inayi saboda ciyar da ita da kuma karatun nawa"

Magana zata sake yi Baffa yace ya wuce abinsa Allah Ya kaimu goben.

A fusace ta juyo "Baffa yaya haka?"

"To gaya min yadda kike so ayi. Kina kallo na kasa fita saboda fargabar haduwata da Mal Fatihu saboda aika-aikar da 'yarki tayi. Kina jin ina da bakin fada masa an fasa auren yaran nan? Salon dan sauran mutumcin nawa ya karasa zubewa ko me"

Tashi tayi ta shige ciki rai a dagule. Ganin Ummiyo tayi rakube da kwaba ta mangareta kafin ta wuce "shegen surutun tsiya gashi nan zaki jawo mana jangwam haka kawai"
*****

Sai wajen taran dare Mal Fatihu suka dawo da Yaya don tun la'asar su Innarsa suka dawo. An baro Ade da Iya a asibitin.

Yau ma sauran yaransu suna gidan kakaninsu.
Chapter 10 · 0% Book details