← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 68

Sashe 45

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anje anyi jeren Mawadda kayanta babu karanta babu karya. Duk wani abu da ya kamata iyaye su yiwa 'yarsu mace nata iyayen sun kamanta. Idan ka duba 'yan uwanta dole kace Mawadda ta wuce zarra domin kuwa ita kusan da biyu ake mata komai. Wanda ya auri 'yarka da duniya take gudu saboda laifin da bai zama nata ba ya cancanci godiya. A wurinsu kuwa godiya idan ta wuce ja wa 'yarsu kunne akan ladabi da biyayya to fa sai fita kunyar juna su nunawa duniya bata wulakanta ba ko da aka juya mata baya Allah Ya tsare bayinSa.

Katin daurin aure bugun farko sunan wani masallaci a nan unguwar tasu aka saka. Sai kuma abin dadi abin mamaki kanin Mal Fatihu yazo gidan tare da wasu dattawa su uku da Maigari ya wakilta akan ya bada umarnin aje fadarsa a tsakiyar garin Tariwa a daurawa Mawadda da Dahiru aure. Suna fadin sakon Baba yasa kuka.

Guda cikin 'yan aiken yace "Mal Fatihu nayi zaton zaka yi farinciki da wannan abu"

Hankici yasa yana goge ido yana murmushi "Mal Uba burina ne ya cika. Ban damu da auren Rafi'a da nayi a nan ba. Amma kaga Mawadda, saboda Mawadda kowa ya tsanemu har ana ikirarin cinnawa gidana wuta. Saboda ita aka yi mana iyaka da mahaifarmu mu duka. Yau gashi saboda ita zamu koma. Kullum kukanta idan ta tuna da gida shine ta janyo an rabamu da 'yan uwanmu tana ganin ita ce silar komai."

Wani mai suna Muntari yace "ka godewa Allah kuma ka yafe mana. Maigari yace shine zai yiwa amarya walicci idan ka amince domin dinke barakar da aka samu a baya"

Shi kuwa Mal.Fatihu idan ba yasha giyar wake ba me zai cewa Maigarinsu. Mutumin da ya ceci rayuwarsu kuma ya basu muhalli harda yafe kudin haya na wata shida. Abinci yasa aka dafa musu aka karramasu karshe sannan yace a sanarwa Maigari ya bashi wuka da nama. Alfarma daya yake nema akwai dan uwan Dahiru wato Attahir da za'a fara daura nasa auren a ranar. Suna son a kara kamar awa hudu ko zuwa azahar ne ayi na Mawadda saboda kowa ya sami halarta.

Baki na tafiya ya sanar da iyalinsa. Kowa kuka musamman Innarsa wadda ta tuno rabonta da garin tunda ta fita takabar Malam mahaifinsa.

Daki Mawadda ta shige tayi sujjadar godiya ga Allah Madaukakin Sarki. Wayar Dahiru ta kira cike da zumudi ta fada masa.

"Zan ajiye miki tukwici babba saboda na fiki farinciki. Burina dama na nunawa 'yan garinmu ina son Mawadda duk runtsi duk wuya"

"Nima ina son Dahiru duk runtsi duk wuya"

Wayar ya kankame kamar ita ce a gabansa "maimaita don Allah"

Tana murmushi tace "Me zan maimaita?"

"Mawadda manaaaa pleaseeee" yace yana jan kowane harafi a kasalance

Mawadda sai da taji bugun zuciyarta ya karu ta daure tace "Yayanmu mata ne ke shagwaba fa a iya sanina. Amma kai naga alama Inna tasha fama."

"Gara ma ki shirya tarihi yazo min ance kyuya ce dani da son jiki."

