← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 68

Sashe 53

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Akwai wani abin ne naga kin tsaya ni kuma kunyarki nake ji bazan iya cire kaya na shiga..."

Rasa ma me zata ce masa tayi tsabar mamaki. Saboda Allah me tayi ko tace da zaisa ya fadi wannan magana har wani sunne kai yake yi. Kuma shi ya tsayar da ita da bayanin ta jira ruwan zafi. Kwafa tayi ta fita tana auno me zata yi masa ta rama.

Sai da ya ga fitarta ya kwashe da dariyar yadda ta kwalalo idanu da yace yana jin kunyarta. Ko babu komai tunda suka shigo gidan bai yi mata wani abu da zai bata tsoro ba sai ma tsokanarta da yake yi.
******

Tamkar Dr Tani ta zuba ruwa a kasa ta sha lokacin da Dr Auwal ya gama waya da DPO din station din da suka kai karar BB yace sunyi magana da abokan aikinsu yanzu haka BB yana Bompai station.

Babu bata lokaci ta dannawa Haj Mara call tana jin ina ma za ta iya ganin yanayin da zata shiga idan taji wannan labari.

Haj Mara tana tare da wani Agent wanda ta bawa passport dinta da na BB akan zaiyi kokarin nemo musu visa China. Duk tsiya tasan akwai kudi a hannun Babawo ga dukiyarta da ya kwashe. Lallaba shi zata yi su hada komai nasu su bar kasar. Da wane idon za ta kalli 'yan uwanta idan ta koma gida. Sannan abin takaici yaranta mata wai jiya suka taru suka zo yi mata nasiha akan ta bawa Alh Sule hakuri akan laifukan da tayi masa kuma ta fadi ina BB yake a dawo dashi. Kaca-kaca tayi musu dukkansu tace basa kaunarta.

Yau dai gashi ta bada miliyan uku cikin kudin gidan Alh Sule da ta sayar wai kudin visa da ticket.

Da murmushi ta dauki wayar Dr Tani "yau kuma an tuna dani ne ko batan kai kika yi?"

"Haj Marakisiyya kenan gaisheki na bugu yi" tace cikin gatse.

Ta san da biyu ta ce hakan ta tabe baki "Ko ma dai meye sai a dena bibiyata haka. Ni da dana shirin bar muku kasar muke yi sai ku karata ke da 'yarki. Don Allah kafin mu dawo ki aurawa Qareeba mijin kece raini"

"Adana damuwarki akan annobar danki ba Qareeba ba. Na bugu ne albarkacin amintar mu ta baya in fara fada miki BB yana hannun 'yan sanda an kama shi ya sace amarya Mawadda Fatihu ina fata baki manta ta ba."

Cikin Haj Mara ya bada wani sauti ta soma cewa karya ne barazana ce kawai Dr Tani ta bugo tayi mata. Har da karin cewa Babawo a gida ta baro shi yana bacci saboda kawai ta tabbatar.

Dr Tani dariya tayi sosai " su Mara ashe kema ki kan taba kazzibu, kodayake na tuna kin kware a wannan fannin. Mu dai munyi matukar sa'a case din za'a mika shi ga wata Alkali da ta tsani masu fyade sosai bata musu sassauci. Sai ku fara shiri irin naku na masu kudi"

Sakato Haj Mara tayi da waya a hannu kafin ta kira Alh Sule ta soma kuka ta fada masa.

"Allah Yasa sanadin shiriyarsa ne" ya bata amsa.

"Zaman gidan yarin?"

"Kinga ki rufawa kanki asiri ki bari a hukunta shi kafin lokaci ya kure. Ke bakya tsoron idan ya laluba ya rasa wadda zai saukewa rashin mutumcinsa kan wa zai dawo?"

A tsorace tace "kan wa zai dawo?"

"Nima ban sani ba" ya bata amsa a dakile sannan ya kira Dr Auwal.

Ya sanar dashi iya abinda suka ji yayi masa godiya da alkawarin a ranar zai taho Kanon. Haj Mara ma gida taje ta shirya ta kira dreba yace Alhaji yace kada ya sake janta a mota. Ta kira ta gama masifarta dole ta hakura don yaki amincewa. Wani yaro ta kira dan 'yar uwarta da kyar ya amince zai tukata zuwa Kano ta biya shi.

******

Daga masallaci bayan su Dahiru sunyi sallar la'asar Attahir ya kula da yadda yake yarfe hannu.

"Ka sake fama hannun nan ko?"

Kallon babban yatsansa yayi babu alamun sacewa ga ciwo.

"Ina jin bai gyaru bane"

"Kana sakaci dashi dai. Ko muje a sake duba maka?"

Ba don yaso ba Attahir ya matsa masa sai an sake dubawa kada ciwon ya koma wani abin daban.

"Bari na fadawa Mawadda babu waya a hannunta"

Yayi dariya "Nima ba tafiya zanyi ba banje na fadawa amaryata ba. Kasan mu ne da amarci, mai hannu daya sai dai jinya"
******

Mawadda bata jin ta taba yin wanka taji dadin jikinta kamar yau. Ta jima tana sake ruwa sai da taji mai zafin ya fara karewa ta hakura ta fito.

Ta gama shafa mai da feshe feshen turare tayi kwalliya da kayan da aka jere akan madubin ta laluba dakunan kaf babu akwatunan kayanta sai na Dahiru. Salati ta shiga yi ga dukkan alamu bayan dauketa da akayi jiya kayanta da aka ce sai za'a kaita zasu tafi dasu an mayar gida.

Ta kalli wadanda ta cire ita kanta kyamarsu take yi duk wahalar nan dasu tayi harda zama a kasan bandakin gidan da aka kaita jiya. Ga lokacin la'asar na neman wucewa har hudu rabi tayi. Da kunya ta tambayi Nawal kuma babu wayar kiran gida.

