← Book details Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 80

Sashe 27

Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Manna wayar tayi a kunnen ta, chikin sanyi da girmamawa duk da batasan wanene ba tace "Assalamu alaikum ina kwana" daga ɗayan ɓangaren Ammi tace "lfy hiyana Ykk y gida? Chike da farin chiki da zumuɗi tace "Ammi ina lfy ya gida yasu Abba wlh ina kewar ku dukkan ku" "sunanan lfy muma muna kewar ki" "ayya Ammi ki sa a dawo dani gida kinji na gaji da nan banason kasan nan ko kaɗan" jin abun da hiyana tace ba karamin ɗagawa Ammi hankali tayi ba hakan ya tabbatar mata da Bgs baya kula da hiyana idan yana kula da ita bazata yi wan nan furuchin ba, wani irin bakin chikine ya tokarewa Ammi makoshi awan nan karo gaskiya bazata kyale Bgs ba ya isa haka "Ammi ya naji kin yi shiru ko dai kin kashe wayar ne? Muryan hiyana ta katse mata tunani da sauri tace "aa ban kashe ba, kina jina hiyana yanzu zan sanya yayan naki ya sai miki waya yau ɗin nan anjima sai muyi magana da wayar ki yanzu kam ki bashi wayar sa" Ammi ai jiya yaya Khalid ya sai mana waya dukkan mu nawa babu charji ne yanzu nasa a charji idan yayi charji zan ansa number ki ko wajen Aunty Zahra ne sai na kiraki" mamaki ne ya kama Ammi lallai ba karamin abu Bgs kewa hiyana ba tun da gashi shine mijin ta amma batace zata ansa number na awajen Shi ba sai dai wajen Zahra yarinya kwata kwata bata so ayi mata zanchen sa, amma bari na ɗan tambaye ta "Hiyana ina yayan ki? "Yana ɗakin sa Ammi" "to naga lokachin tafiyar su wajen aiki ya kusa kije ki tayashi shiryawa mana zamuyi waya anjima" "kai Ammi! Shiryawa kuma kinason ya....sai kuma ta yanke maganar tace "to Ammi bari naje" hmmmm kawai Ammi tace dan ta rasa me zata che da Hiyana, chikin karyewar zuchiya tace "to hiyana ki je ki kai masa wayar In Sha Allah daga yau kasar zata fara yimiki daɗi kinji? "To kawai hiyana tace tare da mikewa ba tare da ta katse kiran ba ta nufi betroom nashi

da sallama a bakin ta ta shiga yana tsaye gaban mirrow yana shafa mai, gaban sa dazo ta tsugunna chikin sanyin murya tace "yaya prince ina kwana ga wayar" shiru yayi bai ansa mata gaisuwar ba kuma bai ansa wayar ba, aikin gaban sa kawai yake, Almost 10mins tana sugunne shi kuma ya gama shafa mai yana gyara gashin, chike da tsoro tace "yaya prince dan Allah ka ansa wayar mana wlh ji nake kamar zan faɗi kai na na chiwo sosai" shiru kamar baya wajen duk wannan abun da suke Ammi na jin su dan bata katse kirar ba, sai da ya gama abun da yake san nan ya ansa wayar ya wuche dressing room dan shirin zuwa wajen aiki, sauri sauri Hiyana ta miƙe ta fito ta nufi kitchen already jourfree ya gama shirya breakfast na bgs ɗauka tayi ta nufi betroom nashi.

Tana shigowa dai dai lokacin ya fito daga dressing room ya shirya chikin haɗaɗɗadiyar suit ash colour, da alama wani meeting zai je ba ƙarin kyau kayan suka masa ba, sun kara fito masa da ainahin suran jikin sa, kyawun sa ya kara bayyana sosai, ya ɗaure lallausan bakin gashin kan nan nashi, sai wani haske da ya kara, fiskar nan tashi a ɗaure take sosai kamar wadda akayiwa wani abun, dan yanzu da yake tsaye gaban mirrow fiskar a ɗan sake, daga shigan sa dressing room ya fito fiskar sa ta sauya sosai, ɗamtsen hannun san nan kullun kamar kara hurasu ake sai kara chika suke kamar zasu fasa hannun rigar,
sosai hiyana ke satar kallon sa ta kasan ido tana addu'ar Allah ya dai dai ta tsakanin su, kwata kwata bata son ya fahimci tana son shi shiyasa bata taɓa yarda tayi gigin kallon face nashi kai tsaye sai dai ta rinƙa satar kallon sa ta sanya wa ranta ko mutuwa zatayi da son sa bazata taɓa bari ya fahimci tana son nasa ba.

Saman table ta ajiye masa abincin, ta tsaya awajen tana jiran shi yazo tayi sarving na shi

Sake feshe jikin sa yayi da perfume nashi mai bala'i kamshi da daɗi sannan ya nufi saman sofa ya zauna, chikin sauri ta fara haɗa masa tea ta miƙe masa, sai da ya ɗauki tsawon 2mins kafin ya ansa cup ɗin, a hankali ya kai cup ɗin sai tin dan karamin bukin sa ya fara sha tea ɗin, kasa kasa hiyana ke satar kallon yadda yake shan tea ɗin kamar bai san sha, zuba masa chips tayi a plate tare da soyayyun kaji, ta dora saman table ɗin ta matso masa da table ɗin, komawa gefe tayi ta zauna tana jiran ya kammala ta kwashe kayan.

