← Book details Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 80

Sashe 68

Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan an kawo kusu takeaway hiyana ta ansa suka fice daga wajen suka koma mota chikin daji ya nufa da su yana tuki chikin kwanchiyar hankali
bakin wani katon dutse mai dubar da ruwa yayi parking na motar ya fito ya zauna saman bayan motar fitowa tayi itama bin wajen ta farayi da kallon wow wajen ha haÉ—u iya haÉ—uwa wajen kewaye yake da dogayen furanni masu kyau launin fari da kuma yellow daga gefe katon dutsene wadda ruwa ke zuba daga chikin sa kamar faffo yana taruwa akansa kamar rafi ga dogayen bishiyoyi koraye shar shar kewaye da dutsen wajen shiru baka jin kokai sai sautin kukan tsuntsaye
dawo da kallon ta tayi kansa ya chire face mark nashi ya ajiye a gefe yana kallon ta "yaya Prince wajen nan yana da kyau sosai" shiru yayi yana kallon bai yi magana ba takawa tayi a hankali ta karisa wajen dutse dake zubar da ruwa hannu ta sanya ta tara ruwar da mamakin ta sai ta ji ruwan da zafi kamar an sa a wuta kasa kasa taji sexy voice nashi yana faɗin "yinwa nake ji" da sauri ta juyo ta dawo wajen motar ta ɗauko musu abinchi ta kawo masa dirowa kasa yayi daga saman motar ya ɗauke ta chak ya ɗaurata saman bayan motar kafin shima ya haura ya zauna a tare suka chi abincin gwanin ban sha'awa sosai yau Bgs yaci abinci har mamaki hiyana keyi bata taɓa ganin sa yaci abinci mai yawan wanna ba suna gama chi ta diro kasa ta kwashe kayan abincin ta zubar ta koma wajen dutse ta tsaya tana kallon ruwan ta zubawa tsuntsayen dake zuwa shan ruwan awajen ido ji take kamar ta shiga ruwan tayi wanka tayi nisa chikin tunanin sai jin sa tayi ya rungumota ta baya ya kwantar da kan sa saman kafaɗarta ya zuro hannun sa saman kugun ta kasa kasa yace "zaki shiga ruwan ne?" Hannu ta ta ɗaura saman hannun sa dake kan kugun ta tana shafawa chikin shagwaɓa tace "eh zan shiga kai ma zaka shgane? Juyo da ita yayi suna fuskantar juna "ba yadda zan yi in shaga chikin ruwan nan da kayan jiki na ɗin nan" kallon sa tayi da kyau kwafa tayi a ranta tace zaka shigane ma ai na san me zan maka sakin sa tayi ta faɗa chikin ruwan tare da sakin ihu dan duk tunanin ta ruwan dake taruwa a kasan dutse bai da zurfi sai ta ji akansin haka dumin kuwa ruwan ya haɗiye ta gaba ɗaya gashi bata iya ruwa ba diyana ta fita iyawa ko a garin su ita bata shiga rafi diyana ce mai shiga yana tsaye yana kallon yadda take shan ruwa sai mulewa kasa take tana ɗagowa sama sai da ya barta ta jigata sannan ya chire agogon hannun sa da wayar sa tare da hulan kan sa ya ajiye ya faɗa chikin ruwan kamota yayi ya daurata saman kirjin sa yana kallon face nata langwaɓar da kai tayi a kafaɗar sa tana jan numfashi "kin kyau ta da kika jika mu yanzu dame zamu koma gida? Kankame sa tayi ta kasa magana domin tasha ruwa sosai takawa yayi zuwa in da ruwan ke zuba kamar fanfo ya tsaya a dai dai wajen, ruwan na zubo musu daga kai "har yanzu baki dawo dai dai ba kenan? Sai lokacin ta ɗago kai da kyar ta iya chewa "yaya Prince dan Allah ka fitar da Ni" matso da face nashi yayi dab da nata "no ai tun da kika sani na shigo ruwan nan tofa sai ki shirya ɗaukan duk abun da zan yi" chizon sa tayi a saman lallausan lips nashi chikin shagwaɓa tace "yaya Prince wlh bana numfashi sosai ka fitar da ni daga ruwan nan kar na mutu" lasan lips nashi in da ta chijesa yayi kafin yace "kina so kenan" bai jira amsar ta ba ya haɗe bakin su waje guda ga ruwa na zuba musu daga kai yana jikasu almost 10mins suna haka kafin ya zame bakin sa daga nata yana kallon face nata yana kokarin yin magana wayar sa ta fara ringing kai kallon sa in da ya ajiye wayar yayi kafin ya dawo da kallon sa kanta gaba ɗaya ta jiggata da kyar take iya buɗe ido zame mata ɗan karamin hijabin kan ta yayi ya shiga watsa mata gashin kan ta ruwa na jika gashin kwantar da kanta tayi saman kafaɗar sa tana numfashi da kyar da kyar juyo da face na shi yayi yana kallon ta wani irin yanayi mai daɗi da annashuwa ke ratsa shi ya shagala da kallon ta bai ankara ba sai ji yayi tana kokarin sume masa a sukwane ya juya da ita ya fice daga chikin ruwan wajen motar su ya koma ya jinkina da jikin motar ya fara kiran sunan ta kasa kasa "Sister sister" da kyar ta iya waro idon ta da suka sauya daga blue zuwa jaa sosai,waro ido yayi yana kallon ta bai ɗauka ta jigata haka ba ta sha ruwa sosai buɗe gidan baya na motar yayi ya kwantar da ita dukkan su sai ɗigan ruwa suke

