← Book details Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 80

Sashe 71

Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

har 1:30Am basu yi barci ba a hankali ta ɗago kai kasa kasa kamar mai raɗa tace "yaya Prince baka sha fruits ɗin ba" mai da kan ta yayi ya kwantar dan bai san ta motsa ko kaɗan idan ta motsa za'a iya samun matsala da kyar ya iya buɗe baki ya fara magana dan yana cikin wani hali "no ba zan iya sha ba" "to yaya Prince in tafi wajen Ammi? yatsa ya ɗaura mata a saman lips nata kafin yace "karki sake magana kiyi barci dare yayi" shiru tayi tana son komawa part nasu amma ba hali kunya take ji da safe ta tashi ta haɗa ido da Ammi ita da tace zata je ta dawo da haka har barci ya ɗauke ta. Sai 2:30 sanna ya kwantar da ita ya miƙe ya nufi toilet wanka yayi ya fito ya sanya wani kayan barcin ya haye gado ya kwanta ya juya mata baya

kasa barci yayi ji yake tamkar ya rasa wani abu gaba ɗaya ya rasa me ke masa juyowa yayi ya jawota jikin sa nauyayyar ajiyar zuchiya ya sauke tare da ja musu blanket ya rufe su da haka barci ɓarawo ya ɗauke sa

5:30am

Tana idar da sallar asuba ta naÉ—e daddumar sauri sauri tana kokarin fita daga bedroom nashi ta tafi part É—in Ammi sai sauri take kar ya dawo masallaci ya same ta. dai dai zata fita palo shi kuma yana shigowa karo sukayi kan ta ya bugi faffaÉ—ar kirjin sa dake tsaye dam dam baya tayi zata faÉ—i yayi saurin damko wuyar hijabin ta ya fiskota ta faÉ—a saman faffaÉ—ar kirjin sa a tare suka sauke ajiyar zuchiya kasa kasa yace "where are you going? "É—akin mu zanje" "na baki izinin tafiya ne? Chikin sauri ta É—ago kai yana kallon sa "izinin kuma? Ta tambaya tana saukar da idon ta kasa "eh izini" "yaya Prince idan matar Aure ce iya mijine kawai ake neman izinin sa idan za'a je wani waje idan kuma budurwa ce to wajen baban ta zata nemi izini ka ga kai kuma a matsayin sister ka É—auke ni kaga kenan ba sai na nemi iznin ka ba" matse bakin ta yayi da É—an karfi kafin yace "ni yayan kine kuma ya zama dole ki nemi izini na kafin kiyi abu ba lallai sai miji ko uba ba awajen yaya ma ana neman izini" hannun ta sanya ta zame hannun sa daga rikon da yayi wa bakinta tare da riko yatsar sa manuniya ta sanya a bakinta ta É—an chiza chikin wasa "wash" ya furta chikin zafin nama ya sunkucheta ya goma da ita chikin bedroom

A tare suka faÉ—a saman gadon ya jawota kirjin sa tare da ja musu blanket chikin raÉ—a yace "kiyi barci" lumshe ido tayi ta lafe a jikin sa ba jimawa barci yayi awon gaba da ita dan dama bata sami ishesshen barciba, hannun sa ya tura cikin hijabin ta yana É—an shafa tula tulan ta a hankali har barci yayi awon gaba da shi

To masu karatu sai mun haÉ—u gobe idan mai dukka ya kai

Duk Karfin Izzata comments section group ina matikar godiya da comments naku yana ƙaramin karfin guiwa sosai Allah ya bar zumunci da qaunar juna 🥰🥰

