← Book details Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 80

Sashe 2

Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhamdulliah Alhamdulliah kawai mutanen dake chikin palon ke furtawa chikin sanyin murya Abba ya fara magana "yanzu mace mai irin wan nan halinne Safras zai che baya so lallai kuwa da É—azun ka saki hiyana da ka tapka babban kuskure arayuwar ka" "Abba me kake shirin faÉ—ane wache hiyanar kuma ba dai hiyana da tamin addua ba Abba nifa yanzu ma da kaga nazo palon nan, nazo sanar da kai chewar ina son hiyana ne ina son ta kuma zan Aure ta,

tirkashi chike da tashin hankali Khalid ya fara magana "Ahmad sai dai kayi hakuri domin hiyana dai matar Bgs che yanzu, kai in ta kai che maka gaba É—ayan mu yau Aka É—aura auren mu, chikin tashin hankali Ahmad yace "yanzu shike nan hiyana tayi Aure innalillahi wa inna ilaihir rajiun hasbunalluhu wani mal wakil, shikenan ba komai nasan haka Allah yaso wai ina Aiman da Aryan da Bgs ne? A sukwane Abba ya É—ago yayi saurin chewa Aiman baya nan yana Maiduguri wajen Aunty farida, juyawa Ahmad yayi yanufi hanyar fita yana faÉ—in zuwa Maiduguri ya kamani a yanzu nan kenan dan ina matikar son naga É—an uwana kuma shima nasan yayi kewana sosai zai ji daÉ—i sosai idan ya ganni yana kai karshen maganar ya fice daga palon ba tare da ya lura da yanayin fuskokin su Ammi ba Allah ma yasa Aiman na kwanche a kujerar bayan ne shiyasa Ahmad É—in bai ganshiba, dafe kai kawai Abba yayi yana addu'ar Allah ya kawo masu mafita dago ido yayi chikin bada umar ya fara

"Kar wanda ya kuskura ya sanar da Ahmad rasuwar Aiman yanzu ku kyalesa ya tafi Maiduguri dan musamu muyi jana izar Aiman É—in, idan É—aya daga cikin ku yayi kuskuren sanar dashi yanzu tofa za'ayi gawa biyu kunga yanzu ya tashi daga chiwo dan haka ku kyalesa, Abba ya karisa maganar dai dai lokacin da hiyana ta farfaÉ—o

Sambatu ta fara yi tana faɗin "wayyo Allah na lamrat ta mutu diyana ta ɓata na shiga uku na dan Allah wadda ya sace diyana ya dawo da ita ya ɗauke ni ko kashe ni ma yake son yi ya kasheni ni dai ya dawomin da yar uwa, wayyo Bappa na Inna ta" gaba ɗaya palon ba wanda bai tau sayawa hiyana ba harta Aunty Amarya wadda yanzu mutuwar Aiman yasa tafara na damar rayuwar ta da abun da tayi

miƙewa Abba yayi ya koma kusa da ita hannun ta ya kamo chikin nashi murya kasa kasa ya fara magana "hiyana kiyi hakuri kinji jarabawa che Allah ya jarabce mu gaba ɗayan mu kiyi kokarin muchi jaraban nan kinji? Kuma ita lamrat bata rasuba doguwar suma tayi zata farfaɗo nan ba da jimawa ba, diyana kuma zamu gano ta kinji ko? Jin abun da Abba yace yasa hiyana miƙewa zaune da sauri tana faɗin "yanzu lamrat na raye wayyo Allah Alhadulillah Alhamdulliah Allah na godemaka, shiru Abba yayi yana kallon ta tunani yake
ya wan nan marainiyar Allah zataji idan ta samu lbr yanzu matar Safra che ita mutumin da ya nuna mata tsantsar tsana da kiyayya agaban idon ta, gakiya nayi na damar haÉ—a wan nan Aure dan nasan mawuyachin Abune Safras yaso yarinyar nan tun da ya furta da bakin sa ya tsaneta gaskiya nayi ganganchin sauri haÉ—a Auren nan.

