← Book details Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 80

Sashe 76

Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga palo yake jiyo kukan ta har ya kai cikin bedroom ɗin frog jump take tana kuka da hawaye sharɓa sharɓa lokacin guda yaji ta bashi tausayi, wucewa yayi ya zauna a bakin gado yana kallon yadda take frog jump da kyar da kyar,kewaye ɗakin take da frog jump har ta kariso ta gaban sa kama dogayen kafofin sa tayi chikin shasshekar kuka ta fara magana "yaya Prince dan Allah kayi hakuri wlh ba zan sake ba na tuba wanna frog jump ɗin akoi wahala na gaji bazan iya ba dan Allah kayafe min" hannu ya sanya ya ɗagota amma ta kasa miƙewa tashi yayi ya ɗaga ta chak ya ɗaura ta saman gadon tare da zama gefen ta yana kallon face nata "yau na miki afuwa ne saboda dalili ɗaya idan kika sake yimin abun da kika min yau sai na lahira ya fi jin daɗi" faɗowa tayi saman faffaɗar kirjin sa tana shasshekar kuka tana faɗin "amma yaya Prince ba kai kace idan na samu miji zaka min aure ba?" ɗago haɓar ta yayi yace "eh ni nace haka amma ai ba mijin kan hanya nace ki samo ba ko?" hannunta ta zuro ta bayan sa ta kewaye sa da shi tana faɗin "to ai ba zan samu wani mijin ba idan a gida ne" yatsa ya ɗaura mata a saman bakin ta yana faɗin "shiiiii ya isa maganar" "yaya Prince dan Allah.....ba ta kai ga karisa maganar ba ya ɗaura hannu sa saman bakin ta yana girgiza mata kai, shiru tayi ta kwantar da kan ta saman kirjin sa. Zame hijabin kan ta yayi ya mai da shi wuyar ta ya fara shafa lallausan bakin gashin kanta shafa bayan sa ta fara yi itama, lokaci guda yayi saurin raba ta da jikin sa yana mamakin how comes yake ji feeling da ta taɓa shi? runtse ido yayi na yan mintoci kafin ya sake buɗe wa miƙewa yayi a zafafe ya nufi wajen mirror da sauri ta riko hannun sa ta marairaice murya tace "yaya Prince dan Allah ka mai da ni asibiti ina son ganin diyana" kwace hannun sa yayi ya wuce gaban mirror yana faɗin "an jima da yanma zamu koma" ya kai karshen maganar dai dai lokacin da ya buɗe drawer mirror ya fito da kwalin alluran yana dubawa

To masu karatu sai mun haÉ—u gobe idan mai dukka ya kai mu akoi fa chakwakiya

To yan Duk Karfin Izzata comments section group Brigadier general Safras ne ke magana sako ya iso kunnena irin zagin da kuke min a group ya iso ni to ina son ku buɗe kunnenku ku saurare ni idan kuka bari rai na ya ɓaci zan wurgo muku bom ya tarwatse ku 😡😎😹😹😹

💖The talent troupe writer's 💖

💋Duk Karfin Izzata 💋

By Star Lady

Page 33

Kurawa alluran ido yayi kamar mai tunanin wani abun,abun da mamaki gasu dai alluran da ya saba yi ne,5mins ya ɗauka yana kallon alluran kafin ya ajiye ya fito da kayan test yana kokarin jan jinin jikin sa domin ya tabbatar wa kan wani allurane ya shiga jinin jikin nashi,sai jin hiyana yayi ta kwanta a bayan sa tana faɗin "yaya Prince ni dan Allah kasa a....bata kai karshen maganar ba ya fisgota da karfi ya dawo da ita ta gaban sa rai a matukar ɓace yace "idan kika kuskura kika sake kusan tata ran ki yayi dubu sai na ɓata miki get out!!" ya kai karshen maganar tare da sakin ta,da gudu ta ɗauki wayar ta dake gefen gado ta fice daga ɗakin.

Tana fita ta kira layin Aryan bugu ɗaya ya ɗauka manna wayar tayi a kunnen ta cikin sauri tace "yaya Aryan ba zan iya ba nayi kamar yadda ka rubuta min a massage nayi kokarin shashantar da shi karya gane amma yace na fice masa a ɗaki" daga ɗayan ɓangaren Aryan yace "me yake yi yanzu? "Gwada kan sa yake yana son tantance wani allura yayiwa kan sa dan naga ya nemi kwalban alluran da yayi ɗazun ɗin bai gani ba" dogon numfashi Aryan yaja tare da sauke nauyayyar ajiyar zuciya kafin yaci gaba da magana "ni na dauke kwalbar alluran bayan na ɗauke ne na dawo masa da alluran sa na asali dan nasan zai iya zuwa ya bincika na manta cewa bgs ya wuce nan yanzu wlh nasan idan ya gane ba mai kwatata sai Allah kuma tun da ya fara bincike a kai sai ya gane bana son ki shiga case ɗin nan dan haka ki goge duk wani text dana tura miki kiyi kamar baki san komai ba sanna karki yarda yau ki kara haɗuwa da shi zan sa Ammi ta bashi umarnin a ɗauko ki a kawo ki hospital sai yamma zaki koma gida" murya na rawa ta fara magana "yaya Aryan ni fa ina tsoron in ga kuna samun matsala da yaya Prince saboda ni ba na son ganin hakan" "karki damu da hakan ke dai kije ki shirya da wuri yanzun nan Shahram zai kawo ki nan dan ban son ki zauna kusa da shi yau za'a iya samun matsala dan ina da tabbacin yana cikin matsanancin ɓacin rai" "to" kawai tace tare da ciro wayar daga kunnen ta ta katse kiran cikin sauri ta karisa Part ɗin Ammi gudu gudu ta shirya tana fitowa ta duba time 1:30pm komawa tayi ta ɗauro alwala ta gabatar da sallar azhar sanna ta kira Aryan ta sanar masa ta gama shiri umarni ya bata akan ta fito Shahram ya kawo ta idan ya kawo ta sai suce Ammi ce tace a ɗauko ta idan Bgs ya tambaya haka ko akayi Shahram ya kai ta asibiti tana shiga ta samu yaya Aryan a wajen parking space yana jiran ta a tare suka wuce ɗakin da su diyana ke kwance.

