← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 68

Sashe 22

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dadi kamar ya kashe Dr Tani tana ta godiya kamar ta ari baki. Ita kuma Haj Mara sai lokacin aka tayar mata da bacin ranta. Alhaji yanzu ya fita harkarta ba waya ba text. Idan ta kira kullum cikin aiki yake baya sauraronta. Abinda bata sani ba shine sati biyu da suka wuce da ya dawo daga China ya wuce Birnin Kebbi inda aka daura aurensa da wata bazawara sakin wawa suna can Lagos ana cin amarci.
*****

Kwanaki na ta tafiya Dahiru ya fuskanci karatunsa sosai sannan yana kokari bangaren aikinsa don kada ya sami matsala a kore shi ya rasa abin tallafin kansa.

Ranar da akayi albashi yana jiran har na wancan watan amma dubu shabiyu Dr Tani ta bashi. Farinciki ya cika shi yana karba ya kirga ya ga babu dubu hudu a kai.

Dago kai yayi zai mata magana sai ya fasa. Itama daure fuska tayi

"Naji baka ce komai ba. Dubu hudu da ya hau kai nice na cire kudin sabulu. Na kula ashe kullum kayi mana wanki kana tsoma naka kayan a sauran ruwan kumfar. To wannan ba komai bane face ha'inci tunda ba haka mukayi da kai ba. Idan kana son wanki a gidan nan sai ka rinka siyo sabulunka da ruwa. Sannan igiyata ba wurin da zamu rinka hada shanya da mai wanki bane ina fata ka fahimta"

"Sosai" kawai yace ya juya yana jin wani irin bakinciki. Shi kadai yasan yadda yake maneji a makaranta amma wannan bai dameshi ba kamar halin karanta irin na masu gidan nan.

Dama lokacin tashinsa yayi tunda lahadi ce sai kawai ya fice. Wannan mutumin ya gani da yake zaton maigadi ne. Shima yana ganin Dahiru ya saki fuska yana murmushi. Gaishe shi yayi yana tambayarsa aiki

"Kwana biyu na dena ganinka a nan Baba har na fara tunanin ko ka dena aikin ne"

"Wani uzurin ne dai ya taso min. Ya karatun naka? Maigidan nan yace baka neme shi ba har yau"

Dahiru yayi dan murmushi "ni dai da ya barshi wallahi bana son zuwa ya ga kamar kuma maula nake. VC din BUK ne fa na gani a katin"

A take mutumin nan ya sake ji Dahiru ya kuma shiga ransa. Yana son yara masu kwazo sai yake tuna masa da kansa lokacin da ya fara karatu. A wannan lokacin har itace yayi domin biyan kudin makaranta tun daga firamare sai gashi ya zama tauraro mai haskawa a kauyensu. Mutane da dama basu san almajiranci ne ya kawo shi Kano ba yau shine shugaban jami'a ta gwamnatin tarayya a garin.

"Ka daure kaje don nayi masa zancen kaima dalibinsu ne yaji dadi sosai"

Dahiru yace "to amma yanzu nasan ya manta ni da yaya zan kwatanta masa kaina?"

"Kace Dahiru kawai zai gane. Shi ma sunan autansa Attahir kusan sa'anka ne."

Ba don yaso ba ya amince zai je ranar litinin. Hira suka cigaba Dahiru ya bashi dari biyu wai yasa masa albarka ya karbi albashinsa ne. Da yaje gida ya yiwa Bilya korafin albashinsa da aka rage hakuri ya bashi tare da nuna masa masu aiki irin nasa da yawa albashinsu baya wuce dubu biyu. Shima tun farko saboda maigidan yasan zaiyi karatu ne suka saka masa albashi mai tsoka.

Ranar litinin kafin ya shiga lacca karfe biyu yaje ofishin VC. Daga suturar jikinsa sakataren ya fara masa kallon raini da dalilin zuwansa. Yayi sa'a ya tambayi sunansa ya fada. Yana shiga ciki ya fito ya nuna masa kofa.