To masu karatu bari mu leko yaya Aryan kuma muga wani wai nar yake toyawa tun da munji yadda Aunty amarya tafara karɓan hukunchi abubuwar da ta aikata hakkin mutane ya fara bibiyan ta

Maiduguri

Gaba É—aya chikin birni da kauye Aryan ya baza sojojin sa ta ko ina an rufe hanyar shige da fice duk in da yake tsammanin zai ga diyana awajen an duba babu ita babu lbr, yashiga tashin hankali mara misaltuwa yama rasa ina zai sanya kanshi bayaji baya gani haka ya baza sojoji ta ko ina anyi sanarwar a gidan redio jaridu gidan Tv amma shiru babu diyana ba lbr Aryan kamar zai zauche wani azaba da raÉ—aÉ—i yakeji a zuchiyar sa sai jin faÉ—uwar gaba yake time to time kuma yana yawan jin voice na Aiman a kunnen sa yana faÉ—in "É—an uwana ina kaunar ka ina matikar son ganin farinchi kin ka gaba É—aya Aryan ya rasa meke damun kwakwalwa sa da take ta tariyo masa voice É—in Aiman

To masu karatu dan Allah kumin afuwa wlh ina hanyane shiyasa kuma bani da charji amma idan na isa gida na samu charji to gobe zaku sammu sakon zafafan page har 2 yanzu dai ayi kuskuren baki da wan nan ina ganin addu'oe ku ina godiya

NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)

*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)

*5,YA FITA ZAKKA*
by(mum Sayyid)

*Baby*
By (Mhiz innocent)

*💫STAR LADY💫*2

💖The Talent Troupe Writer's 💖

*DUK ƘARFIN IZZATA*

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

Book 2

*Episode 2*

......sosai Aunty amarya take kuka kamar ran ta zai fita sai rarrashin ta Ammi da Ummi suke chikin nitsuwa Abba ya fara magana "ku tashi muyi musamu mu kai Aiman ma kon chinsa, ku kuma Aisha ku tashi ku tafi kowa tayi part nata, kukan ya isa yanzu ba abun da Aiman ke bukata face Addu'a, kuma ina son sanar daku chewa ban yar ku sanar dasu farida yanzu ba ku bari sai bayan kwana biyu domin idan kuka sanar dasu yanzu tofa dole Aryan da Ahmad zasu samu lbr kuma kunsan me zai biyo baya idan suka sani a yanzu, yana kai karshen maganar ya miƙe ya fiche daga ɗakin miƙewa su Ammi ma sukayi gaba ɗaya suka fice sai kuka Aunty amarya take kamar ranta zai fita.

After 8 days da rasuwar Aiman, gaba É—aya family sun haÉ—u a palo Abba, harda su Aunty mardiya Su Aunty farida gaba É—aya family Abba sun haÉ—u A nitse Abba ya fara magana

"Duk kan ku ina mai baku hakuri da rashin da mu kayi san nan ina rokon Allah da ya baku hakuri da juria rashin É—an uwan ku, a tare suka haÉ—a baki wajen chewa Amin, sun kuyan da kai kasa Aryan yayi sai furzar da iska mai zafi yake daga bakinsa chigaba da magana Abba yayi

"Safras Khalid Fahad Yusuf Aryan duk da chewa kai Aryan matar taka bata nan Amma In Sha Allah zamu gano ta, to ga amanar Æ´aÆ´ana nan na baku ku kulamin dasu idan ni bana ganin ku to kusani Allah na ganin ku musamma Safras Aryan Yusuf Fahad kusani marayu kuka Aura idan kuka chutar dasu wlh Allah ba zai kyale kuba.