Muryan sane ya daki gogon kunnen ta yana faÉ—in "kije ki É—auki magani a drawar chan ki sha guda biyu bayan kinchi abinchi, san nan idan kika sake magana ta da Ammi kin san sauran" murya na rawa tace "kayi hakuri yaya prince bazan sake ba" shiru yayi bai sake magana ba yachi gaba da shan tea É—in sa mikewa tayi ta nufi drawer ta É—auko maganin ta fice daga É—akin ta nufi kitchen

abinci kaɗan ta zuba a plate ta dawo palo ta zauna, a nitse ta chi abin chin ta ta sha ruwa sannan ta sha maganin tana kokarin mikewa ta nufi ɗakin, shi kuma yana fitowa, kasa kasa chikin tsoro tace "adawo lfy Allah ya tsare" a'sukwane ya juyo ya kalleta nan take taji numfashi ta ya tsaya duk wani jini dake gudu a jikin ta sai da ya tsaya chak addu'a ta shigayi Allah yasa ba laifi tayi ba faɗin hakan da tayi, juyawa yayi ya chigaba da tafiya ba tare da yayi Magana ba bin bayan sa tayi da kallo har ya fice, yana fita ta sauke nauyin ajiyar zuchiya tare da miƙewa ra nufi betroom ɗin

Kwashe kayan abin chin tayi ta maida kitchen ta dawo ta kara kyara É—akin ta shiga toilet na shi tayi wanka a gurguje ta fito É—aure da towel nashi wadda yazo mata har kasan guiwa, fitowa tayi ta nufi betroom nasu Fahad, sallama tayi a bakin kofar, Amrat na daga chiki ta amsa tare da faÉ—in "Aunty Hiyana ki shigo mana yaya Fahad baya nan" "aa Amrat ni bazan shigo ba ki kawomin hijabi idan akoi a chikin kayan ki" "Aunty hiyana hijabin É—an karamin ne fa bai wuchi ya tsaya zuwa kirjin ki ba" "eh kawomin" bata karisa rufe baki ba amrat ta fito rike da wani haÉ—aÉ—É—en dan karamin hijabi mai stone a jiki, pink colour ta mika mata, chikin sauri hiyana ta ansa ta sanya a jikin ta ta juya batare da ta kara Magana ba sauko palon kasa tayi, ta nufi part na su Zahra.

dai dai zata shiga part ɗin Zahra na fitowa karo suka kusayi baya hiyana tayi tana hararan Zahra "lfy kike harara ta Aunty hiyana? Zahra ta tambaya tana guntse dariya dan tasan batun hijabi ne ya kawo hiyana "yanzu Aunty menen hakan dan Allah ki bani hijabi idan kina da shi wlh yau da blanket ɗin yaya prince na rufa nayi sallah" "dan Allah Aunty Hiyana da gaske kike yi yau da blanket na yaya prince kikayi Sallah" hararan wasa hiyana ta wurga mata kafin tace "eh mana" dukawa kasa Zahra tayi tayi sujudur shukur tana ɗagowa ta rungumi hiyana tana faɗin "Alhadulillah Alhamdulliah ya Allah na godema da ka nunamin wannan rana ya Allah ka dauwamar min da yar uwata chikin farinchiki ya Allah kasa yaya prince ya so ta sosai" "ke Aunty Zahra waya che miki sona yake, baya nan fa na ɗauki blanket na shin kema ai kin san da yana nan ban isa ba" "Aunty Hiyana ke dai karki damu jiya kwana nayi ina sallah ina miki addu'a Allah ya juyo da hankali yaya prince gareki" "hmmmm ko kuma kwana kikayi kina zubawa yaya Khalid iya shege ba" "kai Aunty hiyana to duk ma ba wan nan ba yaya khalid ne yace daman naje na sanar dake ki shirya zamuje yanzu nan ya mana registration zamu koma school" "da farinchiki Hiyana tace "kai Alhadulillah Alhamdulliah daman na gaji da zaman gidan nan, yanzu dai Aunty Zahra dan girman Allah ki bani hijabin ki da kika sanya da zamu zo nan kina ga fa ko hijabin sallah bani da shi" "kimin alkawarin iya sallah zaki rinƙayi da shi kawai" "Aunty Zahra na miki alkawari iya sallah kawai zan rinƙa yi sai kuma idan zan fito palon kasa ya miki? "Eh ya min kije ki shirya zan kawo miki hijabin yanzu" to kawai hiyana tace ta juya ta koma part nasu Zahra kuma ta koma ɗaki

8pm dai dai Khalid ya É—auki su hiyana suka tafi registration yaje ya musu sannan suka wuche wajen sayyaya saya musu duk wani abun da zasu bukata na makaranta yayi sai karfe 1pm dai dai suka dawo gida kowa ya wuche part nashi.

Hiyana na shiga part nasu kai tsaye wajen da ta ajiye trolley kayan ta ta nufa dan ta sanya kayan school nata a chiki, da mamaki take bin wajen da kallo, gani babu trolley ɗin awajen lallaɓawa tayi ta leka betroom ɗin ta tagani ko yaya prince yasa an kai su chan, gani tai basa chiki, juyowa tayi ta nufi betroom nashi, da mamaki take kallon yadda jourfree ya shirya mata trolley ɗin ta a chikin ɗakin tunani take to waye yace jourfree ya kawo mata kayan ta nan kar yaya prince yazo ya hukun tata yayi tunanin ko ita ta kawo su ɗakin, jiki ba kwari ta nufi trolley, zuge zip ɗin babban tayi ta zuba kayan makarantar nata a ciki, ta miƙe ta wuche toile
Chapter 27 · 0% Book details