← Book details Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 80

Sashe 20

Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Aunty Zahra menene wan nan? Ai wan nan ba kaya bane shirme dai kuma naga babu hijabai da irin abayan nan da sauran manyan kaya na Musulunci a chiki sai dai shirmen irin kayan da diyana ke so" chike ta tsokana Zahra tace "Aunty hiyana yaya prince ne yace wa yaya khalid irin kayan da zai saya miki kenan kuma kada ki kuskura ki rinƙa sanya hijabi a chikin hidan nan dan nan ba gidan hijabi bane gidan kashe miji da love ne wai ma Aunty Hiyana ba Aunty farida ta hanaki sanya hijabi ba? Kina son in faɗa mata chewa baki jin maganar ta ko? "Aunty Zahra waye ya tsara miki maganar da zaki faɗamin haka? dan dai na san wan nan ba maganar ki bane sai dai idan wani ne ya tsaramiki "ni Aunty hiyana babu wan da ya tsaramin iya Gaskiya na faɗamiki" "naji iya gaskiya ne to amma Aunty Zahra me yasa kuke son haɗani da mutumin da baya ko san ganin fuskata? "Au yanzu Aunty Hiyana kin manta alkawarin da kikayiwa su yaya khalid ɗazun nan na chewa ki kayi fa kin ɗaura ɗamarar yaki da jiji da kan yaya prince? "Ban manta ba Aunty Zahra ina sane" "to ai saboda mu taya ki yaki da jiji da kan na shine yasa yaya Khalid yace in zaɓa miki irin kayan nan san nan yace ga waya na baki akoi sakon massage a chiki ki karanta" ta kari maganar tana mikowa hiyanar waya kiran i photo 14 promax, murmushi hiyana tayi tasa hannu ta ansa wayar tana faɗin "wow amma gaskiya wayar tayi kyau ki tayani yiwa yaya khalid godiya" "eh to yanzu dai ki duba massage ɗin dake chiki first" "aa Aunty Zahra zan duba amma sai na koma ɗaki yanzu bari na kwashe kayan na kai ɗaki tukun nan, dan bansan ganin waje a watse" shiru Zahra tayi bata sake magana ba miƙewa Hiyana tayi tare da ajiye wayar a hannun kujera ta fara kwashe kayan nata da ta watsa tana mayarwa chikin trolley

"Aunty Zahra yanzu da baku sayamin hijabi ba dame kuke son na rinƙa yin sallah? "To baki da hijabi ko nayin sallah ne daman? Ina wadda kika sanya da za mu zo" "ai shi na yaga dazun yanzu ko ɗaya babu" "to inaga sai dai ki rike na Amrat dake jikin kin nan dan a garin nan ba'a sayar da hijabi" shiru Hiyana tayi ta chigaba da kwashe kayan dan tasan karya Zahra ke mata akoi kasar da ba'a sai da hijabi ne amma bata son yin jayayya da maganar Zahra dan haka sai tayi shiru ta chigaba da kwashe kayan

Babban trolley ta fara za zuwa part nasu tana shiga ta tsaya turus a Palo tunani ta shiga yi aina zata ajiye kayan nata dan wlh ko kasheta za'ayi bazata koma ɗakin taba dan ita bata yarda da ɗakin ba gani take akoi wani snake ɗin a chiki, da taga ba abun da tunani zai kara mata idan ba zafin kai ba sai ta nufi bayan sofa mai zaman mutun 3 ta ajiye trolley haka ta kwaso sauran dukkan ta ajiye su a bayan sofa, buɗe trolley tayi ta ɗauki wasu riga da wando masu ɗan hankalin ta lallaɓa ta leka ɗakin yaya prince dan taga ko ya dawo bata sani ba, tana ganin baya chiki tayi sauri ta shige chikin ɗaki ta chire hijabi jikin ta sauri sauri ta sanya kayan data ɗuko tare da mai da masa towel nashi toilet ta fito da sauri har tana haɗawa da gudu

Sai da ta fito palo san nan ta sanya hijabin Amrat a jikin ta ta fice daga palon nasu ta sauka palon kasa

Tana zama saman sofa mai zaman mutun 1 su yaya khalid na shigowa shi da yaya Yusuf kusa da Zahra yaya Khalid ya zauna, shi kuma yaya Yusuf kusa da Lamrat ya zauna, chikin nitsuwa da girmama Hiyana ta gai dasu, da fara suka amsa mata tare da tambayar ta ya karfin jiki sunkuyar da kai kasa tayi tace "naji sauki"

"Amma sister kin kaiwa Bgs abin chi kuwa? Chewar khalid yayi maganar yana kallon ta "eh yaya Khalid tun kafin ku dawo wajen aiki naje na shirya masa abin chin sa a ɗaki amma bai Chiba, daman kuma nasan ba chiɗin zai yiba dan jiya ma da na kai masa bai Chi ba" chike da ɓachin rai Khalid ya miƙe ya nufi waje yana faɗin "ina zuwa, kai tsaye wajen hutawa dake gefen dama a chikin gidan Khalid ya nufa

Waje ne mai matikar kyau da tsaruwa kewaye yake da furanni masu kyau da tsada sai kamshi suke, daga tsakiyar wajen kuma wasu tsadaddun kujeru masu numbashine a wajen an sanya runfa mai kyau a dai dai saitin kujerun san nan aka kewaye kujerun da glass aka sanya karamin table a tsakiya, ga wasu yan kanan box glass masu kyau suna É—auke da ruwa da wasu irin kifaye (fish) masu kyau sai yawo suke a chiki an kewaye wajen gaba É—aya da box glass na kifin sai wasu tsadaddun fitilla masu bada haske mai tambarin Bgs, komai na wajen É—auke yake da tambarin Bgs, kallo É—aya zaka wa wajen kasan wajene na musamman kuma mai mallaki wajen mutun ne na musamman.