Chikin rashin fahimtar Aunty amarya tace ranka ya dade ban gane me kake son kace ba wai wasu ya'yan naka kake maga kuma amanar wasu Æ´aÆ´an ka basu? Dawo da kallon Abba yayi kansu ya chigaba da magana

"Kamar yadda kuka ji na faɗa hakane gaba ɗaya yaran nan na musu Aure nan dai Abba ya basu labarin yadda ya haɗa Auren nasu da kowa da matar sa, chike da tashin hankali da ruɗu hiyana ta ɓoye fuskantar a chikin chinyoyin ta saboda wani kukan bakinchiki da yazo mata shike nan na shiga uku na yaya prince ne mijina wayyo Allah ni nasan rayuwata tazo karshe kenan.

Chikin ɓachin rai Aunty amarya ta fara magana "wlh ban yar da ba tayaya za'ayi a haɗa ɗana da wanchan kazamar yar kauyen, dawo da kallon ta tayi kan Aryan dake zaune ya sunkuyar da kansa kasa yana kukan zuchi dan tun lokacin da ya samu labarin rasuwar Aiman kullun chikin kukan zuchi yake ya koma shiru baya magana bayama fitowa waje kullun yana kwanche a ɗaki

"Kai Aryan idan har na isa da kai to ka saki yarinyar nan yanzu dan ni bazan haÉ—a zuri'a da masu kiwon shanu ba, chikin jin haushi Aunty Maryam tace "haba Aunty amarya dan Allah ki kyale yaya Aryan yaji da abun da yake ji mana" "zaki min shiru ne ko sai na zabga miki mari wlh yau idan kunga Aryan bai saki diyana ba tofa mutuwa nayi tana magana tana huchi kamar wata zakanya

"Ba yau ba yanzu zan rubuta wasiya idan kika kuskura koda mutuwa nayi ki ka sanya Aryan ya rabu da matar sa tofa sai kin fuskanchi hukunchi mai tsanani gaske" chewar Abba
Chike da izza Aunty amarya tace "wlh babu wan da ya isa yasa na bar ɗana ya zauna da wan chan kazamar yarinyar, rai a matukar ɓache Bgs ya miƙe tare da miƙar da Aryan ya riko kafaɗar sa suka nufi waje tun lokachin da Aryan yasan Aiman ya rasu kullun yake chikin rashin lfy bai da wani kuzari sai yawan tunani

Miƙewa Aunty farida tayi tare da faɗin "ku tashi mutafi tayi magana tana kallon su hiyana, a tare suka miƙe gaba ɗayan su har da su Aunty Maryam suka nufi waje.

Palon ya rage daga Abba Ammi Ummi sai Aunty Amarya, shiru sukayi suna jin yadda Aunty amarya ke surfa ruwan bala'i dole sai Aryan ya saki diyana,Abba batare da yayi Magana ba yasa hannu a aljihun sa ya chiro wayar sa, ya shiga contact ya fara kiran wata number wadda akayi saving da My Brother.

Kira ɗaya a ka ɗaga sanya wayan a hand-free Abba yayi chikin girmamawa ya fara magana "Assalamu alaikum, daga ɗayan ɓangaren aka amsa da wa'alaikumus salam jin muryan wadda ya amsa Sallamar yasa Aunty amarya tayi sauri kwache wayar a hannun Abba ta katse kiran tana faɗin "dan girman Allah kayi hakuri karka sanar wa yaya wlh in dai Aryan ne na barshi yaje ya chigaba da zama da matar sa har abada Allah ya basu zaman lfy Allah yasa a gane ta" tana kai karshen maganar ta miƙe tare da ajiyewa Abba wayar sa a gefen sa ta nufi waje da sauri tana faɗin Allah na tuba kayafi min, duk bachin rai da raɗaɗin rasuwar Aiman dake damun Abba hakan bai hanashi yin ɗan murmushi ba dawo da kallon sa yayi kan Ammi da Ummi ya fara magana
Chapter 2 · 0% Book details