Sashe 52
Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Zaune take saman sofa a palon habibin ta tana buga game da wayar sa ta sha kwalliya sosai jikin ta na sanye da dogiwar riga abaya pink color kanta babu ɗan kwali ta saki gashi har gadon baya tana taunar chewing gum tayi nisa chikin game da take bugawa kamar daga sama aka fisge wayar daga hannun ta a zafafe ta ɗago kai ganin yaya Aryan ne ya sanya ta turo ɗan karamin bakin ta tana faɗin "kai yaya Aryan me haka ne dan Allah" hararar wasa ya wurga mata kafin yace "wai ke baki da Aiki sai buga game to ki tashi kije ki ɗauki Kur'ani ki fara karatu zanje na duba wata criminal ina dawowa ba jimawa" miƙewa tayi tsaye chikin jin haushi tace "daman kana da wata budurwace zakache kana sona? Kallon ta yake da mamaki ya mai mai ta kalmar nata "budurwa" "eh mana budurwa ba yanzu kache zakaje ka duba ta ba to idan ma bata da lfy ne Allah ya sa ta mutu" dariya abun ma yaso bashi wai yar karamar yarinya da kishi to ko me takewa kishi yanzu oho ita da bata san menene Auren bama tukun nan,ganin yayi shiru ne ya san ta fasa ihu tana faɗin "to ni wlh babu in da zakaje sai dai muje tare kuma wlh in dai mukaje sai na kashe ta" Aryan dai yau yaga ikon Allah yama rasa mai zaiche shi da zaije hukunta zulaihat me ya haɗa shi da budurwa wani tunanine ya faɗo masa shin ko dai diyana bata san ma'anar criminal bane tuna hakan ya sanya yayi kasa da murya yace "my jidda nifa mai laifi zanje hukun tawa ni da nake dake ina ruwa na da wata ko kin taɓa kallona ina magana da wata mace ne, ina chewa wayata awajen ki take zama kin taɓa kallon hoto ko number mace? Idan ba su Aunty farida ba" jin haka ya sanya tayi shiru ta sa hannu ta rufe fuska ita adole taji kunya murmushi ya saki tare da chire hannun da ta rufe fuska da shi yana faɗin "my jidda sarkin rigima wato har yanzu baki dai na ba ko? Faɗowa jikin sa tayi tana dariya "ni dai ban taɓa kallon mutun mai kuka da dariya lokacin guda ba sai ke my jidda kuka baya miki wuya kamar yadda dariya ma bata miki wuya" ɗan karamin bakin ta ta kafa a sai yin kirjin sa ta gabza masa chizo har sai da yace "wash my jidda to laifin me kuma nayi? da akamin hukunci haka"chikin shagwaɓa tace "Allah yaya Aryan ka chika neman magana to ni gaskiya ko ina ma zakaje sai dai mutafi tare dan naji kace wadda zakaje hukun tawa macece kar ina zaune a gida kai kuma kaje daga hukunci ku fara soyayya" rungumeta yayi sosai yana shafa lallausan gashin kan ta yace "my jidda nifa ke kaɗai kin ishe ni bana son ƙari ki kwantar da hankalin" ɗago kan ta tayi daga kirjin sa tana kallon face nashi tace "yaya Aryan to yanzu dai ka askemin gashin nan dan wlh yana damuna" juyawa yayi ya kamo hannun ta ta baya ya haurar da ita bayan sa ya goyata ya nufi hanyar fita yana faɗin "muje ki rakani wajen mota kuma idan kika kuskura kika taɓa min wanna kyakkyawar bakin gashin nawa sai na miki hukunci gaba ɗaya jikin ki wanna kyakkyawar gashin naki yafi komai burgeni" "kai yaya Aryan Allah ni kuma ban son gashi ni gaskiya askewa zanyi" tayi maganar dai dai lokacin da suka fito harabar gidan "to shikenan kina aske gashin naki ni kuma zan Aure mace mai gashi domin ni inason mace mai gashi sosai" hannu ta sanya da karfi ta za gashin kansa har sai da yace "wash haba my jidda" yayi maganar tare da sauke ta ɗaure fusaka tayi sosai tana faɗin "yanzu duk dogon gashin kan nan naka bai ishe kaba sai....ba ta karisa magana ba tayi shiru tare da juyawa ta bashi baya, murmushi yayi kafin yace "oh my goodness my jidda wai fushi kikayi kenan? to shikenan yanzu dai muje ki rakani wajen mota idan na dawo sai na rarrasheki sauri nake yanzu" make kafaɗa tayi tana faɗin "aa ni ba zan je ba na fasa rakiyar kayi tafiyar ka" juyawa yayi ya nufi parking space yana faɗin "Allah ya sa na haɗu da wata baby kyakkyawa a hanya nayi wuff da ita" jin abun da yace ya sanya ta juyo da gudu tayi tsalle ta haye saman bayan sa tana dariya,buɗe baki yayi zai yi magana wayar sa ta fara ringing,chikin sauri ya fito da wayar daga aljihun sa dan ya san call ɗin Bgs kawai yake expecting chikin sauri yayi picking call ɗin tare da manna wayar a kunne yana faɗin "hello my blood" daga ɗayan ɓangaren Bgs yace "ba sai kaje ba na sa an saki yarinyar" "What!!! Aryan ya furta azafafe tare da sauke diyana kasa daga bayan sa ya jingina da jikin motar sa "akan me zaka sanya a sake ta!? "Akoi dalili idan na gama da case ɗin zakaji" yana kai karshen maganar ya katse kiran juyowa Aryan yayi yana kallon diyana, gaba ɗaya yama manta bata da ɗankwali a kanta, "my jidda jeki ɗauko hijabi kizo mu tafi" "to" kawai tace ta wuce ta koma part nasu,binta yayi da kallo har ta shige ajiyar zuchiya ya sauƙe tare da ɗaga kai yana kallon sama jim kaɗan ta fito sanye da hijabi ɗan karami zuwa kirji,kallon ɗaya ya mata ya kawar da kansa tun bata kariso ba ya shiga motar gidan gaba mazaunin driver shiga ɗayan gefen tayi tana faɗin "yaya Aryan daman ka iya tuka motane? Yau kenan bazaka tafi da wayanchan masu mummunar fuskan ba" girgiza kai kawai yayi ya tada motar yaja suka nufi gate dan ya lura idan ya biyewa diyana sai su kwana a nan, a bakin gate na gidan ya tsai da mota tare da sauke glass ɗin motar ya dubi Shahram yace "ni kaɗai nake son fita kuma ba lallai mu dawo yau ba" yana kai karshen maganar ya ja motar da gudu suka fice daga gidan