← Book details Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 68

Sashe 46

Gumin Halak Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba ya nunawa Marwanu shi "riko min Dahiru kamar bai san me yake yi ba"

Hannunsa yaji an kamo zuwa gaban Baba ga wasu dattijai makota suna masa jaje yaji wani yace Allah Yasa ayi nasarar kama shi dai.

Hantar cikinsa ta kada yaji ina ma ya bude ido ya ga mafarki yake yi jiki na tsuma yace "Baba..."

Katse shi Mal Fatihu yayi "Mu shiga ciki ta farfado kafin fitowarmu. Dama nasan ko waye bazai zauna a kama shi ba. Allah Ya kare mana ita daga sharrin ko ma su waye"

Kan Dahiru sai ya sake daurewa saboda rashin gane me Baba yake nufi. Danmani da yake tare da mutane kuma ya ga zuwan Dahiru mutumin da BB yace yana nema babu shakka ko dar a ransa ya matsa kusa da Saifullahi.

"Wannan shine mahaifinta?" Ya nuna Baba. Saifullahi ya amsa masa. Sai ya kuma cewa "Ku uku kuma 'yan uwanta kenan"

"Mu biyu dai, wannan shine zai aureta"

Marwanu ya janyo hannun dan uwansa yana karewa Danmani kallo "kai kuma waye?"

" Dan agaji ne, muna can bayan layi ne aka ce anyi hatsaniya a nan nazo gani" yana fadin haka yana ja baya basuyi aune ba ya bar wurin ta cikin jama'a da cincirindon almajirai da suka taru.

Baba ne a gaba ya sanar da iyalinsa tare suke da Dahiru. Kowa ta shiga suturta kanta sannan suka shiga idanunsa da suka kankance suka yi ja suna neman Mawadda. Hamdala yayi ga Allah da ya sameta da ranta bai san wane hali zai shiga ba da ta tabbata ta sake barinshi a karo na biyu.

Da kyar ya tattaro kalaman gaisuwa ga su Ade.

"Waye ya fada maka ne ko zuwa kayi kawai?"

Iya ce tayi tambayar ya amsa mata da cewa waya ya kira.

Bushra ta rufe baki "Laaaaaahhh ashe kaine, lokacin tsoro naji na zata ta mutu"

Hasiya mahaifiyarta ta daka mata duka "ce masa kika yi ta mutu don rashin hankali"

"Wallahi Mama baki ga fa yadda ta rinka rike kirji ba sai kuma ta dena motsi" tace cikin kuka.

Baba ya numfasa "To mu godewa Allah abin yazo da sauki. Ke Bushra bai ji miki ciwo da wukar ba ita ma iyakarta hoto. Allah Ya cigaba da karemu baki daya"

Iya ce ta taba Yaya ta nuna mata su Mawadda. Nata idanun a kasa suna digar hawaye yayin da Dahiru ya kura mata idanu kawai.

Yaya tayi dan tari "Mawadda kije ku gaisa da Dahiru sai kiyi masa bayanin abinda ya faru sosai. Mungode kaji Dahiru ayi ta addua da neman tsari"

Sallama yayi musu ya tashi ya tafi inda su ka saba zama falon soro. Kamar wadda kwai ya fashewa itama haka tabi bayansa.

Tana shiga ko zama bata yi ba ya tsareta da idanunsa "what happened my love?"

Kyabe baki yaga tayi zata soma wani kukan ya shiga girgiza kansa a hankali a hankali yace "babu wata kalmar tausasa zuciya da zanyi amfani da ita wadda ba'a fada miki ba kafin na zo, ki daure ki fada min abinda aka yi miki kinji."

Ta gyada kai sannan su ka zauna "ina jin ki"

Tun daga bayyanar Danmani a gabansu har zuwa farfadowarta ta fada masa. Fuskarta duk ta kumbura saboda kuka.

