← Book details Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 80

Sashe 59

Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bugu ɗaya Aunty farida ta ɗaga chike da damuwa hiyana ta fara bata lbr abun da ya faru dariya Aunty farida tayi bayan ta gama jin bayanan hiyana chikin nitsuwa ta fara magana "oh su Safras manya to an faɗa masa mata wasa ne wato har da wani che miki ki tsaya a matsayin ki na sister ko? Lallai zai gane shayi ruwane kinsan yanzu me abun yi? "Aa Aunty farida ban sani ba sai kin faɗa" ta faɗi maganar tana girgiza kai "na shan yau ba zai dawo da wuri ba ki tsara wanka ki shakwalliya ki shirya masa duk wani abun da kika san zai bukata kafin ya dawo,yanzu idan mun gama waya ki kirashi ki masa ya isa wajen Aiki lfy idan kuma kika kira bai ɗauka ba to ki masa massage sanna idan ya kusa dawowa nan ma ki sake kiran sa idan bai ɗauka ba ki masa massage ki tambaye sa ya Aiki sai ki kara masa da ya sawo miki chocolate a hanya idan har ya sawo miki chocolate ɗin to ba shakka ya fara son ki idan kuma bai sawo ba to fa muna da sauran aiki a gaban mu sanna idan ya dawo bayan kin gama chire masa ta kalma kin masa duk abun da ya dace idan yayi wanka ya shirya ya zauna yana hutawa sai ki tawo ki zauna a kan chinyar sa tun da yanzu ba zai bugeki ba kina da daman zama a jikin sa ba yadda zai yi da ke idan yace ki tashi karki ta shi ki kwanta a kirjin sa chikin shagwaɓa kice yayi hakuri idan ya fara yi miki tsawa ki sa masa kukan shagwaɓa tare da sanya hannun ki a wani shashe na jikin sa kina wasa da shi ko ki sanya hannun ki chikin gashin kansa kina shafawa kina masa kukan shagwaɓa,wlh dole ya sauko idan kika masa haka saura kuma kije ki masa akasin hakan kin san idan kika kure sa ya zuchiya wlh mantawa zanyi da umarnin Ammi ya miki ɗan ban zan duka kina jina ko? Tun da Aunty farida ta fara wanna bayani hiyana ta sunkuyar da kai kasa kamar a gaban Aunty farida dan take "hiyana ba dake nake magana bane nace kina jina!? Kasa kasa chikin jin kunya tace "eh Aunty farida ina jin ki kuma Nagode" "good yanzu dai ki tashi ki fara aikin abubuwan da na faɗa miki idan da dama ki shiga kitchen ki masa girkin gargajiya da kanki dan na san ya gaji da chin abincin turawan nan tukunnan ma kin iya girkin ne? kar kije ki masa shirme ko da yake Auta na nan zata nuna miki duk abun da ya dace kiyi tuwon shinkafa da miyar egusi zaki masa dan yana matikar son tuwon shinkafa da miyar egusi kinji? "Eh Aunty farida naji kuma In Sha Allah zanyi yadda kikace "yauwa nama fasa Auta tayi maki ni zan koya miki yadda ake komai ina system ɗin yayan naki? "Ya tafi da shi" "ok to tun da ya tafi da shi idan lokacin yin girkin yayi sai muyi video call na nuna miki yadda zaki yi komai yanzu dai ki tashi ki fara yin abubuwan da na faɗa miki kuma saura ki sa hijabi idan ya dawo kaya zaki sanya waɗan da dasu da babu duk ɗaya ne kina ji na?" chikin sauri tace "eh Aunty farida naji" "good to tashi kije ki fara duk abun da ya dace" "to" hiyana tace tare da chiro wayar daga kunnen ta ta katse kiran