Bata da wani zabi dole taje gaban akwatunan Dahiru ta shiga daga kaya tana kallon kofa kada ya shigo sannan kayan kansu kunyarsu take ji. Wata shirt ta samu yellow da rubutun baki a tsakiya tayi sauri ta zura tana kamshinsa. Ji tayi kamar shine da kansa a jikinta tayi murmushi sannan ta cigaba da bincike. Wani wando ta samu ash kamar na sanyi a gaggauce ta saka saboda ta ji kamar motsin kofa.

A bayan kofar dakin ta labe gabanta sai faduwa yake. Yana daga labulen ya ga akwatunansa a bude duka bayan kuma ko wanda ya dauki kayan da yasa yasan ya rufe shi.

Shiga cikin dakin yayi bai ganta ba kuma kofar toilet bata rufe sosai ba yasan bata ciki. Ta mudubi ya hangota tsaye sanye da kayansa da suka yi mata burum-burum abin dariya amma kuma tayi masa kyau. Shagala yayi da kallonta har suka hada ido ta mudubin.

Ya shafa kansa da hannu daya sannan ya bita bayan kofar ya matseta babu wurin fita. Mutsu-mutsu ta soma yi tana son barin wurin saboda irin tsayuwar da suka yi motsi kadan zai kara ta fada kirjinsa.

Dukawa yayi daidai kunnenta har tana jin sautin numfashinsa tayi mutuwar tsaye yace "shhhhh kada su kama mu"

"Su wa?" Ta fada a tsorace

"Ke da na gani a bakin kofa ai ke zan tambaya"

Takaici ne ya kamata kamar tayi kuka ta tura kofar da kafarta ta kuwa koma ta kulle da kanta.

"Ya zaki tona mana asiri" yace yana waigawa kamar me neman wani abu.

"Yayanmu ni fa saboda kai na buya."

"Au, tuba nake Matarmu koma ban ganki ba" ya sake jawo kofar yadda ya ganta tana tsaye tana cika tana batsewa jin ya fara cewa "Mawadda, kina ina?"

Turo kofar ta sake yi harda guntun hawayenta ta soma shagwabar da bata san daga ina ta zo ba tana cije lebe "ni wallahi ba haka ake yi ba"

Juya fuska yayi kamar wanda ya shiga tashin hankali "ba haka ake me ba?"

Ta turo baki tana harararsa "bayan ba haka ake yiwa amare ba. Ni sai wasu abubuwa kake yi min kamar ba amarya ba"

"To Mawadda fada min yaya ake yiwa amaren nima nayi miki kinji" ya kashe mata ido.

Kunya taji ta dauko mayafinta ta yafa "ni sallah zanyi"

"Babu damuwa idan na dawo sai ki fada min yadda ake yi."

"Fita za ka sake yi?" A tsorace tayi maganar ya dago mata hannunsa mai targaden da ya gagara warkewa.

"Gyara na uku zani kuma wallahi akwai zafi. Amma bazanyi kuka ba kada Attahir ya baki labari. Daga can zamu biya mu taho miki da kayanki kada ki buda min nawa"

Ya kare da tsokana saboda yadda ya ga tana kallon hannun da tausayawa.

Hararsa ta fara yi sai kuma tayi masa addua ya fita.

Har akayi magrib basu dawo ba ta gama leken ko ina a gidan ta rasa abinyi ga wuta ba'a jona tv ba. Amarya da take tarewa da jamaa ko da daddare yadda lokacin bazai dameta ba ita ta shiga gidanta da rana tsaka gagal. Allah Ya isa ta makawa BB tana jiran ranar shiga kotu.
*****

Gyaran yau yafi na kullum ba karamar wuya Dahiru ya sha ba mutumin yayi ta masa fadan sakaci. Kasa magana yayi a mota da suka je daukan kayan Mawadda wanda har su Saifullahi sun gama loda su a tasi ko fita daga motar bai iya yi ba suka dawo dasu tasu.

Da yake tun a hanyar zuwa wurin gyaran Attahir yace masa yakamata su tsaya siyan nama kada su jewa amarensu haka shiyasa a hanyarsu ta dawowa yace su tsaya duk da Attahir din yaso su hakura.

Ba su suka koma gida ba sai takwas da rabi har anyi isha. Akwatunan Mawadda har bakin kofa Attahir ya hau masa da biyu sauran Dahiru yace sai da safe.

Tana jiyo su suka yi sallama ta tashi daga kwanciyar da tayi akan doguwar kujera ta zauna tana gyara mayafi.

Yana shigowa ta ga hannun nasa an daure da farin kyalle. Sannu ta rinka yi masa akwatunan ma ita ta ja kayanta daki.

A zaune ta dawo ta same shi yayi shiru azabar hannu ta ishe shi.

"Yayanmu ko zaka yi wanka sai ka kwanta"

Ledar naman ya mika mata yana magana da kyar saboda wani irin ciwon kai da zazzabi da suka rufar masa "bani ruwa na siyo pain reliever idan nasha sai nayi wankan"

Da sauri taje ta dauko ruwa da aka jere mata su da lemuka a kasan kitchen kafin ta samar musu wurin zama.

Yana sha ya shiga daki bai dade ba ya kirata.

"Yanzu dai nine kanin kece yayar"

"Me aka yi?"

Ya nuna kayansa "riga kawai zaki cire min "

Tace "kawai ne ma"

"Ki tausaya min bazan iya da hannun nan ba ina tsoron famawa"

Wannan daren amarcin nata dai bazata taba manta dashi ba ta ayyana a ranta. A hankali tace
"Ba ka jin kunyata to?"
Chapter 53 · 0% Book details