Zaune saman kujera yana latse latse a system dake kan chinyar sa Khalid ya iskoshi sanye yake chikin wando 3cuter da yar riga mara nauyi, chike da bachin rai khalid ya shigo wajen amma yanayin arba da face É—in Bgs nan take yasha jinin jikin sa dan yaga babu alamar wasa a face nashi, jiki a mache ya zauna kusa da shi har yar shakewa voice nashi take ya fara magana

"Haba Bgs ba kamin alkawarin idan sister ta kawo maka abinchi zaka chi ba? Why yau baka chi ba? Shiru Bgs yayi kamar bai san da zaman mutun a kusa da shi ba, idan da sabo khalid ya saba yasan idan kayiwa Bgs magana wani lokaci ma yana É—aukan 10mins kafin ya baka amsa idan sauri kake ma to sai dai ka tafi, dan wannan abun ya zamo masa jiki, wani lokaci sai ka chire rai da samun amsar Bgs tukun nan sai kuma kaji ya baka amsa wata zubin har sai ka manta da maganar da kayi masa ma, kafin ya baka amsa, to awan nan karon ma hakane sai da Khalid yayi zaman 15mins san

Batare da ya dogo idon sa daga kan system ɗin ba ya fara magana "ni fa Khalid ban maka alkawarin hakan ba kawai nache maka zanyi tunani ne, so naga ma no need nayi wani tunani dan nasan ba zan iya chin abun da yarinyar nan ta taɓa da hannun taɓa kyama take bani ban so, ɗazun ma dana che zanyi tunanin kawai dan naga kaji bachin rai sosai ne shiyasa na maka hakan dan ka sauko amma yanzu ka tashi ka bani waje dan nima raina a bache yake yanzu!! Ba musu khalid ya miƙe ya bar wajen dan ya lura tabbas Bgs na chikin bachin rai idan ya tsaya yache zai masa wani magana to zai iya sumar da shi awajen

Chikin gida ya koma kai tsaye ya wuche part nashi mikewa Zahra tayi ta bi bayan sa dan taga fiskar sa kamar babu annuri.

11pm Amrat che kadai zaune a palon kasa tana shan complex su Zahra sun tafi part nasu, a tare Fahad da Bgs suka shigo palon kai tsaye part nashi Bgs ya nufa, Fahad kuwa tsayuwa yayi yana kallon Amrat dake ta faman shan complex nata "ke me kike yi a nan har yanzu baki kwnata ba? "Naga baka dawo ba ne yaya Fahad kuma sai na fara jin yinwa shine na fito na haÉ—a complex, karisowa in da take yayi yasa hannu ya ansa cup din, debo complex É—in yayi a spoon ya kai bakin sa ya sha zama yayi kusa da ita, ya fara shan complex É—in sosai yana sha yana bata a baki gwanin sha'awa, a tare suka shanye complex É—in bayan sun gamane ya ajiye cup É—in a gefe, ya dawo da kallon sa kanta matso da fukarsa yayi kusa da tata har suna iya jiyo numfashi juna harchen sa ya kai kan É—an karamin bakin ta la lashe ragowar madarar complex dake wajen, wani dogon numfashi Amrat taja tare da runtse ido kasa kasa yace "numfashi me kike ja kuma? Ko kinyi tunanin bakin naki zan sha ne? Girgiza masa kai tayi tana faÉ—in "aa" "to ai garama kiyi tunanin hakan dan yanzu kuwa zan fara shan kayana" buÉ—e baki Amrat tayi zatayi magana yayi saurin haÉ—e bakin su waje guda, sosai yake kissing nata chikin dabara ba tare da ya zame kabin sa daga nataba ya duke ta ya É—orata kan chinyar sa tare da mikewa da ita ya nufi É—akin su, yana shiga palon part nasu yachi karo da hiyana kwanche saman doguwar kujera tana barchi, É—aure fuska sosai yayi a hankali ya zame bakin sa daga na Amrat tare da sauke ta kasa chike da bachin rai yace "Amrat jeki É—aki ina zuwa, batare da ta lura da hiyana ba ta wuche É—aki

Karisowa yayi wajen Hiyana yasa hannu ya ɗan bubbuga jikin kujerar yana kiran sunan ta, da kyar ta iya waro blue eyes nata waje sunyi jaa almar barchi bai ishe taba, "sister me ya kwantar dake a nan? Me yasa baki shiga ɗakin ki ba? Mikewa zaune Hiyana tayi chikin muryan barchi ta fara magana "yaya Fahad wlh ɗazun machiji na gani a ɗakina to na roki yaya prince ya chiremin shi amma har yanzu wlh tsoron ɗakin nake ji bazan iya shiga chiki ba" "machiji kuma!? a chikin gidan nan kai anya kin gani da kyau kuwa sister to wai ta yama za'ayi machiji ya shigo gidan nan har ɗaki" "wlh yaya Fahad na gani da kyau machijin gaskiyane, ka tambayi yaya prince kaji shi ya chire da kansa" "Gaskiya abun da abun mamaki a che snake a gidan nan amma dai ina zuwa" yana kai karshen maganar ya miƙe ya shiga ɗakin Bgs.
Chapter 20 · 0% Book details