"Bismillah"

Dahiru yayi godiya ya shiga. Mutumin da ya gani a zaune ne ya bashi mamaki sai kuma kunya da ya tuna dari biyun da ya bashi. Durkusawa yayi gwiwa kasa ya soma bashi hakuri kada ya kore shi.

Dariya ya rinka yi kafin yace ya tashi ya zauna.

"Yallabai Frofesa kayi hakuri kuskure ne wallahi"

Professor Abdulhadi Bature ya sake dariya "Dahiru tashi ka zauna magana zamuyi ta uba da dansa kaji ko. Yadda naga ka sake dani tun ranar yasa ban gyara maka zatonka na cewa ni maigadi bane. Akwai lemo a fridge dauko wanda kake so"

Tabdi yadda gabansa ke lugude idan ba gani yayi ya fita salin alin babu takardar kora ba yaushe zai iya shan wani lemo.

"Ko na dauko maka da kaina" yace yana masa dariya

Da gudu gudu Dahiru ya dauko wanda hannunsa ya fara kaiwa ya dawo ya zauna.

Daidaita fuskarsa yayi ba alamun wasa yace "Dahiru kada kaji tsoro alkhairi yasa na nemeka. Ina son yara masu kwazo da sanin yakamata. Yadda ka inganta rayuwarka da guminka yasa naji ka burgeni sosai. Ni bana son rago ba kuma nason yaron da zai kwanta yana jiran komai sai iyaye sunyi masa bayan hankali ya soma zuwar masa. Ga wannan ta Attahir ce amma ta kwana biyu. Ka fara amfani da ita kasan akan abinda kazo karanta. Computer engineering sai da laptop kuma nasan baka da ita. Wannan ita ce tukwicin dari biyun da ka bani"

Jakar laptop ya mikowa Dahiru wanda hawaye ya soma zubar masa. Sauka yayi daga kujerar yana ta godiya. Daga nan Prof Abdulhadi yace masa ya kusa sauka daga mukaminsa shiyasa yake gini zai dawo kusa dasu. Nasiha sosai yayi masa sannan yace duk sanda yake bukatar taimako ko shawara yaje gidansa na nan cikin BUK in sha Allah zai saurare shi.

Bayan ya tashi zai tafi ya tsayar dashi ya tambayeshi ko yana da wata matsala a yanzu. Dahiru baiyi kasa a gwiwa ba yace turanci ni yake bashi wahala yayi masa tsauri. Prof yace masa akwai English Academy a gwauron dutse ya nema ya shiga. Yana bukatar result din farko ya ga yayi kokari shi kuma yayi masa alkawarin kyakkyawan surprise kamar yadda yace yana dariya.

Ko kwabo bai bashi ba da zai tafi shima baisa a ka ba. Shi kuma Prof dalilinsa shine kada ya dora alakarsu akan kudi. Shi taimako daki daki ake bi domin samar da kyakkyawar alaka. Wani daga ka fara bashi kudi to fa duk inda yaji dugudugu wurinka zai kawo matsalarsa.

******

"Yasin bazamu yarda ba kawai asan wacce ake ciki"

Wani kaura ya cafe "ku barni na balbale gidan kawai a rage mugun iri kun gane ai"

"A'a mu dai ce kawai su bar garin nan. Idan ba haka ba sauran 'yan matan haka zasu rinka lalacewa a birni su dawo mu auri ragowar cuta"

Hayaniya ce sosai a kofar gidan Mal Fatihu. Samari da sanduna da gorori suna ta hargowa su dai kawai su bar garin. Kauyukan makota kowa zancen Mawadda akeyi ana bata mata suna. Su kuma sun gaji da zama dasu. Su kansu iyalin gidan abubuwa da dama idan suka je siya a yan kantunan dake kauyen sai a hanasu. Rayuwa tayi kunci garesu komai yayi tsanani.

Ana wannan rigimar Mal Isiyaku mahaifin Dahiru ya gansu. Kememe dama sun shatawa Dahiru layi akan zuwa gidan amma yadda yaga samari da yara suna wake wake ana jefa duwatsu a gidan ya tayar masa da hankali. Gidan maigari ya nufa kai tsaye ya sanar dashi. Ranar fadar maigarin hirar da aka dasa kenan.