Ammi da Ummi suna zaune saman sofa dake cikin ɗakin suna yar hira gefen gadon da diyana ke kwance ta zauna ta zuba mata ido har wani hasken wahala ta kara ta shagala da kallon diyana sai ganin hannun ta na motsi tayi cikin sauri ta miƙe tsaye tana faɗin "yaya Aryan tana motsi" a tare suka kariso wajen shi da su Ammi. zuba mata ido sukayi suna kallon ta tun bata buɗe ido ba ta fara sambatu "bana son ka yaya Aryan mugu azzalumi....hiyana bata bari ta karisa maganar ba ta rufe mata baki tana faɗin "diyana!!ki buɗe idon ki kinsan me kike faɗe kuwa? da karfi ta waro manya manyan idon ta waje wadda sukayi ja sosai suka kumbura kyakkyawar fiskar hiyana ta fara cin karo da shi ganin ta ɗan nitsu ne ya sanya hiyana ta zame hannun ta daga kan bakin ta kamar jira take ba tare da ta lura da su Ammi ba ta fara surutu "hiyana wlh yaya Aryan mugune azzalumi kuma....sake rufe mata baki hiyana tayi tana girgiza mata kai "diyana koma me yaya Aryan ya miki bai kama ta kice masa mugu ba wato kin manta karatun da na koya miki ko ba'a zagin miji kome zai miki kici gaba da hakuri Allah na kallon ku kuma da ki cuci mujin ki gara shi ya cuce ki karki kara zagin yaya Aryan zaki shiga wuta wato ke duk karatun ma da na ke koya miki bakya ɗauka ko?" ta kai karshen maganar tana zama kusa da ita sai lokacin diyana ta ga su Ammi dake tsaye ta bayan hiyana "kuka ta saki tana kallon Ammi tana faɗin "Ammi dan Allah ki mai dani wajen Aunty farida"jiki ba kwari Aryan ya juya ya fice daga ɗakin yana godewa Allah da sanya hiyana ta rufe masa bakin diyana ba dan haka ba ai da ta kwanto masa ruwa

Zama Ammi tayi kusa da ita tare da riko hannun ta cikin nitsuwa ta fara bata hakuri da nasiha mai ratsa jiki da kyar suka samu diyana ta hakura ta dai na kuka amma ta kafe akan bata son yaya Aryan sai dai ya sake ta bazata zauna da shi ba su Ammi basu da zaɓi dole su yardan mata akan yaya Aryan zai sake ta sai a mai data gidan Aunty farida da haka suka samu tayi shiru. ganin ta hakura tayi shirune ya sanya hiyana ta miƙe tabi bayan yaya Aryan

Chan ta hangosa zaune saman kujera kusa da shi taje ta zauna tana faɗin "sannu da hutawa yaya Aryan" ba tare da ya kalle ta ba ya fara magana "yau na kwanto kura nayi abun da ban taɓa yi ba ina da tabbacin idan Bgs ya gane alluran da na sanya mishi idan ba Ammi ba ba wanda zai iya tare wanna rikicin ban taɓa tunanin Bgs zai gane alluran nan ba domin dana canza alluran bayan yayi wa kan sa na dawo na ɗauki wayan da na sa masa na mayar masa da na asalin na shi na ajiye dan in yazo ya ga masu kyau ɗin ne na ɗauki guda ɗaya na fasa na zubar da ruwan na ajiye masa kwalbar a dustbins domin idan yazo bincika wan da yayi wa kan sa ya ga kwalbar ban taɓa tunanin jinin jikin sa zai bincika ba hmmmmm akoi kura" "to yaya Aryan wani allurane wanna ka sa masa yayi da har kake ganin idan ya gane akoi matsala?" dogon numfashi yaja tare da sauke ajiyar kafin yace "hmmmmm sister ba zaki gane allun ba ke dai bari na ɗan miki example idan kayiwa kan ka wanna alluran to ko kayi wancan da Bgs yake bazata maka amfani ba shi ya sanya nake tsoron rikicin da zamuyi da shi yau" "to amma yaya Aryan daman wani irin allura yaya Prince yake wa kan sa ne? sai lokacin ya ɗago ya kalle ta chanza topic ɗin hiran yayi da cewa "ya jikin my jidda ta dai na kukan ne? gyaɗa masa kai tayi kafin tace "eh ta dai na kuka" miƙewa tayi yana faɗin "bari na duba ta" miƙewa ita ma tayi suka jera zuwa cikin ɗakin.
Chapter 76 · 0% Book details