guntun tsaki yaja ya koma wajen da ya ajiye wayar sa ya dauko tare da agogon sa ya dawo kusa da ita kunna wayar yayi ya shiga latsawa da alama wani sakon yake turawa bayan ya gama ya duba miss call Aryan ne ya kira shi,kiran layin Aryan ɗin yayi bugu ɗaya Aryan ya ɗaga manna wayar tayi a kunnen sa daga ɗayan ɓangaren Aryan yace "blood ina ka bar wayar? Tsaki yaja kafin tace "menene?" "Na gama aikin da ka sani yanzu shigowar ka kawai nake jira amma akoi wata yar matsala" "matsalar me? "Har yanzu bai iya gane ɗan leken asirin dake chikin muba na binciki sojojin mu dukka ban samu ba" "No karka damu da wanan ni dai nace maka karka yarda da kowa idan na shigo zan kama koma wanenne yanzu dai zamuyi waya anjima yanzu akoi abun da nake" "ok to ina sister na take? Juyowa yayi yana kallon ta da kyar da kyar take numfashi sai rawan sanyi take "ban san in da take ba" dariya Aryan yayi kafin tace "amma Bgs kai fa ɗan duniya ne ka gama yiwa yar mutane mugun ta jiya instead of yau ka zauna ka bata kulawa amma sai kayi fitar ka ko? Allah dai yana kallon ka...bai bari Aryan ya gama maganar sa ba ya katse kiran yana kallon ta kawar da kansa gefe yayi yana ɗan jan tsaki ajiye wayar yayi chikin motar ya harɗe hannun sa ya kirji yana kallon sama kamar mai tunani

Almost 10mins suna haka sai ga Abdol ya danno hanchin motar sa wajen kusa motar su yayi parking sanna ya fito chikin sauri hannun sa rike da jaka mikawa Bgs jakar yayi sanna ya shiga motar sa ya juya ya koma buÉ—e jakar Bgs yayi ya fito da duguwar riga abaya ce baki kayan jikin ta ya fara chire mata sauri sauri ya sauya mata doguwar rigar sai rawan sanyi take yana kokarin chire nashi kayan yar karamar nauran dake gaban motar sa ta fara kara chikin sauri ya fasa chire kayar na shi ya rufe kofar baya na motar ya buÉ—e gidan gaba ya shiga ya kunna motar da gudun gaske ya bar wajen kai tsaye gida ya wuce dan sai rawan sanyi hiyana ke yi shi kan shi kayan jikin sa sun takura masa

Yana shiga gida bai ɓata lokacin ba ya fito ya ɗauke ta chak ya shiga chikin gida kai tsaye bedroom nasu ya wuce saman gado ya shinfiɗe ta ya wuce toilet wanka yayi da ruwa mai zafi sosai ya fito ya shirya chikin kayan sanyi dan shima daɗewar da jikakken kayan sukayi a jikin sa ya sanya yana jin zazzaɓi kayan sanyin sa ya ɗauko mata tare da safa da hula ya sanya mata tana kwance tayi shiru sosai ya shirya ta chikin kayan sanyin sa ganin har yanzu sai rawan sanyi take ya sanya ya kunna na'uran ɗumama ɗaki ya jona hand dryer da kansa ya busar mata da gashin kanta bayan ya gama komai ya duba time 2pm alwala yayi ya fito ya gabatar da sallah ya miƙe ya hauro saman gadon duba time ya sake yi 3pm saura 1h jirgin su ya ɗaga kwamciya yayi saman gadon ya jawota jikin sa ya jawo bargo mai laushi ya rufesu sosai ta shige jikin sa tana shan ɗumin jikin sa kasa kasa da murya kamar mai raɗa yace "sister are you okay now?" gyaɗa masa kai tayi alamar eh shafa kan ta ya fara yi suka yi shiru kowa da abun da yake tunani

To masu karatu sai mun haɗe gobe a Naija zamuga ya wasan zata kaya akoi fa shagali akoi sharholiya yanzu zaa fara buga asalin game ɗin mu damalmale da ku gobe zamuga wazaiyi winning 💃💃

💖The talent troupe writer's 💖

💋Duk Karfin Izzata 💋29

By Star Lady

Page 30

Uk
Chapter 68 · 0% Book details