Layin Bgs ta fata kira bayan ta kammala waya da Aunty farida sau uku tana kiran layin amma shiru bai ɗaga ba, massage ta tubuta masa kamar haka "yaya Prince ya Aiki fatan ka isa lfy? Ni dai ba zan gaji da ce maka kayi hakuri ba" Tana gama turawa ta ajiye wayar ta buga tagumi tana tunani kamar daga sama taji karar wayar alamar shigowar sako chikin sauri ta duba sakon zubur ta miƙe ganin sakon yaya Prince ne "I'm good" shine abun sa ya rubuta a sakon murmushi ta fara yi tare da rungume wayar a kirjin ta tana faɗin "kai yaya Prince shine kana ganin kirana kaki ka ɗaga ko to zaka dawo ka same ni ne Allah yau na san me zan maka
Bgs dake zaune chikin katafaren Office na shi yana kallon ta ta chikin system É—in dake gaban sa ya waro ido waje jin abun da tace kasa kasa yayi magana wadda ina da tabbacin ko shi bai ji me yace ba lokaci guda kuma ya ja tsaki tare da kawar da system É—in daga gaban sa ya jawo cup É—in tea ya fara sha a hankali

Ita kuwa sai surutun ta take tana juyi a tsakiyar ɗakin tayi nisa chikin abun da take wayar ta ya fara kara tana dubawa sai taga number yaya Aryan chikin sauri ta ɗaga kira tare da manna wayar a kunnen ta chikin nitsuwa ta fara magana "yaya Aryan ina kwana? Daga ɗayan ɓangaren diyana ta kwashe da dariya tana faɗin "Kamar wata mutuniyar kirki har da kashe murya wani wai yaya Aryan ina kwana to ba yaya Aryan bane Aunty diyana ce" dafe kai Hiyana tayi kafin ta saki cool murmushi ta fara magana "amma diyana baki da kirki wai har yanzu baki hankali ba" tsaki diyana taja kafin tace "ni ba wanan ne ya sanya na kiraki ba kin san me ni so nake ki che wanan mugu mai kama da ke ɗin maza ya sake ki ki dawo gida idan ba haka ba wlh shaiɗanun yara mugaye zaki haifa" lokacin guda hiyana ta ɗaure fuska chike da jin haushi zagin Bgs da diyana tayi ta fara magana "ke diyana kina da hankali kuwa kin san wanene yaya Prince awajena? miji nane fa ina mutuwar son shi ina kaunar sa fiye da rayuwa ta ina son farincikin sa fiye da nawa bani da buri a duniya da ta wuche yau na ganni gani ga shi mun zauna muna hira idan har ba zaki tayani son abun da nake so ba to bai ka mata ki zageshi a gaba na ba ni ina son kaya na a haka ke in ta kai ce miki komai yaya Prince yayi burgeni yake komai nashi kyau yake min komai idan yayi kyau take masa kamar dan shi akayi abun Kum.... Bata karisa ba diyana tace "ya isa haka hajiya soyayya sai yanzu na gane chewa nayi kuskure yanzu dai ba abun da zanche sai dai in che ki chi gaba dan son yaya Prince Allah ya sanya ya soki shima ko dan maraicin mu da wahalar da kika sha a kan mu Allah ya miki zaɓi mafi alkhari" ajihar zuciya hiyana ta sauke kafin ta chi gaba da magana "amin diyana ki rinƙa tayani da addu'a Allah ya sa yaya Prince ya so ni ko da kwatan son da nake masa ne amma na sha wahala sosai a kan sa" "in Sha Allah zai so ki hiyana zai so ki sosai ma in dai yana da tausayi da imani to tabbas zai so ki in dai yana da ido kuma idan sa na gani da kyau to dole ya soki in dai yana da ilimin addini kuma yana amfani da ita to dole ya soki zan tayaki da addu'a"

taɓe baki Bgs yayi yana kallon su ta system nashi yana jin me suke faɗe abun ma har mamaki yake bashi "wai yanzu yar yarinyar nan ta san me so tab gaskiya Abba ya chucheni ya haɗa ni da wahala" dogon tsaki ya kuma ja tare da miƙewa ya fice daga office ɗin

Aɓangaren hiyana kuwa sosai ta bawa diyana lbr tun zuwar su Uk har yau sosai suka sha hira diyana ta jajan tawa hiyana akan wahalar da ta sha, ji suke kamar su haɗiye juna saboda so da kauna har sun yi sallama hiyana ta kuma chewa "diyana karfa ki faɗawa kowa hiran da mukayi" "ba zan faɗa ba hiyana na" godiya Hiyana ta mata sanna sukayi sallama ta ajiye wayar ta ɗauki hijabi ta sanya ta fito ta nufo part ɗin su Zahra

Kano Nigeria
Chapter 59 · 0% Book details