Dahiru kuwa ko yawu ya kasa hadiya saboda wani daci da yaji ya taso masa har wuya. Bakinciki, bacin rai da damuwa babu wanda bai rufar masa ba. Tashi yayi ya koma bakin tagar falon wadda ta bulle wajen gidan ya tsaya. Ya rasa ma ta ina zai fara. Wane irin dan iska ne zai tare mace yasa ta daukar kanta a hoto. Me yasa kowane mara kirkin idan ya kwaso shararsa akanta yake ajiyewa.

Kukanta yaji ya tsananta ya juyo ya dawo gabanta ya tsuguna "me ki ke so nayi miki kiji sauki a ranki? Ko menene ki fada min nasan bazaki nemi abinda Dahiru bashi dashi ba."

Sai da wasu hawayen suka zubo ta iya bashi amsa.
"Ka dubi girman Allah ka fada min gaskiya Yayanmu. Ina yin wani abu ne da yayi kama da gayyatar maza masu mugun hali gareni? Ina bayyana tsiraici a inda ya kamata na boye ne?? Yanayina ko maganata sunyi kama da na mata marasa kamun kai??? Meyasa sai ni kawai suke bi????" ta kuma fashewa da kuka.

Ba karamin karyar masa da zuciya tayi ba tamkar ya tayata kukan.

"Babu ko daya sai dai ke din baki fi karfin Allah Ya gwada imaninki ba. Kin manta yana daga cikin abinda Allah Yake mana nuni dashi wato kada muyi tunanin don munce munyi imani shikenan mun tsira daga komai na rashin jindadi. Dole ne mu fuskanci kalubalen rayuwa sai dai na wani ya fi na wani. Allah Yace bazai dora mana abinda yafi karfin imaninmu ba. Ki sawa ranki komai ya wuce."

Murya a dashe tace "Yayanmu tsoro nake ji. Tun farkon maganar auren nan sai naji gabana yana yawan faduwa."

Gyara zamansa yayi daga tsugunawar saboda gajiya da ya soma ya zauna sosai a gabanta amma ya bar tazara tsakaninsu domin ya san iyakarsa. Domin ya kwantar mata da hankali yayi murmushi.

"Nima ina jin haka sai dai na alakanta shi da sabuwar rayuwar da zamu fuskanta daban da wadda muka saba. Kinsan fa aure ba karamin abu bane. Hatta sunanki sai ya chanja"

"Daga aure sai chanja suna? Ni dai ban taba ji ba"

Kallonta yayi tana tuttura baki yayi dariya kadan "Yanzu sunanki Mawadda kawai, amma muna aure zaki ji an koma cewa Matar Dahiru, Mawaddan Dahiru idan wata tara da kwana tara ya cika kuma ki koma Maman wane ko wance"

Bata san lokacin da ta soma dariya ba tana rurrufe fuska.

Yaji dadin ganin ta saki ranta ya sami damar cigaba da tsokanarta kuwa "sai yanzu na tuna ma, ko irin hirar nan ta sunan 'ya'yanmu na fari bamu taba yi ba."

"Ni dai kada ayi wannan hirar ko na koma gida yanzun nan" tace tana masa murmushi.

Alamun sakawa baki zip yayi "To Qulqulatul qurabati na bari"

Wannan suna da taji yasa ta rinka dariya harda guntun hawaye tana yi tana rufe baki.

"Allah Sarki Anti Qareeba Yayanmu kaima kasa mata rai fa"

Yasha kunu "ta sawa kanta dai, kinsan fa daga baya ko muryarta naji sai gabana ya fadi saboda kawai nasan akwai abinda tazo dashi na takura min"

"Idan....idan"

Karkace kai yayi yana kallonta "idan me?"

Maimakon ta fada sai ta tsuke bakinta. Kunya take ji tace masa idan ta tare tana son zuwa duba Qareeba.

"Bari na tafi tunda kin kasa fada"

"Zaka kaini na dubata idan...."

