← Book details Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 80

Sashe 74

Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Chikin kanƙanin lokacin suka isa PRINCE SAFRAS HOSPITAL hannu bibbiyu aka karɓesu chikin sauri akayi A&E da su aka fara basu taimakon gaggawa shiru hiyana ta tsaya kusa da bgs tana addu'ar Allah ya sa diyana bata ji wani ciwo sosai ba zubawa Aryan dake kai kawo a bakin kofar accident and emergency ido bgs yayi ya ma rasa me zai ce masa. Tsawon 30mins suna tsaye ba wanda yace da wani ko uppan. suna tsaye mai sai da face mask yazo wucewa kiran sa bgs yayi ya ansa biyu ya sanya ɗaya ya miƙa wa hiyana ɗaya kallon mai sai da face mark ɗin yayi kallo ɗaya ya kawar da kansa kafin yace "ka bamu sa daka ne? dan bamu fito da kuɗi ba" murmushi ɗan yaron yayi kafin yace "ba komai oga,ae sadakar face mark kamar haka kam ba yau na fara ba Allah ya bawa mara lfy ku lfy" yana kai karshen maganar ya wuce chikin sanyin murya bgs yace "zo ɗan yaro" juyowa yayi ya dawo kusa da su "what is your name? da murmushi a kan face nashi yace "my name is Sadiq" hannu bgs ya miƙa masa da mamaki hiyana ke kallon su daman bgs yana kula talakawa kamar haka ne yanzu duk kyankyanin san nan zai haɗa hannu da wanna yaro ɗan dattin nan lallai ma tab. zazzakar voice nashi ne ya katse mata tunani yace "ina iyayen ka? Lokaci guda fiskar yaron ya sauya murya kamar zai fashe da kuka yace "ni bani da mama kuma bani da baba a hannun yayata wadda nake bi nake ita kaɗai ta rage min a duniya" kallon yaron da kyau bgs yayi kwata kwata yaron nan ba zai wuchi 13 years ba amma wai a hannun yayar sa wadda yake bi to ko itama ba zata 15 to 16 years ba kenan ina yan uwan maman sa da baban sa yayi nisa chikin tunani yaron ya katse shi da cewa "oga zan iya tafiya? Kallon Shahram bgs yayi chike da kaunar yaron ya fara magana "Shahram kuje ka tawomin da yar uwar tasa" waro ido waje yaron yayi chikin tsoro yace "dan Allah karka cutar da mu wlh bamu da kowa bamu da komai daga ni sai ita iya face mark ɗin nan nake sayar wa na kai mana kuɗi muci abin ci dan Allah idan ma face mark ɗin kake so tom gashi amma mu dai ka kyale mu" ganin yaron ya tsorata sosai ya sanya bgs ya shafa kan sa chikin kulawa yace "mai sunan Abba ka kwantar da hankalin ni soja ne ba zan cutar da kai ba sai dai ma na yaki masu cutar da mutane ina son akawomin yar uwar kane dan naji ina yan uwan ku suke da har suka barku kuke yawo haka" girgiza kai yaron yayi alamar shikenan ita dai hiyana ta zuba musu ido tana ganin ikon Allah bin yaron tayi da kallo har suka wuce da Shahram. dai dai lokacin Dr ya fito daga A&E chikin sauri Aryan ya tare sa yana faɗin "Dr ya jikin nasu" chike da rashin mutunci Dr yace "kubar yara suna yawo a gari sai abu ya same su kuzo ku dame mu a asibiti yanzu ka duba irin fyaɗen da aka yiwa yarinyar nan lokacin da aka mata ina k...bai kai karshen maganar ba Aryan ya ɗauke sa da wata mahaukaciyar mari wadda ya sa shi yin tangal tangal kamar zai faɗin lokacin guda yaji duniya ta tsaya chak chikin zafin nama ya danko wuyar rigar sa yana kokarin kara masa mari bgs ya kariso wajen tare da rike hannun sa ta baya dai dai lokacin Doctor Peter and doctor John suka fito da sauri suka kariso wajen ganin abun da ke faruwa,rai a matukar ɓace Aryan ya dubi dr John ya fara magana "kai John wanene wanna? yaushe kuka kawo shi aiki a hospital nan? "I'm sorry sir bai daɗe da fara aikk bane shi ya sanya bai san ka ba kuma ina ganin bai lura da face naka da kyau bane shi ya sa har yake kokarin ja da kai amma amasa afuwa" Aryan zai yi magana bga ya rufe masa baki chikin nitsuwa ya dubi dr Peter ya fara magana "dr ya jikin nasu?" ɗan murmushin dr Peter yayi kafin ya fara magana "jiki da sauki sai dai dukkan su basu farfaɗo ba mun dai yi nasarar shawo kan matsalar su yanzu zamu chanja musu ɗaki zuwa ɗaki na musamman" shiru Aryan yayi ya kasa magana, wucewa dr Peter da dr John sukayi juyawa bgs yayi ya nufi wajen motar su har ya ɗan yi nisa ya juyo yace "ke mutafi" tana tsaye kusa da Aryan kamar bata ji me yace ba kallon ta Aryan yayi "sister yaya Prince na kiran ki" dogon numfashi taja tare da sauke nauyayyar ajiyar zuchiya kafin tace "yaya Aryan menenen ya samu diyana? Satar kallon bgs yayi ta kasan ido yayin da shima bgs ɗin ya tsare sa da ido kasa magana yayi bashi da amsar da zai bata "yaya Aryan dan Allah ka faɗa min me ya same ta idan ba haka ba zuciya ta zata iya bugawa ka....bata kai karshen maganar ba aka fito da diyana a saman gado tana kwance,chikin sauri ta nufesu;tana kiran sunan ta "diyana!!diyana!!" bata kai ga karisawa wajen ba ya hamko hannun ta tare da jawo ta ta faɗa saman faffaɗar kirjin sa hannu ya sanya ya kwantar da kanta a kirjin sa "yaya Prince dan Allah ka sake ni inje in ga meke damun diyana,ɗazun fa muna tare da ita lfy ta kalau kuma accident da suka yi yaya Aryan yace basu ji ciwo ba iya yarinyar chan suka buge" hannu ya ɗaura mata a saman bakin ta yana faɗin "shiiiiiii" buɗe baki tayi zata sake magana yayi sauri sanya mata manuniyar yatsar sa a baki ya danne harshen ta chizon yatsan nashi tayi har sai da yace "wash" sai da ya ga an wuce da su diyana sanna ya zame hannun sa daga bakin ta tare da raba jikin su ya kama hannun ta suka koma wajen mota sai magiya take masa akan ya kai ta taga diyana amma yaki kula ta

