← Book details Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 80

Sashe 28

Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sauri sauri tayi wanka ta fito gaban mirro taje ta tsaya chike da tsoro ta fara shafa man shafawar sa tanayi tana tunanin karfa yaji kamshin man shi ajikin na ya hukun tani, hannu ta kai zata ɗauki perfume nashi sai kuma ta fasa ta juya taje ta ɗauko wasu sheɗanun riga da wando kwata kwata rigar babu hannu, ita kuwa wando crazy che duk an tsastsaga ta a dai dai chinyoyin, sosai kayan suka matse ta, chinyoyin ta kamar zasu fashe, ɗaure gashin kanta tayi ta ɗauki hijabin Zahra ta sanya, ta fito ta nufi kitchen, already abin chin Bgs na shirye ɗauka kawai tayi ta koma part nasu, saman table da ta saba ajiye masa a nan ta ajiye ta kara gyara masa ɗakin ta nufi wajen turaren ɗaki dake gere chikin wani box glass mai ɗan girma wani haɗaɗɗen turare ta zaɓo mai bala'i kam shi ga daɗi, gaba ɗaya lungu da sakon dake chikin ɗakin sai da tabi ta feshe air freshener nan ta kara gudun Ac ta fito ta zauna a Palo, ta ɗauko wayar ta, ta kunna ta shiga massage dan ta duba massage ɗin da yaya Khalid yace ta duba, tana kokarin fara karan tawa sai taji takun sa alamar yana shigowa da sauri ta ajiye wayar, ta nitsu ta kame jikin ta waje guda

Kasa kasa yayi sallma kafin ya shigo, kafin ta buɗe baki ta gai da shima har ya shige betroom nashi, chikin sauri ta gyara hijabin jikin ta, ta miƙe tabi bayan sa, zaune saman sofa ta same sa ya jingina kai a jikin sofan yana kallon sama, gaban shi tazo ta tsugunna chike da tsoro ta fara chire masa ta kalmin kafar sa tana faɗin "sannu da dawuwa yaya prince ina wuni" chikin sanyin murya tayi maganar shiru yayi kamar ba da shi tayi maganar ba, bata damu ba dan bai amsa mata gaisuwa ba idan da sabo ta saba, zame masa safar kafan sa tayi, zubawa kafan sa blue eyes nata tayi ba Karami kyau yatsun kafar sa ke mata ba, ba abun da ya faɗo mata a rai sai marin da ta sha ranan akan taɓa kafar sa da dayi tuna hakan ne yasa tayi saurin kawar da idonta gefe tare da mikewa ta ɗauki ta kalman da safan ta mai dasu wajen da ya dace

Gaban shi ta dawo ta sugunna ta ɗauko goran ruwan faro mai sanyi daga chikin try abin chin da ta kawo masa, dauko glass cup tayi ta balle bakin roban ruwan ta zuba a chikin glass cup ɗin, ta ɗago ido tana satar kallon sa chikin sanyin murya tace "yaya prince ga ruwa" sai lokachin ya ɗago daga jinginan da yayi a jikin sofan, ba tare da kalli in da take ba yasa hannun ya ansa cup ɗin, a hankali ya kai cup ɗin sai tin dan karamin bakin sa ya fara shan ruwan, wani nauyayyar ajiyar zuchiya ta sauke wadda yasa shi ɗan kallon in da take chikin sauri ta fara kokarin zuba masa abin chi, hannun ya ɗaga mata kasa kasa ya furta "no need am ok" yana kai karshen maganar ya miƙe, da sauri ta miƙe itama ta dan duka ta anshi cup ɗin hannun sa, wuchewa yayi ya nufi toilet ita kuma ta kwashe kayan abin chin tayi waje dasu, sai murna take yau yaya prince ya bari ta chire masa ta kalma lallai yau ba zata manta da wannan rana ba, Allah dai yayiwa Ammi albarka daman ta faɗa mata daga yau yaya prince zai sauya mata to kuma gashi nan zan chen Ammi ya fara tabbata, kitchen ta mayar da kayan abin chin ta dawo palo ta haye doguwar kujera ta kwanta tare da jan hijabin jikin ta ta rufe har kafanta, ta lumshe ido kamar mai barchi.

Maiduguri Nigeria

Da matsanan chin gudu sosai motar su Aryan ta shararo akan mikakkiyar hanyar da zata sadasu da titin gidan Aunty farida, dai dai zasu shiga kwanan da zata sadasu da hanyar gidan Aunty farida, lokachin motan Ahzan ya danno kai, a sukwane ya taka birki, da da sauri motochin su Aryan ma suka taka birki wani wawan birki Shahram yaja wadda yasa Aryan dake zaune a gidan baya kan shi ta bugu da kujerar gaba na motar saura kaÉ—an motar sojojin dake gaban ya bugi motar Ahzan, chike da bachin rai Aryan yace "wani irin birki ne wannan Shahram? Murya na rawa Shahram yace "sorry sir bamusan mota na zuwa a gaban mu bane Shiyasa Allah ma ya tsare" shiru Aryan yayi bai sake magana ba ya dukar da kan sa dake matsanan chin sara masa, zuchiyar sa na bugawa da sauri sauri ji yake gaban sa na faduwa sai mai mai ta innalillahi wa inna ilaihir rajiun hasbunalluhu wani mal wakil a chikin zuchiyar sa

