← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 68

Sashe 21

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ku sakeni ragwaye" yace sannan ya dan yunkura amma kansa ne kawai ya motsa. Sake yunkurin yayi yaji da gaske bazai iya ba. Zuciyarsa ta buga da karfi don ya tsorata ya daure yace "Haule jeki ki kira min likita na kasa motsa ko ina banda wuyana"

Bai karasa ba ta fita a guje yayin da Ade ta soma kuka tazo tana cewa ya daure ya tashi. Likitan ya zo sai ga Iya da Inna tare da Mawadda. Gefe suka matsa ya dan dudduba shi sannan ya juyo yana fuskantarsu.

"Tun dazu da aka kawo shi munyi zargin haka amma bamu da tabbas sai yanzu da ya tashi. Kayi hakuri Malam ka sami shanyewar barin jiki"

"Innalliahi wa inna ilaihi raji'un" suka shiga fada wasu na salati. Kan kace kwabo sai kuka domin wannan abu ya dokesu ba kadan ba.

Likitan ya rinka basu hakuri sannan yace idan har zasu rinka kawo shi gashi ko bayan sallama to hakika bangaren hagunsa zai sami lafiya ko bai dawo daidai ba zaiji sauki.

Fita yayi ya barsu da jimami da kuka. Innar Fatihu ta kira kaninsa guda namiji da yake aikin dreba. Baya gari duk abinda akeyi a lokacin sunyi tafiya da ubangidansa tana kuka ta fada masa. Hankalinsa ya tashi ya kira mijin kanwarsu daya da yake da waya yace aje gidansu a sanar da Malam.

Kamar an tsikari Ade ta soma juye juye tana cewa ina 'yarinyar nan ne da ta farga Mawadda bata wurin. Kowa kuma sai lokacin ya lura Baba ya daure yace ta fita ta nemota.

Waje tayi kaf wurin reception din bata nan. Kofar shigowar ta kalla sannan ta fita, dubawar farko ta hangota tayi hanyar gate.

Kwala mata kira tayi iyakar karfinta amma Mawadda bata tsaya ba. Ganin tsayuwa bazata kai mata ba ta bita da sauri. Shima hakan baiyi ba don tafiya kawai take kai tsaya dole Ade tasa gudu tana kiranta. Tana zuwa gate Mawadda tayi gaba ta hau titi bata kallon gabanta. Kusan ma bata san me take yi ba da ya wuce kukan zuci na jin lalurar da ta kama mahaifinta.

Motoci ne suka taho suna ta horn da taka burki ganinta a tsakar titi. Wata mota ta taho da gudu mutumin sai taka burki yake abu yaki yi. Ade hannuwa ta dora a kanta kawai ta rufe ido tana kuka don ta saddakar sai an bigeta kawai.

Wani mugun burki mai motar ya sake ja tayoyin suka yi wata kara ya karkata motar ya daki jakin babangida. A fusace ya fito jibgege mutum yasha babbar riga yana zuwa ya dauketa da mari har biyu a inda tayi mutuwar tsaye.

"Baki da hankali ne zaki zo tsakiyar titi ki nemi jaza min masifa?"

Mutanen da suke wurin kowa ya tsorata aka soma zaginta wasu na cewa mahaukaciya ce kila. Kasa cewa komai tayi sai kalle kalle take yi kamar wadda ta tashi daga bacci. Ade ta taho ta kama hannunta tana bawa mutumin hakuri.

Yadda ya gansu cikin tsumma yasan babu abinda zai tsinta a tare dasu idan ma yaki hakura.

"Tunda babu abinda ya faru kuje kawai Allah Ya kiyaye gaba"

Tana ta yi masa godiya ta kama hannunta suka koma ciki. Kafin su karasa ta tsaya daidai jikin wata bishiya ta riko hannayen Mawadda.

"Kashe kanki zakiyi ki tona min asiri ko kuwa so kike muma mu mutu?"

