← Book details Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 80

Sashe 19

Duk Karfin Izzata Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kwanche saman gadon hanan ya same ta tana kuka, saman drawer gefen gadon ya zauna a nitse ya fara magana "ya isa haka kukan kinji? Ɗago kai tayi tana ganin sa ta mike zaune tana goge hawayen "yaya Ahzan wai daman a gidan nan yaya deen yake kuma wai daman kanin kane, ni kullun idan Aunty hanan tana bani lbr sa, ina tunanin ko ba'a nan yake ba ban ma taɓa tunanin ɗan mum bane, yanzu gashi saboda ni ka da kesa a banza" tana magana tana shesshekar kuka "look ya isa haka deen kani na ne baban mu ɗaya amma ba mum che ta aife sa ba maman shi daban ina ga tun da kikazo gidan nan baki fita waje bane, amma da kin fita tsakar gida zakiga gate na shiga part nasu, daga gefen hagu, ki daina damuwa ba dan saboda ke na bugi deen ba kisani baa taɓa yin sati ban bugi deen ba na rufesa a station na bashi horo amma duk da haka a banza baya jin magana ga shaye shaye da bin abokan banza, idan na hukun tashi kullun sai mum nashi tayi ta faɗa bata son laifin sa ko kaɗan, dan haka babu ruwanki da shi idan ya shigo ya sameki a palo ki tashi ki koma ɗaki ki bar masa palon kinji ko? Gyaɗa masa kai tayi tare da faɗin "eh naji" "munyi magana da mum tun da har yanzu baki tuna sunan kiba zamu rinƙa kiranki da Ummi kinji" "to yaya Ahzan Nagode" "ki dai na min godiya kinji? ni yayan ki ne kuma kin chan chan chi na miki hakan, yanzu dai ya kamata ki shiga school kafin Allah yasa muga iyayenki ko? Da sauri ta mike zaune ta goge hawayen fuskarta ta fara murmushi "yaya Ahzan yanzu nima zan rinka sa uniform irin na Aunty Hanan? zan rinka zuwa in da take zuwa? Zan rinka rubutu a takarar da kamar yadda take? Kasa bata amsa ma yayi ya zuba mata ido kawai yana kallon yadda take murmushi chike da farinchiki, shi kanshi bai san lokacin da ya fara murmushi ba "yaya Ahzan yaushe zaka kai ni to? "Ranar Monday In Sha Allah" saukowa tayi daga gadon ta dawo gaban sa ta sungunna tace "Nagode yaya Ahzan" mikewa yayi ya nufi waje yana faɗin "ki dai na yimin godiya ni yayan ki ne mai kaunar ki dan Allah" yana gama faɗin hakan ya fice daga ɗakin, da murna Ummi ta mike ta koma kan gado tana ta farin ciki ta kwata ta lumshe ido kamar mai barchi

KANO

Kwanche Ammi take a saman gadon Abba ta tada kai da chinyar sa, tana wasa da yatsun hannun sa ɗaya, chikin nitsuwa Abba ke shafa gashin kanta da ɗayan hannun sa "Aisha an gama ginin gonan kun nan fa saura mu ɗauki ma aikata sai a kwaso dabbobi a zuba aduba abubuwa da ya kamata a kara awajen, amma wani suna ya kamata a sanyawa gidan gonan? Gyara kwanchiya Ammi tayi tana kallon face nashi da kyau ta fara magana "ni har ga Allah na barwa su hiyana rabon nawa gadon nariga da nayi kyauta da wadda zanyi sauran kuma a chigaba da kula musu da shi ka zaɓi duk sunan da ya dache ka sanyawa gidan gonar, amma ina neman wata alfarma, idan ba damuwa "wace alfarma che wan nan Aisha? " Ina son idan anje ɗauko dabbobin nan a ɗauko har da bello dan bello ba mutunne na yarwa ba, ya mana halak chi ya chanchan chi muma mu kyautata masa, ina gidan da ka sayawa Ahmadu lokachin da mukayi mukayi ya dawo nan yaki to kabawa Bello gidan ya zauna da matar sa" "Aisha wan nan shawara ce mai kyau kinga daman yasan kan dabbobi sosai sai mu bashi aiki a gidan gonar yanayi duk wata muna biyan shi Albashi ko? "Eh hakane kaga yaransa zasu samu karatu zasuyi ilimi kuma zai sanya matar sa ma a makarantar tun da itama ba wani girmane da itaba kwata kwata bazata wuchi 18 to 19 years ba, shi kan shi Bellon ma bai wuchi 25 years ba zai iya shiga school ai" hakane kina da gaskiya Aisha Allah dai ya dafa mana zanyi magana da Aryan dan muga sunan da ya dache musawa gidan gonar.