Washegari Maigari da kansa yaje gidan Mal Fatihu saboda yasan bashi da lafiya. Shimfida akayi masa a karkashin bishiya matasa sukayi dafifi a wurin.

Kaninsa ne ya riko shi ya fito aka zaunar dashi akan tabarmar ya kwashi gaisuwa. Maigarin yasa aka kori matasan sannan ya soma magana.

"Mal Fatihu ina sake jajanta maka wannan hali da kuka sami kanku a ciki Allah Ya kiyaye gaba. Yaran garin nan sun bullo da sabuwar fitina wadda idan ban kawar da ita ba suna iya yin abinda bazai mana dadi ba. Sabili da haka ga mutane a wurin nan suna shaida nasan baka da wurin zuwa idan ka bar Tariwa. A cikin Kano unguwar Tunga ina da gida dan karami ne daki uku da bayangida. Wata shidan farko na amince ka zauna kyauta daga nan idan na shigo garin sai muyi maganar kudin haya. Ka amince?"

Kuka Mal Fatihu yake kamar yaro. Wannan wace irin masifa suka shiga. Ya koma Kano yayi me? A kauyen ma shi talaka ne sosai ina ga ya koma birni. Yanzu saboda kaddara ta fadawa yarsa shikenan sai a taru a koreshi daga mahaifarsa?

Maigari ga katse masa tunani "nasan kana cikin tashin hankali da damuwa amma ina tsoron abinda zaije ya dawo. Ka tafi da iyalinka idan kura ta lafa sai ku dawo. Zan gargadi yaran da iyayensu na baka sati guda"

Har Maigari ya tafi Mal Fatihu yana kuka ya ma kasa godiyar gida da aka bashi. Da taimakon kaninsa ya koma ciki ya sanar da iyalinsa. Ranar Malam babansa yazo gidan da kansa yace gara ma su tafin saboda yanzu ma meye marabarsu da basa nan kowa ya fita harkarsu.

Kuka dai baya karewa iyalin gidan. Haka suka hada kaya Mawadda tana jin kamar ta wayi gari taga komai mafarki ne ko kuma ta mutu ta huta.

*Sabon Shafi*
[08/01 8:32 pm] Biebie: *GUMIN HALAK...*💰9

*Batul Mamman*💖

Kafin ya karasa ciki yayi kokarin saisaita kansa a soro sai dai kallo daya zaka yi masa kasan akwai abinda yake damunsa.

Innarsa ce ta fara tambayarsa ko Dahirun ya fada masa magana wadda batayi masa dadi bane. Murmushin dole ya kirkiro sannan yace

"haba Inna kema kinsan yaron ba dai dattako ba kamar wanda ya tashi cikin tsofaffi irinku"

Jin har lokacin kirjin nasa ba dadi ya zauna sannan ya cigaba da cewa "yaso kwarai ya ga Mawadda nace ya dai yi hakuri ya nemi wata ita ma zamu yi ta bata baki ta karbi kaddararta"

"Hakane, amma gaskiya ban taba tsammanin haka daga gidan Mal Isiyaku ba" cewar Iya.

"Wani masoyin sai kana cikin yanayi kaka-ni-kayi dama kake sanin ainihin me ya aje a zuciyarsa game da kai. Allah Yasa hakan ne mafi alkhairi. Yaya Fatihu sai ka fadawa Yaya a tattaro komatsansu a mayar musu ko"
Ade ta fada kana ji kasan ranta a bace yake.

Shi dai Baba shiru yayi sai can ya tashi ya shige rumfar mahaifinsa ya nemi wuri zai kwanta.

Mawadda na zaune kamar an kafeta sai da ya tashi kuka ya taho mata ta mike tayi dakin Iya cikin sauri. Inda ta tashi Iyan ta kalla sai ga alamu na jini a jikin tabarmar.
Chapter 22 · 0% Book details