← Book details Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 80

Sashe 80

Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Zahra hiyan Sun gama shirin su tsab yaya Khalid da kan sa ya ja su a cikin motar sa suna tafiya suna yar hira Zahra a gaba mota hiyana a baya "yaya Khalid ayya zaka kai mu wajen lallema idan mun gama gyaran gashin?" chewar hiyana kallon ta yayi ta cikin mirror motar kafin yace "yanzu haka addu'a nake Allah ya sanya kar bgs ya nemiki har muje mu dawo nayi gangancin fita da ke ba tare da izinin sa ba sai yanzu ma nake nadamar yin hakan" "to ai yaya Prince bay...bata karisa maganar ba tayi shiru kasan cewar ta tuna tun da yaya Prince bai sanar da yaya Khalid akan tafiyar su ba to tafiyar sirri ce bai kamata ta sanar wa kowa ba amma ta sha ruwan mamaki ya akayi yaya Prince bai sanar da yaya Khalid ba ya sanar min?
tayi nisa cikin tunani Khalid ya taka wata wawan birki wadda ya sanya sai da kanta ya bugu da jikin kujerar gabar motar.
A zafafe ta É—ago kai dan taga me ya sanya yaya Khalid taka irin wanna birki haka,wata mota ta gani kirar siyasa baka mai bakin glass ne ta sha gabar su kan kace me jibga jibgan bakaken mutane sanye da bakin kaya sun rufe fuskar su baka iya ganin komai sai ido ne suka fito daga cikin motar
Khalid na kokarin ɗaukan wayar sa babban cikin su ya buɗe kofar motar nasu ya damko Khalid ya fitar waje ba tare da ɓata lokaci ba suka tura Khalid cikin motar su sanna suka fito da hiyana da Zahra nan fa suka ruɗe sun rasa wacece ogan su yace su kawo dan Zahra da hiyana da bgs duk kamannin su ɗaya sak kamannin Ammi suka ɗauko. Fito da wani hoton ogan nasu yayi da wata murya mara daɗin ji ya dubi su Zahra ya nuna musu hoton yana faɗin "wacece wanna a cikin ku? Murya na rawa hiyana tace "ni ce" da sauri Zahra tace "ba ita bace ni ce" tsawa ya daka musu tare da fito da bindiga ya saita su yace "idan baku faɗa min wacece ba sai na harbe ku dukkan ku biyu!!" "wlh karya Aunty Zahra take ni ce ba ita bace" chewar hiyana damko wuyar hiyana yayi ya turata cikin mota suka shiga suka tada motar da gudun gaske suka bar wajen

durkushewa kasa Zahra tayi ta saki kuka mai ban tausayi tana faÉ—in "me yasa zaki ce kece Aunty Hiyana? why ba zaki bari su tafi da ni ba tun da yaya Khalid na hannun su ni nasan yaya Prince ya fara son ki yanzu idan suka kashe ki shike nan ba zai sake son wata mace ba" tana kuka tana surutai kamar mahaukaciya.

Sai da tayi kukan ta mai isar ta san nan ta miƙe ta koma cikin motar su cikin sauri ta ɗauko wayar ta tafara kiran layin Bgs sau uku tana kiran sa bai ɗaga ba kiran layin Aryan tayi shima har sau uku bai ɗaga ba juyawa tayi gabas da yamma hanyar shiru babu motsin kowa lokacin guda mugun tsoro ya dira a ranta gashi ita bata san haryan komawa gida ba dan ba fita take ba ko school kai ta ake kuma a ɗauko ta chan wani dabara ya faɗo mata akan ta kira layin Abba
cikin sauri ta fara kiran layin Abba shima bai É—aga ba ihu ta saki tare da yin wurgi da wayar gefen titi dan bakin ciki
tarwatsewa kaca kaxa wayar yayi,sai bayan da ta fasa wayar ne kuma ta fara nadama yanzu dame zata nemo gida akan azo a É—auke ta fita tayi daga cikin motar ta fara tafiya da kafa tana tafiya bata ma san in da ta nufa ba tanayi tana kuka kamar zararriya.

To masu karatu sai mun haÉ—u gobe idan mai dukka ya kai mu to masoyan yaya Khalid masoyiyan hiyana masoyan Zahra aikin tsayuwar dare ya ganku fa amusu addu'a gashi zaku nan gidan Abba basanan suna Maiduguri akoi chakwakiya fa hmmmm
Chapter 80 · 0% Book details