Girgiza kai tayi tana hawaye "kinga yadda Baba ya koma saboda ni"

"Kaddara ce, idan kika kashe kanki ni dashi bazamj taba yafe miki ba kamar yadda Allah bazai yafe miki ba. Kiyi hakuri mu barwa Allah komai muna nan dake watarana mutanen nan sai sun dandani fiye da abinda suka yi mana"

Su biyun duk kuka suke suka koma ciki. Jikin Baba Mawadda ta fada tana kuka yana rarrashinta.
******

Karfe uku saura a kotun ta yiwa Dahiru sai dai ya tarar an gama shari'ar. Da tambaya wani ya sanar dashi yadda aka kare ransa ya baci ga tashin hankalin ance masa Baba ya fadi ba'a sani ba ko yana da rai ko babu.

Rashin sanin ina zai nufa daga nan ya koma gida ranar haka ya wuni ko makaranta bai samu yaje ba yana jira zuwa yamma ya kira Baffa a bawa Danlami suyi magana.

*****

*Bayan sati uku*

A daddafe Mal Fatihu yayi kwana tara a asibitin aka sallamosu. Kudin kwanciya da na magunguna yana neman fin karfinsu dole suka nemi sallama da gaggawa. Cikin ikon Allah barin hagunsa ya mike kamar yadda likitoci suka sanar dasu sai dai nauyin bangaren daman da kuma rashin sabo yasa har yanzu sai ya dafa wani yake iya tafiyar kirki. Bangaren daman gabadaya ba kwari hannu da kafa duk sun shanye don ma an kaishi asibiti da wurwuri.

Kowa a gidan yanzu hidimarsa yake yi. Hatta manyan 'ya'yan suna zuwa kusan kullum. Ya kasa cire damuwa a ransa ganin Mawadda bata da aiki sai kuka. Makota baifi mutum uku bane maza da mata suka zo dubiya. Zantuka kawai ke yawo a gari cewa Mawadda ta gama yawonta ne a Kaduna tsoron kada asirinta ya tonu tunda biki ya gabato suka kirkiri wannan abu ita da iyayenta bayan ta dawo da cikin da suka zubar a asibitin Bebeji. Wannan magana ita tafi kowacce karbuwa a garin shiyasa iyalin gidan suka zama abin kyama abin Allah wadai. Wani karin bakincikin shine da ake cewa sun so cin kudin mutanen da tayi aiki a gidansu ne amma bukata bata biya ba kunya da dogon buri irin na Mal Fatihu da kuma hakkin yaron da suka yiwa sharri ne suka kwantar dashi.

Kukan da iyalin gidan suka yi na zahiri da na zuci bazai kwatantu ba.
*****

"Ki dena kuka Jamila kina kara karyar min da zuciya"

Goyonta ta gyara sannan ta goge hawayen da ya zubo mata "Allah kadai Yasan halin da Baba zai shiga idan naje musu da maganar sakin nan"

Katuwar jakar bagco din da ta hado kayanta ya cicciba ya dora a kansa sannan ya duka ya dauki wata ghana mustgo suka fito daga dakin.

Mahaifiyarsa tana tsaye tana jiransu tace "gayyar na gayyaro dangin yawo a tafi inda aka fi wayo. Halisa kuma kina yayeta zanzo da kaina na karbeta kafin a koya mata mugun hali"

Jamila bata iya cewa komai ba ta fita mijinta na biye da ita da kaya niki-niki. Da kyar da sudin goshi ya lallaba mamansa ta barshi ya kai mata kayanta don tace ko kofar gidan ta sake zuwa Ja'e zata tsinewa. Yanzu ma da batun tsinuwar tasa ya saki matarsa duk kuwa da son da yake mata.

Cikin rana mai zafi suka isa gidan. Da kuka ta shiga gida su Yaya suka bita da kallo. Goyon ta kwance ta mikawa Mawadda wadda ta tashi tun shigowarta sannan tace tare da Ja'e suke.