"Kada ka damu bazan rinka saka ka aiki ba kasha zamanka da son jikinka"

"Assha, ba kya ganewa. Son jiki fa irin wanda zanyi ta makale miki dinnan. Duk inda ki ka zauna ina kwance a jikinki"

Bata san Dahiru ya kware a iya bata kunya ba sai yanzu. Ta dan cije lebe tana tunani sannan tace
"Ban ma san me kake cewa ba. Kasan nakan kurmance lokaci zuwa lokaci sai abinda kunnen ya ga dama yake ji....hello, hello, Yayanmu bana ji ka sake kira"

Yana dariya yace "idan ki ka ajiye wayar nan zamu yi fada Mawadda. Ki saurareni kawai ki tsinci na tsinta ki bani amsa"

Turo baki tayi da nata salon shagwabar
"me yasa ma na kira ka ne?"

"Soyayya mana. Ina yi miki kallon wata saliha ashe ashe" yace yana tsokanarta.

"Ashe me? Yanzu ni ba saliha bace?"

"Ban ce ba. Amma fada min gaskiya me kika fi so game dani uhmm?"

Tsuke bakinta tayi tana tunanin rayuwarta dashi tun a Tariwa har yanzu.

"Yayanmu babu abinda bana so game da kai. Kayi abinda babu wanda yayi min irinsa a duniya banda iyaye da 'yan uwa. Matsayinka naka ne kai kadai. Allah Ya bani ikon zama da kai da amana"

Yaji dadin kalamanta sosai. Jan hanci tayi ya gane kuka take yi "kefa kin iya bata abu. Muna hirarmu mai dadi zaki soma kuka."

Kukan ta cigaba tace "na dade ina son fada maka hakan ne ban samu dama ba sai yau"

"Baki sani ba ai Mawadda, irin wannan jira akeyi sai an kai amarya ya rage mu biyu sai ki fada kina kuka ni kuma na sami damar daukanki na rungume"

"Kurmanci, kurmanci ya sauko Yayanmu bana ji bana ji" tace tana jin wata irin kunyarsa ta katse wayar tana jiyo dariyarsa.

Sumbatar wayar tasa yayi yace "saura kwana hudu."
******

BB ya kalli wayar da yayi jifa da ita rai a bace ya tashi yaje inda ta fadi ta tarwatse ya rinka dukanta da kwaftatareren boot dinsa irin na 'yan kwayar Amurka.

Ya dago kai ya kalli Danmani wanda jikinsa ya soma bari. Duk takadarancinsu basu taba ganin hodar iblis ba balle su sha. Amma wannan gidan samari ne da 'yan mata 'ya'yan masu kudi kuma musulmai suke ta busa hayaki suna shanta.

Idanun BB a birkice ya danko wuyansa yana wani shafa masa gefen fuska a hankali idanunsa na rufewa don kansu.

"Ya kaga Mawaddata da kaje? Tayi min kyau kamar na lasheta a hoton kawai. Amma wannan arnen mutumin me yake yi tare da ita? Ko dama kasan harda shi nake nema?"

Danmani ya girgiza kai "ban sani ba yallabai amma tunda kana nemansa sai na binciko maka ko yaya suke"

BB ya sake shi jikinsa babu kwari kwaya ta fara dibansa "haka ne sannan ka binciko min wane kafirin ne zai aure min mata. Kaga hotonta ya kamata nayi ta kallo yanzu amma tunda ka hado ta da wani kasa na fasa wayar"

"Tuba nake yanzu zan sake zuwa na samu wasu"

BB yayi dariya ya mika masa wayar da yake amfani da ita bayan ya canja sim.
"Ka ciko min wannan da hotunanta masu kyau kaji. Mawadda zata kasheni da kyaunta...hakurina ya soma karewa I NEED HER" ya kare cikin karaji.
******

Karfe takwas ta wuce ana kiran sallar Isha Mawadda da Bushra 'yar yayarta Hasiya mai kimanin shekaru goma sha biyu suka sauka daga adaidaita sahu daga bakin titi. Dreban da suka tsadance tun a gidan Anti Zahra wadda ita ke yi mata gyaran jiki ya amince zai shiga dasu har ciki. Amma yana ganin wasu mata da yawa yace su sauka ya fasa. Dama gashi ana ta mata waya cewa dare yayi. Yau aka gama gyaran jikin da jan lalle. Da safe kafin lokacin kamu za'ayi mata baki.