A ɓangaren Ahzan kuwa chike da jin haushi ya kama marfin motar zai fita Hanan dake zaune a gidan baya kusa da Ummi tace "yaya Ahzan karka fita dan Allah kana ganin wayan nan manya manyan Sojojin daga ganin fiskar su basu da imani" "haba hanan sufa suka so buge ni, ko ina mukaje sune masu laifi dan baa shiga kwana da irin wannan gudun da suka shigo yanzu da mun samu haɗari fa? Dole doka tayi Aiki a kansu duk da suke sojoji ai sun karya doka su kaya, juyawa yayi yana kokarin buɗe kofar motar sai ji yayi ana buga glass ɗin motar, fasa buɗe motar yayi ya sauke glass ɗin, da sauri ya runtse ido yasa hannu yana goge idon na shi dan ya tabbatar wa kan sa ba mafarki yake ba kuma ba karya idon sa ke gane masaba, wani jabgegen sojane tsaye awajen fiskar sa babu annuri chikin tsawa da karfin murya sojan yace "kai ka jaye mana motar kan nan ka bamu hanya!! Nan take jikin Ahzan ya fara rawa hannun sa sai kerma yake da kyar ya iya tada motar da gudu ya bar wajen, komawa chikin mota sojan yayi suka tayar suka bar wajen da gudun gaske.

UMMI

"Aunty hanan ji nake kirjina na bugawa da karfi zuchiya ta sai tsinkewa take kamar wani abu zai faru dani, Ahzan dake zaune a mazaunin driver yana tuki ya É—an kalleta ta chikin mirrow motar yace "haba Ummi kawai kin tsoratane saboda haÉ—arin da muka kusa yi, ba wani abu da zai faru dake ki chigaba da faÉ—in hasbunalluhu wani mal wakil kinji? GyaÉ—a masa kai Ummi tayi alama to, suka chigaba da tafi suna hiran irin sayayyan da zasu idan sun karasa shopping É—in, "amma fa ba zaku shiga shopping É—in nan ba jira zakuyi a mota ni zanje na sayi komai ba dan kun matsa ba ma da ba zaku bini ba" Hanan zatayi magana ya É—aga mata hannu dai dai lokacin da yake shiga gate É—in super market É—in.

To masu karatu sai mun haÉ—u gobe idan mai dukka ya kai mu

NEW TEAM💖
💖THE TALENT TROUPE WRITER'💖

*LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
👇👇👇👇

*1,DUK ƘARFIN IZZATA*
by(Star Lady)

*2,GIDAN AUNTY*
by(mss lee)

*3,SARKI SAMEER*
by(xeemat....love)

*4, JINI DAYA*
by(mrs bbk)

💖The Talent Troupe Writer's 💖

Wannan page É—in sadaukar wane gareki masoyiya Gidan Aunty ya Allah ya baki lfy Allah yasa kaffara ce

💖Story And Written💖
⬇️
*Star lady*

Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

Book 2

*Episode 15*

Aryan Aunty Farida, zaune suke a palon Aunty farida suna hira

"Aryan gaskiya ban yar da ba awannan karon kam sai dai muje tare, dan ni gani nake kamar baku duba diyana da kyau ji nake kamar idan naje da kai na zan iya gane ta" chewar Aunty farida tayi maganar tana kare masa kallon kan sa na kasa ba tare da ya É—ago ba yace "no Aunty farida nima ba iya zuwa zan yi ba domin gaba É—aya ji nake zuchiya ta na bugawa da karfi karfi na rasa me yasa tun dana kamo hanyar zuwa gidan nan naki gabana ke faÉ—uwa gaba É—aya naji jikina ya mutu, na kira commitioner akan su kawo mana mutane gidan nan, kawai" "eyya sorry Allah ya sauwaka ya Allah kasa diyana ce awan nan karon, Aryan zanyi magana wayar sa ta fara ringing, chirota yayi daga aljihun sa, ganin sunan Shahram ne ya bayyasa akan screen É—in yasa yayi saurin picking call É—in,

"hello sir ga mutanen sun kariso" mikewa yayi da kyar yana faÉ—in "ok am coming" yana gama faÉ—in hakan ya katse kiran tare da ficewa daga palon, chikin sauri Aunty Farida ta haura masa ta É—auko hijabi ta sanya ta bi bayan sa.

A harabar gidan Aryan ya tsaya tare da bawa sojojin sa umarni akan su shigo da mutanen, ba afi 2mins ba sai ga Shahram tare da wasu murane guda 2, dai dai lokacin Aunty farida ma ta fito ta kariso wajen nasu, chike da kwarin guiwa da sa ran zasuyi na sara Aunty farida ta fara magana "bayin Allah sannun ku" har suna haɗa baki wajen chewa yauwa hajjiya ina wuni? Batare da ta amsa gaisuwar ba tace "yanzu so muke ku kaimu in da mahaukachiyar yarinyar take, dan mu duba ita muke nema ko ba ita ba" shikam Aryan ido kawai yake bin su da shi ya kasa magana "hajjiya wlh tun lokacin da wani mai mota ya bugeta bamu sake ganin taba bamu sake jin ɗuriyar taba a takaice dai bamu san in da take ba, iya abun da muka sani shi ne lokachi da mai motar ya bugeta ya ɗauke ta ya sanya ta chikin motar sa, ina tsaye saman bene ina kallon sa har motar sa ta sauka daga kan titin layin ina kallon sa" Aunty farida zatayi magana Aryan ya riga ta da cewa "kun rike number motar ne? Motar wace iri ce? Shiru mutumin ya ɗan yi yana tunanin chan yace "gaskiya ban riƙe number motar ba ni dai na san motar baka che" tsaki Aryan yaja tare da bawa Shahram umarni akan ya sallami mutanen nan dan basu da anfani, chike da ɓachin rai ya juya ya nufi chikin gida da sauri Aunty Farida tabi bayan sa.
Chapter 28 · 0% Book details