Ya karasa mata "idan kin tare kin zama matar Dahiru? In sha Allahu ko an sallameta zamu je"

Dahiru bai bar gidan ba sai wuraren goma da rabi. Shima don kada a ciki a ga rashin hankalinsa ne amma ko kadan bai gaji da zaman ba yana ta sako hirar da zata dauke mata tunani.

Da ya tashi wayarsa ya dauko "please kada ki zauna tunani idan na tafi bacci kawai."

"Yes sir" tace tana masa salute irin na sojoji.

Da haka suka yi sallama cike da farinciki sun manta da wani mai daukar hoto.

******

A bangaren Danmani kuwa gidan da BB yake ya wuce kai tsaye. Wayarsa da ya bashi ya dauki hotunan kasa budeta yayi tun a hanya. Dayake aljihunsa da nauyi waya ya fara saya kafin yaje unguwarsu Mawadda. Yanzu da ya kai masa sai ya bashi wayarsa yace ya tura.

BB kamar yayi hauka da ya ganta. Tayi kyau ta canja gabadaya fatarta sai sheki take yi. Idan ya aureta ya more ya ayyana a ransa yana cewa Danmani da fatan bai taba koda yatsanta ba don yarinya ce mai daraja.

"Wane ni yallabai, sai dai na bincika wannan mutumin shine zai aureta asabar dinnan"

Wata irin dariya BB ya rinka yi sannan ya dawo ya tafa da abokinsa "ko kasan komai ya koma more interesting da wannan bayanin. Sai yayi danasanin dukan da yayi min."
******

Sannu sannu bata hana zuwa inji Bahaushe sai dai a dade ba'aje ba.
Yau alhamis aka tashi da kamun Mawadda. Iyaye da 'yan uwa da ita kanta amaryar farincikinsu bazai misaltu ba. Filin wata makaranta suka kama da ake yawan biki zasuyi taronsu a ciki. An gyara wurin sosai ya kayatar.

Amarya ta hade cikin wani purple din lace da pink din ashoke. Lokacin da zasu tafi wurin kamun Ade har kuka tayi. Ta dade da cire rai zata ga auren tilon 'yarta mace ashe inda rai da rabo. Dahirun da take matukar so da 'yarta Allah Ya sake dawo musu dashi lokacin da basuyi zato ba.

Dayake kamun shine babban taro daga bangarensu sun kashe masa kudi don ya tafi daidai da zamani suma. Komai nasu cikin burgewa daidai ruwa daidai tsaki. Haj Mama ita ce ta fesawa Mawadda turaren kamu na al'ada ta rugumeta a jikinta aka yi musu hoto. Ganin Mawaddan na sunne kai tace mata ita dai surukar zamani ce matar danta ta zama 'yarta gara ta ajiye wannan kunyar sun zama daya.

******

Ana can ana taro Dahiru da Attahir da wasu abokansu suna gidan da Dahirun yake zama don nan suka dawo saboda baki. Itama Nawal ranar suke nasu kamun.

Hira ake yi da barkwanci irin na angwaye Attahir ya sako zancen kai amaren da za'ayi ranar asabar.

Da fari an tsara akan kowacce za'a fara kaita gidan iyayen nata mijin. Sai dai saboda nisa da ma kawaici na mutan kauye Inna tace Dahiru ai dan su Hajiya Mama ne saboda haka a kaita gidan Baba Prof kamar yadda za'a kai Nawal. Daga nan sai kowanne ango ya dauki amaryarsa. Murna wurin angwayen ba'a cewa komai su tsari yayi musu daidai.

"Dahiru ka shirya tsere fa zamuyi aga wanda zai fara zuwa gida da matarsa"

"Baka isa ka sani yin gudu da Mawadda akan titi ba ranar shigarta motarmu ta farko. Idan kasan tafiyar kwai to ita zanyi"

Ihu abokai suka sa shi kuwa ya fuske. Attahir yace "kai dai kana da matsala na rana dayan ma bazamu yi ba. To ba tsere ba mu tafi a mota daya"
Chapter 46 · 0% Book details