Fita suka yi suna hirar da Bushra ce take ta surutunta Mawadda tana dariya.

Daga nesa Danmani ya hangota saboda akwai haske duk da babu wuta gidaje da dama sun kunna inji. Layin babu mutane sosai an shiga masallaci.

Sauri yayi ya iso gabansu yace "Mawadda dan dakata mana"

Gaba na faduwa suka tsaya ita da Bushra. Gefensa suka yi niyar rabewa su wuce ya nuna musu wukar dake makale a gefen wandonsa.

"Ki tsaya kawai ba wata tsiyar zan miki ba, Oga hotunanki kawai yake so"

"Oga? Hoto?? Kana da hankali kuwa???" ta daure tace tana kankame hannun Bushra.

Janyo Bushran yayi ya manna mata wukar a gefen ciki. Mawadda ta rasa yadda zata yi sai kuka da roko.

"Kinga idan kika daga murya har mutane suka taru bazan bar yarinyar nan ba sai na burma mata wukar nan Yasin. Ungo ni ki kashe selfie kamar kala goma ki bani kafin a idar da sallah"

Wannan wace sabuwar masifar ce kuma tace tana hawaye. Jikinta ko'ina yana rawa haka ta karba ta fara dauka. Shake Bushra yayi yace ta saki fuska ta dena kuka.

Bushra taji wuya tace "Anti kiyi murmushi"

Mawadda na kuka tace "To don Allah kada kayi mata komai."

Ita kanta bata san nawa ta dauka ba sai dai zuciyarta tamkar ta fito ta baki don bakinciki da tsoro. Numfashinta har neman daukewa yake. Rayuwar Bushra take dubawa kawai da take hannun wannan mahaukacin.

Sallama yaji liman yayi ya fizge wayar ya hankada Bushra kan ta suka fadi tare. Sai da Bushra ce kadai ta tashi Mawadda kokawa take da numfashi. Duhu ya mamaye idanunta zuciyarta kamar an daddaure.

Bushra na ganin yadda take sandarewa ta soma kuka tana cewa ta tashi wayarta dake cikin purse ta soma kara Dahiru ya kira.

Bushra na dauka ko suna bata gani ba cikin kuka tace "kuzo Anti ta mutu"

A wurin ta yar da wayar maza suka taru a kansu ana cewa me ya sameta.

Kusan dakika talatin Dahiru yana rike da wayar kwakwalwarsa ta toshe ya kasa gane me yaji yanzu.

[31/01 9:36 am] Batuul Mamman: *GUMIN HALAK...*💰19

*Batul Mamman*💖

Cikin kankanin lokaci jama'a sun fara taruwa. Marwanu da Saifullahi sun fito daga masallacin suka hango taron mutane suka je. Mawadda da Bushra suka gani nan da nan suka daukota suka yi gida ana ta jajanta musu. Danmani yana cikin masu jajen don bai bar wurin ba har aka tafi da ita.

A tsakar gida aka shimfideta Yaya ta rinka shafa mata ruwa a fuska. Ade tayi gefe tana matsar kwalla. Bushra tana kuka ta fada musu gamon da suka yi a kasan layi kowa sai al'ajabin wannan abu yake yi. Da kuka mai cin rai Mawadda ta bude ido ana ta bata baki amma kamar suna zuga ta ne. Mutum baka san shi ba baka taba ganinsa ba kawai ya tsareka yace ka dauki hotunan kanka a wayarsa. Wannan abu da ban mamaki yake. Su Marwanu harda Baba waje suka yi da iya kwatancen da Bushra tayi na mutumin suna nemansa.

Shigowar mota layin a guje yasa kowa kallonta. A gaban gidan Dahiru yayi parking ya fito da sauri ko kashe motar baiyi ba saboda yadda ya ga su Baba da maza da yawa ana ta kai kawo a wurin.

Gwiwoyinsa ne suka yi sanyi duk taku daya tamkar yana yi a iska sai bin mutane yake da kallo.
Chapter 45 · 0% Book details