"Yauwa niko ɗazun banga Aryan awajen breakfast ba naje part nashi baya nan na kira layin sa bata shiga" "Aryan fa baya nan ya tafi Maiduguri dan an kirashi jiya da daddare akoi wadda ya kalli diyana, shine yaje ya duba ko itace" zubur Ammi ta miƙe chike da farinchiki sai murmushin take tace "Allah yasa itace ko Aryan ya samu kwanchiyar hankali bawan Allah wlh kullun sai na tayashi da addu'a, duk lokacin da na tunashi sai nayi hawaye yana matikar Son diyana sosai gashi abun ya haɗe masa rasuwar Aiman batar diyana" Abba da ya lura yanayin Ammi ya fara sauyawa ta fara shiga bakin chiki da ta tuna diyana, sai ya matso kusa da ita chike da so da kauna ya rungumota tare da ɗago habarta yace "ai yadda nake son ki yafi yadda Aryan ke son diyana" hararan wasa ta wurga masa tana faɗin "gaskiya Aryan yana bala'i son diyana sosai" kara rungumota sosai Abba yayi yana kokarin mantar da ita maganar diyana dan yasan yanzu zata fara kuka, kwan chiya yayi da ita a jikin sa, yana shafa bayan ta a hankali, shiru sukayi har barchi ya ɗauketa.

UK

karfe 6pm hiyana ta farka a hankali ta waro idon ta, da kyar ta miƙe zaune a hankali chike da tsoro ta kai idonta kan katafaren gadon sa, ganin tayi Bgs baya nan chikin sauri ta fara jujjuya blue eyes nata tana duba ta ina zata gan shi, amma ina ko alamar sa babu a ɗakin mikewa tsaye tayi jiki ba kwari, tana son fita waje amma babu kayan sawa, a hankali ta taka ta fito palon su, ta rasa ya zatayi gashi daman da hijabi ɗaya tazo kuma ta yaga hijabin tana son ta shiga ɗakinta domin ta ɗauki kayan da ta chire ta mai da tun da bata da wani amma tana tsoro gani take kamar akoi wani machijin, tayi nisa chikin tunani sai ji tayi an taɓa ta firgigit ta ɗago ido ganin Amrat che yasa ta sauke ajiyar "Amrat jeki kawomin hijabin ki, in sanya ina su Aunty Zahra kuma? "Aunty Zahra suna palo yanzu muka dawo daga wajen shopping nima zanje na ajiyewa yaya Fahad kayan shine a ɗaki kizo muje palo kema kiga kayan da Aunty Zahra ta zaɓi miki" "to jeki kawomin hijabin ki tukun nan" to Amrat tache tare da wuchewa ta shiga ɗakin su Amrat na wuchewa sai ga Bgs, chikin sauri Hiyana ta sugunna kasa tace "ina wuni yaya prince" ko kallon in da take bai yiba ya wuche betroom nashi jim kaɗan ya fito ya fice waje, da alama wani abun ya ɗauko, tunani hiyana ta shigayi anya yaya prince zai iya sauyawa kuwa shi kwata kwata ma ba zaka taɓa gane in da ya dosaba baka gane daman shi bare hagun sa, mutunne kamar ba mutun ba, amma zanyi magana da Aunty Farida da kuma Ammi kila su karamin wani shawara amma gaskiya ina da babban aiki kuma da alama na dauki alkawarin da ba zan iya chikawa ba, tana duke a wajen har Amrat ta fito mata da hijabin ta.

"Aunty Hiyana ga hijabin" mikewa hiyana tayi ta ansa hijabin ta sanya iya guiwa hijabin Amrat ya tsaya mata tare suka jera zuwa palon kasa, nan suka samu Zahra da Lamrat sun baza kaya a gaba sai surutu suke, saman sofa mai zaman mutun 1 Hiyana ta zauna tare da É—agawa Zahra gaisuwa, fiska É—auke da fara Zahra ta amsa tare da faÉ—in "Aunty hiyana wayan chan trolley guda ukun nakine ki duba kayan idan akoi wani abun da kike bukata wadda baa sa a chiki ba yaya khalid yace ki faÉ—amin sai gobe mu koma wajen ki zaba da kan ki idan ma kayan gaba É—aya basu miki ba sai muje gobe ki zabo da kanki.

Saukowa kasa karfet din Hiyana tayi batare da tayi magana ba ta fara bubbuÉ—e trolley tana duba kayan, gaba É—aya trolley sai da ta buÉ—e su ta duba chike da jin haushi ta É—augo blue eyes nata tana kallon Zahra ta fara magana
Chapter 19 · 0% Book details