chikin motar su Aryan ya dawo ya zauna tare da chiro wayar sa ya fara kiran layin Ammi.
"Yaya Prince inje? Zanyi magana kenan wayar sa ta fara kara satar kallon ta yayi ta kasan ido kafin yayi picking call ɗin ya koma daga ɗan nesa da su gyara tsayuwan ta tayi a jikin motar ta harɗe hannu a kirji tana tunanin ko me ya sanya diyana rashin lfy lokacin guda har da suma bata, murnushin tayi lokacin da wani tunani ya faɗo mata a rai ko dai yaya Aryan ne yayi maganin ta tab lallai in dai ko haka ne yau akoi dirama dan idan diyana ta farka sai yaya Aryan ya gwammaci da bai taɓa ta ba. tayi nisa chikin tunanin kamar daga sama taga mutun a gaban ta yana magana "sannun ki yanmata" kasa kasa tace "yauwa sannu" duk tunanin ta tambayar ta wani abu zai yi sai ta ga akasin haka,sai washe baki yake yana surutu "amma gaskiya yammata ke kyakkyawa ce duk da kin sanya face mark hakan bai hana kyanki bayyana ba ban taɓa ganin masu blue eyes a zahiri ba sai a film yau kam gashi na gani dan Allah idan ba damuwa ki tai makamin da phone number,dan mu rinƙa gaisawa,kuma ni sunana tarif,a nan kano nake babana mai kuɗi ne sosai kinga baki da matsala in dai akan kuɗi ne" tsaki taja kafin tace "malam ni matar Aure ce ka kama kan ka" murnushin yayi yana faɗin "haka kuke kyawawan matan nan idan mutun yace yana son ku sai ku fara cewa kuna da Aure to nima ai mijin Aure ne" shiru tayi bata yi magana ba lokacin guda ta birkice ta rasa ina zata sa ranta,ganin ta birkice hankali ta baya kan sa yana bayan sa ne ya sanya yace "yammata menene naga kin birkice haka yana maganar yana juyowa karaf idon sa ya sauka kan bgs dake tsaye a bayan sa fuska a ɗaure kamar an aiko masa da sakon mutuwa
Chapter 74 · 0% Book details