Yana shigowa da kaya hankalin iyayen ya tashi sun san kwanan zancen. Hakuri yayi ta bawa su Baba da alkawarin yana komawa wurin aikin kafintansa a Dutse zai nemi gida ko daki daya ne ya dawo ya dauketa.

Gani yayi Mal.Fatihu yana hawaye shima ya fara yana dada bashi hakuri "don Allah kada ku bari tayi saurayi wallahi zan dawo komai dadewa. Ni na mayar da ita ma tun yanzu a gabanku"

Zuciyar Mawadda kamar ta fashe. Banda abubuwa da suke ta faruwa kuma harda kashewa yayarta aure.

Gashi dai ita ce aka cuta kuma itan dai ake kyama. Danginta sune suke ganin bakinciki da bacin rai duk akan abinda BB yayi mata. Jamila ta rungume suka shiga daki suna kuka ba mai rarrashin wata.

Bayan tafiyar Ja'e Baba ya kirasu yana musu nasiha akan ko bayan ransa su rike juna da zuciya daya kada suyi wasa da zumunci.

"Wannan abu da ya faru jarabawa ce ta imaninmu. Kuyi hakuri wata rana ko ina nan ko bana nan zaku ga farincikin rayuwa. Sakayya akan wadannan mutane ko a duniya ko lahira sai sun koka"

Zantukan Baba suka sake taba Mawadda tana cikin kuka kawai ta fadi a wurin. Hakan ya sake ruda gidan ba babba ba yaro kowa ido yayi ja suna zubar da hawaye. A haka Iya, Ade da Innar Fatihu suka samesu. Basu dade ba 'yan uwan Baba suka zo kowa dai basu baki yake akan hakuri da wannan iftila'i da ya fada musu.
*****

Zaune take tana danna remote tana chanja tasha wayarta tayi kara a karo na barkatai. Tsaki taja sannan ta dauka a wulakance.

"Likita bokan Turai"

Ajiyar zuciya Dr Tani tayi "haba Marakisiyya shiru-shiru sati uku kusan kullum sai nayi miki waya ba'a dauka. Qareeba ma tace Babawo baya kira baya amsa nata kiran. Me yake faruwa ne?" Ta fada cike da damuwa da fargabar ko sun fasa ne. Qareeba har wata rama ta soma saboda masoyi Man baya kiranta. Yanzu ma tana kusa da Mummynta ita ke kara takura mata akan kiran.

Haj Mara ta yamutsa fuska kafin kuma ta gyara murya ta soma tari.

"'Yar uwa ciwo ya sani gaba sai dai a kwantar a tayar. Daga ni har Babawo ina muka ga karfin waya. Shi yake wuni dani tare da 'yan uwansa"

Hankalin Dr Tani in yayi dubu fa ya tashi "me yasa baki sa sun fada min ba? Ina Kano ina Kaduna da tuni nazo."

Ita fa Haj Mara gaskiya Qareeba ce bata so ko kadan. Yanayin maganarta na shagwaba da kuma shirme yarinyar ta fice mata a rai. Daurewa tayi tace mata ba sai tazo ba yau taji sauki sosai.

"Allah Ya kara sauki. Uhmm nace ba, wai yaushe su Alhaji zasu zo ayi maganar auren. Nasa Daddy ya sanar da 'yan uwansu da abokai don kada suji date bazata gara kowa ya zama cikin shiri."

Dariya Haj Mara tayi ta ganin wautar Dr Tani. Ita fa ba don ta santa ba sarai idan ance mata ta shiga aji tayi karatu na aikin lafiya sai ta karyata. Ba tantama 'ya'yanta tsotso halinta suka yi a jikinta.

"Kada ki damu yana dawowa tare ma zamu zo yayi miki godiya sannan ayi magana sosai. Ya tsaya a Lagos ne zai jira kayansa su iso"
Chapter 21 · 0% Book details