💖The talent troupe writer's 💖

💋Duk Karfin Izzata 💋

By Star Lady

Page 31

8:30am ya farka a hankali ya waro manya manyan green eyes nashi yana kallon sama na yan mintoci kafin ya sauko da idon sa saman gadon ta gefen sa wayam babu kowa hiyana ta tafi wajen Ammi yunkurawa yayi ya tashi zaune,zuro ƙafarsa kasa yayi kafin ya miƙe ya nufi wajen mirror A box ya ɗauko yana kokarin haɗa allura Aryan ya shigo ɗakin bakin sa ɗauke da sallama ta chikin mirror ya karewa Aryan kallo kusa da shi Aryan yazo ya tsaya chike da zolaya yace "ina kwana yaya Prince? yanzu kana gida ka tashi daga oga Bgs ka dawo yaya" harara bgs ya wurga masa ba tare da yayi magana ba ya chi gaba da haɗa alluran sa,chikin zafin nama Aryan ya kwace alluran daga hannun sa a sukwane Bgs ya ɗago yana kallon sa,chikin jin haushi Aryan ya fara magana "haba my blood wai bazaka bar alluran nan haka ba sai ka chutar da lfyn kane? Kayi hakuri haka ka rungumi matar ka duk da na san chewa mawuyacin abune sister ta iya ɗaukan ka yanzu amma zaka iya lallaɓawa kuna wasa haka nan pls my blood karka sake alluran nan dan Allah" miƙa wa Aryan hannu yayi chikin kwanchiyar hankali yace "bani" "no bgs gaskiya ba zan baka ba kuma bazan taɓa bari ka sake yiwa kan ka alluran nan ba gaskiya" a fusache bgs yace "ba Safras zaka bawa ba Brigadier general Safras zaka bawa" Aryan ya gane me Bgs ke nufi jiki ba kwari ya miƙa masa alluran,ansa Bgs yayi ya gama haɗawa chike da ba da umarnin ya dubi Aryan "kai ɗaure min hannun nan ka nemomin jiniya" ba musu Aryan ya ɗaure masa hannun ya nemo masa jijiyar chike da bacin rai ya juya ya koma bakin gado ya zauna yana chije laɓaɓa. ta chikin mirror bgs ke kallon sa ajiye allura yayi saman drawer mirror ba tare da ya juyo ba ya fara magana "my blood taya za'ayi nayi abun da zai saka bakin ciki na gwada kane naga zakamin taurin kai ne ko dai, duk abun da zai sanya ɗan uwana farinciki ina son shi amma dai bazan iya ansan sister a matsayin mata ba domin bani da ra'ayin hakan ina mata addu'ar samun miji na gari" murnushin Aryan ya saki tare da miƙa wa ya dawo kusa da shi hannu ya sanya ya kwance masa hannun sa daya ɗaure masa dan neman jijiya "why bazaka iya ansan sister a matsayin mata ba? Me ta rasa? "she's too small for me" murmushi Aryan ya kuma yi kafin yace "ka jarraba ta zata iya kuma wlh you will enjoy.....bai kai karshen maganar ba yayi shiru" "Aryan wani lokaci idan kana magana kamar baka sanni ba let me tell you the truth babu mace a tsarin rayuwa ta kwata kwata duk abun da ka gani tsakani na da sister ina yin shine domin idan mum zo kar su Abba su sani a gaba da zanchen da ba shi ba ba karamin daure wa nakeyi wajen biyewa yarinyar nan ba wlh ji nake tamkar a kabari nake idan yarinyar nan tana kusa dani domim damuna take da magana da sauran su ina son kasani ina yin hakan ne kuma dan farincikin iyaye na amma ni babu wata mace da ta isa ta zauna kusa da ni babu mata a tsarina" a tsorace Aryan ya ɗago yana kallon sa ganin yadda yayi maganar in a serious matter "Bgs wai me kake faɗe ne? kana nufin dan zaku zo Naija ne ya sanya ka shirya wa sister irin wanan abun to ina son ka sani idan kayi kuskuren yin hakan wlh sai Allah ya hukun taka kasan da chewa sister tana mutuwar son ka kuma ita yanzu duk tunanin ta da gaske ka sauko ka fara kulata kasani hakan da ka mata zai sanya ta kara son ka ne pls Bgs ya isa haka chutar da zuciyar yanmata da kake yi abeg karka yiwa sister hakan" ɗaure fuska sosai Bgs yayi kafin ya fara magana "oh now kayi girman da zaka tsaya a gaba na kama faɗa min magama kenan? To ina son ka buɗe kunnen ka kaji ni na faɗa da babban murya babu mace a tsarin rayuwa ta mata rauni ne daga tarayya da nayi da ita na 2days har tasa nayi losing abubuwa da dama wanna shine karo na karshe idan ka sake zuwa min da maganar mace idan ranka yayi dubu sai na ɓata maka" yana kai karshen maganar ya ɗauki alluran sa chikin ɓacim rai ba tare da ya ɗaure hannu ba ya damke jikin sa ya nemi jijiya yayi wa kan sa alluran chike da bacin rai yayi wurgi da sirinjin alluran ya nufi toilet.
ajiyar zuciya Aryan ya sauke lamarin Bgs ya fara bashi tsoro jiki ba kwari ya juya ya nufi hanyar fita Ba shiri ya ja birki ganin Hiyana a tsaye a bakin kofar shigowa É—akin hannun ta É—auke da kayan breakfast na Bgs ga hawaye wani na bin wani a kan kuncin ta juyawa yayi ya kalli kofat toilet É—in kafin ya sake dawo da kallon sa kanta yana kokarin yin magana ta juya da sauri har tana haÉ—awa da gudu ta fice daga É—akin chikin zafin nama Aryan yabi bayan ta a tsakiyar palon ta ajiye masa breakfast É—in ta wuce waje da gudu bayan ta Aryan yabi shima har yana haÉ—awa da gudu tsoron sa É—aya karta faÉ—awa Ammi duk da ya san Hiyana macece mai hakuri da sirri.

kasan chewar tasan yaya Aryan na bin bayan ta sai bata shiga part na Ammi ba sai ta nufi wajen basket ball É—in su yaya Omar ajiyar zuciya Aryan ya sauke lokacin daya ga ta sauya hanya bata shiga part É—in Ammi ba

Zaune ya iskota a kasa tayi zaman yan bori ta chusa kan ta chikin chinyoyin ta tana kuka takawa yayi ya kashe Cameran dake wajen kafin ya kariso gaban ta ya tsugunna tare da sanya hannu ya É—ago fuskar nata gaba É—aya fuskar tayi jaga jaga da hawaye har da majina chikin sanyin murya yace "yi kuka yi kuka sister kiyi kuka sosai dan ki samu sauki a zuciyar ki nima da da dama dana tayaki kukan" kamar kara ingiza ta Aryan yayi sosai take kuka take shassheka.
Chapter 71 · 0% Book details