← Book details Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 80

Sashe 26

Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

saman ka tafaren gadon sa ya kwantar da ita tare da mikewa ya ɗauko Box ya dawo saman gadon, magani zazzaɓi ya fitar ya ɓalli guda biyu, chikin sanyin murya yace "gashi an sa ki sha" jikin ta na kerma ta sa hannu zata ansa zubawa hannun ta ido yayi da mamaki yake kallon yadda hannun nata ke kerman tsoro, ɗaugo idon sa yayi ya fara kallon ta from head to toe gaba ɗaya jikin ta kerma yake hannun ta ya kasa tsayawa waje guda ba lallai idan ya sanya mata maganin a hannun ta ta iya kaiwa bakin ta ba, mikewa yayi ya koma falo ya ɗauko ruwa mai sanyi tare da glass cup ya dawo ɗakin a gefen gadon ya zauna ya balle bakin roban ruwan ya zuba a glass cup ɗin, zama yayi da kyau ya sa hannu ɗaya ya ɗagota, kasa kasa yace "buɗe bakin ki" da kyar ta iya sai ta kerman da bakin na ta keyi ta bude masa, sanya mata maganin yayi sannan ya kafa mata glass cup ɗin a bakin ta, sosai ta sha ruwan sai da ta shanye dukka, san nan ya chire mata cup ɗin a baki ya mai da ta ya kwantar, ya mike ya mai da cup ɗin da roban ruwan saman table ɗin tsakiyar ɗakin, toilet ya nufa.

Wanka yayi ya fito É—aure da towel a kugun sa, a gurguje ya shafa mai tare da fesa perfume nashi mai bala'i kamshi da daÉ—i, dressing room ya nufa, jim kaÉ—an ya fito sanye chikin kayan barchi masu kyau da tsada ga laushi fararen tas riga da doguwar wando, saman katafaren gadon sa ya haye, ya kwanta hannu yasa saman drawer ya É—auki remote ya kashe wutan É—akin ya mai da remote É—in ya ajiye, ya kunna wutan gefe da gefen gadon masu bada haske blue da green, addu'ar barchi yayi ya shafa, sannan ya juyo ya É—an kalli in da hiyana ke kwanche yadda ya kwantar da ita ko motsawa ba tayi ba, hannun sa ya kai saman goshin ta ba laifi jikin nata ya fara sanyi, dauke hannun sa yayi ya juya ya bata baya yana fiskantar gabas ya ja blanket zuwa saman chikin sa, tare da lumshe ido, asuba ta gari.

1:30am hiyana ta farka daga barci dishi dishi ta fara gani goge idon ta da kyau tayi domin ta tabbatar wa kanta shin muryan mutun take jine ko dai aljani ne mai wannan karatun dan ita dai a chikin bil adama kam bata taɓajin voice mai daɗin wannan ba, mikewa tayi zaune a saman gadon, tafara bin ɗakin da kallo.

mamaki ne ya kamata yaushe ta zo ɗakin nan kuma? Waya kawota? Dan ita jiya kwata kwata batama san in da kanta yake ba, yan waige waige ta fara yi tana neman ta in da take jiyo wannan kira'an Alqur'ani mai bala'i daɗin, karaf idon ta ya sauka kan shi yana zaune saman dar duma yana rike da Alqur'ani mai girma yana karatu, tasha ruwan mamaki wai daman yaya prince ɗin nan ya iya karatu? wai da gaske ne daman yana da imani? Ashe yasan Allah? Ashe yasan in da gabas take? ai na ɗauka shikam in ban da bindiga ba abun da ya sani, da wani zuchiyar sa kamar na Abu lahabi, duk girma da kima da mutunci da fiyayyen halitta manzon rahma yake da shi sai da abu lahabi, ya rinka kokarin kashe sa, to haka yaya prince ka ke duk mai mutunchi da imani da kima wadda Allah ya ɗaura maka responsibility sa a kanka komai kyaytatawar da zai maka sai ka nemi ka masa rashin mutunchi kai mutun baya taɓa kyau tata maka ko mai aka maka laifi ne, tayi nisa chikin tunani da take kamar daga sama har tsakiyar kanta taji voice nashi "ke sauka kije ki kawomin Black tea mara sugar! Chikin sauri ta diro daga gadon ta nufi waje mai da kanshi yay kan karatun da yake ya chigaba.

Jim kaÉ—an sai gata ta shigo rike da Cup mai shegen kyau gefen sa tazo ta tsugunna murya na rawa tace "gashi nan yaya prince" ko kallon in da take bai yi ba, shiru shiru sai zuba kiraar karatun qur'ani kawai yake tun hiyana na sa ran zai ansa har ta chire rai ta gaji da tsugunno gashi ba wani isshen lfy ke gareta ba, Almost 30mins tana tsugunne a wajen har barchi ya É—an fara É—aukan ta, slowly ya sa hannu ya ansa cup É—in, da kyar ta iya mikewa sai kuma ta kasa komawa saman gadon nashi ta kwanta, gani take kamar idan ta hau zai mata tsawa yace ta sauka, shiru tayi tana tunanin ta haune ko dai ta koma Palo, dan bata son tsawan nan da yake mata ko kaÉ—an, daga karshe dai ta yanke shawarar komawa saman sofa set dake chikin É—akin dan tana ganin hakan ne É—an dama dama.

Saman doguwar kujera ta kwanta ta lunshe ido, har barchi ya fara É—aukan ta sanyi mai karfi ne taji ya fara ratsa gaba É—aya jikin ta, takurewa tayi waje guda, sai rawan sanyi take, har karfe 2:45am ba abun da kakeji a chikin É—akin sai karan hakoran ta dake kakkarwa suna haÉ—uwa da juna
mikewa yayi ya mai da Qur'an mazaunin sa bayan ya gama karatun dawo yayi ya naɗe daddumar ya nufi gadon sa, hayewa yayi ya kwanta yaja blanket zuwa dai dai chikin sa, ƙaran sautin haɗuwar da hakoran ta keyi ne suka takura masa, chikin tsawa yace "ke zaki dai na damuna ne ko sai na ɓallaki!? Da sauri ta sanya hannu ta toshe bakin ta ta dungule waje gida, rmt ra ɗauko ya kara gudun Ac sosai ya mai da ya ajiye, ya ɗan kara hasken din light dake gefen gadon ya lumshe ido ba jimawa barchi yayi awon gaba da shi.

Hiyana kuwa barchi ya gagara, sai juyi take saman kujera sabon zazzaɓi ne ya rufe ta tun tana iya hakuri har ta fara kuka kasa kasa, gashi yace bai san jin karan sautin hakoran tama bare kuma kuka sosai ta toshe bakin ta, ta rasa in da zata sa ranta, shiko sai sharara barchin sa yake a haka har asuba, bata yi barchiba tayi kukan ta kasa kasa har ta gaji tayi shiru, tana jin sa ya tashi yayi wanka ya shirya chikin jallabiya fara ya fice ya nufi masallaci, yana fita ta chire hannun ta daga bakin ta, ta saki wani marayan kuka da kyar ta tashi ta nufi toilet na shi sauri sauri tayi wanka da ruwa mai zafi sosai, ta fito ɗaure da towel nashi ta nufi Palo, kamar zatayi kuka lokachin da take duba kayan da zata sanya dan tayi sallah gaba ɗaya babu kayan arziki, daga rigar da wando masu kama da 1 sai doguwar riga mara hannu, ji take kamar taje ta dauko Zahra ta mata mugun duka dan haushi, da kyar ta samu wani bakin wando da rigarsa fari mai hannu ɗaya, hannun ɗayan ma ɗan siriri da shi da babu duk ɗaya ne, komawa tayi chikin ɗakin sa da sauri ta sanya kayan ta ɗauki blanket na shi ta rufa a jikin ta daga kanta har kasa ta shin fiɗa daddumar tayi Sallah, tana idarwa ta mai da blanket ɗin ta naɗe daddumar, ta ɗauki Cup da yasha black tea da daddare ta fice daga ɗakin ta mai da kitchen, tunani ta shigayi shin yauma naje na gyara masa ɗaki ne ko dai na kyalesa kar yazo yamin hukunchin irin na jiya.

Da wannan tunanin ta koma betroom nashi, gadon ta nufa ta chire bet shirt ɗin ta nufi waje ajiye kayan datti ta ajiye ta dawo ta shiga dressing room ta ɗauko wani dankareren bet shirt fari tas mai bala'i kyau da tsada ga laushi kai ka che audigane, sauri sauri ta shinfiɗa gadon ta sauko ta nufi toilet ta wanke masa fes ta gyara ko ina a chikin ɗakin, ta sanya turare mai bala'i kamshi, shiru ta tsaya tana mai da numfashi tunani take in koma palo in zauna ne ko dai in zauna a nan kar kuma na zauna a nan ya dawo ya fara faɗa, dan shi bazaka taɓa gane menene idan ka masa dai dai da kuma ba dai dai ba, yanzu na samu ya fara ansan abu daga hannu na bai kamata nayi masa wani laifin da zai sa ya dai na hakan ba, jiki ba kyari ta fito palo ta zauna saman sofa, tayi shiru tana tunanin chan ta tuno ashe tana da waya, mikewa tayi chikin sauri ta ɗauko wayar a chikin akwatin ta, ta kunna babu charji, mikewa tayi ta sanya wayar a chaji ta dawo ta zauna.

Karfe 6 Bgs ya shigo palon yana waya betroom nashi ya nufa har ya kai bakin kofa sai kuma ya juyo kallo ɗaya ya mata ya kauda kai tare da chere wayar daga kannun sa, daga in da yake tsaye ya sai ta ta da wayar alamar tazo ta ansa, chikin sauri ta miƙe ta garisa gaban sa ta sugunna ta ansa watar juyawa yayi ya shige chikin betroom ɗin.
Chapter 26 · 0% Book details